Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Za a yi jana'izar Ebrahim Raisi ranar Talata - Rahoto

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 20 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. An sanya lokacin gudanar da sabon zaɓe a Iran bayan mutuwar Shugaba Raisi

    Kafafen yada labarai a Iran sun ce za a gudanar da zaben shugaban kasa nan da ranar 28 ga watan Yunin gobe, bayan mutuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi.

    Raisi ya rasu ne a ranar Lahadi sakamakon hadarin jirgin da ya rutsa da shi tare da Ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian.

    Shugaban sojin kasar ya bayar da umarnin a gudanar da binciken dalilin hatsarin jirgin.

    Gabanin zaben an ayyana mataimakin Raisi, Muhammad Mukhbir a matsayin wanda zai ci gaba da jagorantar kasar.

    An kuma nada tsohon kwararen mai shiga tsakanin kan makamin nukiliya Ali Bageri a matsayin sabon ministan harkokin wajen Iran.

  2. Firaministan Isra'ila ya yi watsi da buƙatar kotun duniya ta kamashi kan yaƙin Gaza

    Firaiministan Isra'ila Banjamin Netanyahu ya yi Allah-wadai da bukatar mai gabatar da kara na Kotun Duniya ta neman a kama shi da wasu shugabannin Hamas bisa zargin aikata laifukan yaki a Gaza.

    Netanyahu ya ce "na yi watsi da bukatar mai gabatar da karar ICC, da kuma tir da kwatancen da ya yi tsakanin gwamnatin dimokradiyyar Isra'ila da ta masu kisan kai".

    Shugaba Biden ya yi na'am da kalaman Netanyahu yana cewa ba za a taba kwatanta Isra'ila da Hamas ba.

    Mai gabatar da karar ICC Karim Khan ya ce akwai kwararan hujjoji kan cewa Netanyahu da Ministan tsaron kasar sun aikata laifukan yaki a Gaza.

    Babban mai shigar da karar ya gabatar da hujjojin da aka tattaro a Gaza ga alkalan kotun.

    Yanzu hankali ya koma kan alkalan, domin ganin ko za su ba da izinin kama shugabannin nan da makonni masu zuwa.

    Mista Khan ya ce akwai shaidar Isra'ila ta yi amfani da yunwa da yunkurin murkushe al'uma da kuma kai hari kan farararen hula a Gaza da gangan.

    A gefe guda kuma, ya zargin shugabannin Hamas da fyade da azabtarwa da kuma rike Isra'ilawa fararen hula a yayin harin da suka kai a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

    Ita ma Hamas ta yi watsi da neman kama shugabanninta, tana cewa ICC na cakuda gaskiya tsakanin wanda aka cuta da wanda ya cutar.

  3. Rikicin siyasar Rivers: An buƙaci APC da PDP su gargaɗi Wike

    Jagoran kabilar Ijaw Chief Edwin Clark ya bukaci shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da takwaransa na PDP, Ambasada Umar Damagum, da su gargadi ministan Abuja, Nyesom Wike.

    Clark ya ce kalaman da ministan kuma tsohon gwamnan jihar Rivers ya yi kwanan nan a jihar ka iya haddasa rikici a can.

    A wasikar da ya rubuta wa shugabannin manyan jam'iyyun na Najeriya, biyu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Clark, ya tunashe su illar barin rikicin jihar ta girma.

    Ya ce, babu ta yadda shugabannin jam'iyyun biyu za su ce ba su san abubuwan da ministan na Abuja yake yi a jihar Rivers ba na neman tayar da zaune tsaye.

    Jagoran ya ankarar da su muhimmancin jihar ta Rivers ga tattalin arzikin Najeriya.

    “Ina fatan ba ku manta da cewa manyan kamfanonin mai na duniya da kuma tashar jirgin ruwa ta teku ta Onne, na kafe daram a nan jihar Rivers ba,'' in ji jagoran.

    Ya kara da cewa'' Ta yaya gwamnatin tarayya da kuma manyan jam'iyyu biyun za su bar wani mutum daya, ya tayar da zaune tsaye da kuma cin mutumcin gwamnan da aka zaba ta dhanyar dumukuradiyya, Siminalayi Fubara, a kan cewa wai shi kadai ne tilo ba al'ummar Rivers ba ya sa Fubara ya zama gwamna, a kalamansa na tsokana da neman haddasa rikici?''

  4. Ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya sun ɗaura ɗamarar shiga yajin aiki kan kuɗin lantarki da albashi

    Shugabannin kungiyoyin kwadago na Najeriya na NLC da TUC, sun sanar da abokan tafiyarsu na kungiyoyin farar hula da cewa su zauna da shirin shiga yajin aikin gama-gari, muddin gwamnatin kasar ta ki janye karin kudin lantarki da ta yi ta kuma kasa cimma matsaya a kan mafi karancin albashi nan da ranar 31 ga watan nan na Mayu.

    A wata sanarwar bayan taro ta hadin gwiwa da suka fitar yau Litinin shugabannin kungiyoyin biyu, sun bai wa gwamnatin tarayya da hukumar da ke kula da harkar samar da wutar lantarki ta kasar (NERC), wa'adin zuwa karshen watan nan na Mayu, kan su janye karin farashin.

    Haka kuma shugabannin sun jaddada wa'adin zuwa ranar 31 ga watan nan na Mayu ga gwamnati ta kammala maganar sabon mafi karancin albashi a kasar ko kuma ma'aikata su tsunduma yajin aiki na gama-gari.

  5. 'Ɗaliban manyan makarantun tarayya ne kawai za su fara samun bashin karatu na Najeriya'

    Shugaban asusun bayar da bashin karatu na Najeriya, Mr Akintunde Sawyerr, ya ce dalibai miliyan 1 da dubu 200 ne a fadin manyan makarantun gaba da sakandare na gwamnatin tarayya za su samu bashin a kashin farko.

    Da yake magana a yau Litinin kafin bude kafar intanet ta neman bashin a ranar Juma'a, ya ce za a fara bude kafar ne ga daliban makarantun tarayya, wadanda makarantunsu suka riga suka kammala sanya bayanan daliban.

    A bayanan da ya gabatar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, shugaban ya ce bashin wanda za a ba wa dukkanin daliban manyan makarantun gaba da sakandare na gwamnati, za a bayar da shi ne kashi-kashi inda za a fara da makarantun tarayya kafin a kai ga makarantun gwamnatocin jihohi.

    Shugaban ya ce, hanyoyin biyan bashin maras kudin ruwa, suna da sassauci, kuma dalibi zai fara biya ne shekara biyu bayan kammala aikin yi wa kasa hidima (NYSC) idan har ya samu aiki.

  6. Kotu ta sake hana belin Nnamdi Kanu

    Wata kotun tarayya a babban birnin Najeriya, Abuja, ta sake yin watsi da bukatar bayar da belin shugaban haramtacciyar kungiyar 'yan-a-ware ta Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, inda lauyoyinsa ke neman kotun ta kawar da umarnin soke belinsa na 2017, bisa zargin tsere wa shari'a.

    Haka kuma a yayin zaman sauraron, Maisharia Binta Nyako, ta yi watsi da bukatar Kanu ta neman a kaishi gidan yari na Kuje, idan har aka ki yarda da bukatarsa ta neman beli.

    Maisharia Nyako, wadda ta ce kotun ta dade kuma a lokuta da dama tana nazari a kan batun nemin belin na jagoran 'yan a-waren na Biafra, ta ce zabin da ya rage masa kawai a yanzu shi ne ya daukaka kara kan hukuncin.

    Ta kara da cewa daga yanzu duk wata bukata da aka sake gabatar wa kotun a kan batun belin, to za ta dauki hakan a matsayin wasa da shari'a.

    “Na duba na kuma gamsu cewa wurin da ake tsare da mai neman belin wuri ne da ya dace,'' in ji ta.

    Daga nan ta umarci Kanun ya mayar da hankali kan fara gudanar da shari'arsa.

    Kotun ta dage zaman zuwa ranar 19 da kuma 20 ga watan Yuni domin fara shari'ar.

  7. Yadda dubban Iraniyawa ke alhinin rasuwar Shugaba Raisi

    Tun bayan da hukumomi suka tabbatar da mutuwar shugaban Iran Ebrahim Raisi, 'yan kasar magoya bayan gwamnati suke ta tururuwa zuwa dandalin Tehran dauke da hotunan marigayin domin nuna alhininsu da makoki.

    A irin wannan taron a baya akan yi jigilar mutane daga makarantu da ofisoshin gwamnati a cikin motocin bas, a kai su dandalin.

    Sannan a wannan karon 'yan kasar ta Iran da dama na nuna farin cikinsu da mutuwar shugaban a shafukan sada zumunta da muhawara.

  8. Za a fara binciken abin da ya janyo haɗarin jirgin Shugaba Raisi

    Hafsan hafsoshin sojojin Iran Manjo Janar Mohammad Hossein Bagheri ya bayar da umarni ga wata babbar tawaga ta gudanar da bincike kan abin da ya janyo hadarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya janyo mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi da ministansa na waje Hossein Amir-Abdollahian.

    Kamfanin dillancin labarai na kasar, IRNA, ya bayar da rahoto a yau Litinin cewa, tawaga karkashin Birigediya Janar Pilot Ali Abdollahi, da ta kunshi kwararru na kasar da kuma na soji sun isa wurin da hadarin ya faru a gabashin Azerbaijan, kuma tuni har sun fara gudanar da bincike.

    An bayar da labarin mutuwar manyan jami'an ne cikin tsakar daren da ya gabata bayan sa'o'in da aka kwashe ana ta neman wajen da jirgin ya yi hadari.

    Wadanda suke cikin jirgin da ya yi hadarin wanda ke komawa bayan ziyara zuwa arewa maso yammacin iyakar kasar da Azerbaijan sun hada da gwamnan gabashin Azerbaijan, Janar Malek Rahmati da kuma wakilin jagoran addini na Iran a lardin, Ayatollah Mohammad Ali Al-e Hashem.

    Kamfanin dillancin labaran na Iran, ya ce nan gaba za a bayyana sakamakon binciken.

  9. Liverpool ta sanar da daukar Slot a matakin sabon kociyanta

  10. Kalli bidiyon shugaban Iran Ebrahim Raisi gabanin hatsarin jirgin da ya yi ajalinsa

  11. Mutumin da ya banka wa masallaci wuta a Kano ya amsa laifinsa a kotu

    Matashin da ya banka wa masallaci wuta a jihar Kano, ya amsa laifin da ake tuhume shi da aikatawa a gaban kotu.

    Mutumin mai shekara 39 wanda ya gurfana a gaban wata kotun shari'ar musulunci da ke birnin na Kano, inda aka tuhume shi da laifuka uku, ya ce ya amince da tuhume-tuhumen da aka karanta masa.

    A ranar Laraba 15 ga watan Mayu ne matashin ya cinna wuta a wani masallaci da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano, daidai lokacin da ake ibada.

    Yanzu haka mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar wutar sun kai 17, yayin da wasu mutum 12 ke kwance a asibiti.

    Kotun ta ɗage sauraron shari'ar zuwa 31 ga wanna wata na Mayu domin bai wa wanda ake zargi damar samun lauya, sannan masu gabatar da kara su samu damar tattara shaidu.

  12. Amurka ta amince da janye sojojinta daga Nijar nan da tsakiyar watan Satumba

    Amurka ta amince ta kammala janye sojojinta fiye da 1,000 daga Jamhuriyar Nijar nan da ranar 15 ga watan Satumba, bayan kammala shawarwarin da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu.

    "Ma'aikatar tsaron ƙasar Nijar da ma'aikatar tsaron Amurka sun amince da aiwatar da janyewar sojojin Amurkan, wadda tuni aka fara aiki da ita. An amince da cewa Amurka za ta janye sojojinta ne nan da ranar 15 ga watan Satumban 2024," in ji wata sanarwar hadin gwiwa da aka buga shafin sada zumunta na X na asusun gwamnatin sojan Nijar a jiya.

    Tawagogin biyu sun bayar da tabbacin kariya da tsaron sojojin Amurka a lokacin ficewar su.

    Sanarwar ta kara da cewa, Nijar da Amurka sun kuduri aniyar tattaunawa don fayyace makomar dangantakarsu.

    Shugaban mulkin sojan Nijar, Birgediya Janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023, ya bayar da umarnin korar sojojin Amurka a cikin watan Maris bayan da aka samu saɓani tsakanin Yamai da Washington kan yadda kasar ta yankin Sahel ke kara kusanci da Rasha da Iran.

  13. Shugaba Putin ya tattauna da sabon Shugaban Iran Mokhber ta waya

    Mun samu labarin cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tattauna da sabon shugaban Iran na riƙon ƙarya Mohammad Mokhber, inda ya bayyana marigayi Raisi a matsayin "abokin hulɗa nagari".

    Fadar Kremlin ta tabbatar da tattaunawar tasu ta waya, inda ɓangarorin suka jaddada "aniyarsu ta yauƙaƙa alaƙa tsakanin Iran da Rasha," kamar yadda kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Iran babbar ƙawar Rasha ce ta fannin ayyukan soji tun bayan da Rashar ta ƙaddamar da hare-hare kan Ukraine a 2022.

    Tun da farko, Putin ya bayyana alhininsa bayan ɓullar labarin rasuwar Shugaba Raisi a hatsarin jirgin sama samfurin mai saukar ungulu - ko kuma helikwafta.

    Putin ya bayyana marigayin a matsayin "cikakken abokin Rasha kuma "ƙwararren ɗan siyasa".

  14. Tinubu ya miƙa ta'aziyyar rasuwar Raisi ga al'ummar Iran

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya miƙa ta'aziyyar mutuwar Shugaban Iran Ebrahim Raisi, da Ministan Harkokin Waje Hossein Amir-Abdollahian, da sauran abokan tafiyarsu sakamakon hatsarin jirgin sama.

    Wata sanarwa daga fadar shugaban a Abuja ta ce Tinubu "ya bayyana damuwa game da wannan tsautsayi, kuma ya siffanta Raisi a matsayin shugaban da ya mayar da hankali wajen cigaban Iran".

    Da yake taya iyalansa alhini, Shugaba Tinubu "ya yi addu'ar ɗorewar zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da kuma cigaban ƙasar Iran," in ji sanarwar.

    Babu wata alaƙa mai girma a hukumance tsakanin Najeriya da Iran amma akwai mabiya mazahabar Shi'a masu yawa a Najeriyar ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky, waɗanda suke samun goyon bayan Iran.

  15. Sabon shugaban Iran ya yi wa ministoci jawabi

    Mun samu hoton sabon shugaban Iran na riƙo, Mohammad Mokher, lokacin da yake yi wa majalisar ministoci jawabi a Tehran.

    Mokhber wanda shi ne mataimakin shugaban ƙasa na ɗaya kafin yanzu, an san shi a matsayin na kusa-kusa da Shugaban Addini Ali Khamenei.

    Za a shirya zaɓen shugaban ƙasa nan da kwana 50.

  16. Kalli yadda masu aikin ceto suka zaƙulo gawawwaki a wurin hatsarin jirgin shugaban Iran

  17. Labarai da dumi-dumi, Limamin da ke tare da Raisi ya tsira daga hatsarin tsawon awa ɗaya

      • Marubuci, Siavash Ardalan
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian

    Yayin da ƙarin bayanai ke fitowa game da hatsarin jirgin sama da ya yi sanadiyar mutuwar Shugaban Iran Ebrahim Raisi, an gano cewa limamin da ke cikin jirgin tare da shi ya tsira daga hatsarin.

    Imam Mohammad Ali Al-Hashem, shi ne limamin masallacin Juma'a na garin Tabriz, inda jirgin nasu ya nufa kafin hatsarin.

    A cewar Mohammad Nami, shugaban hukumar kiyaye afkuwar bala'i ta Iran, ya tsira tsawon sa'a guda bayan faduwar jirgin. Har ma ya yi kokarin tuntubar taimakon ofishin shugaban kasar.

    "Babu buƙatar gwajin DNA don gano fasinjojin da ke cikin jirgin," in ji Nami.

    Jimillar mutum tara ne suka mutu a hatsarin, waɗanda suka haɗa da ma'aikatan jirgin.

  18. Labarai da dumi-dumi, Mai shigar da ƙara a Kotun Duniya ya nemi a kama Netanyahu da shugabannin Hamas

    Babban mai shigar da ƙara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ya nemi kotun ta ba da umarnin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma jagoran Hamas a Gaza saboda aikata laifukan yaƙi.

    Karim Khan ya ce akwai hujjoji ƙarara da ke tabbatar da cewa ɓangarorin biyu sun aikata laifukan yaƙi da na tarwatsa rayuwar ɗan'adam daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

    Kotun ta ICC da ke birnin Hague na bincikar ayyukan Isra'ila a yankunan Falasiɗnawa da ta mamaye tun daga shekara uku da suka wuce - da kuma ayyukan Hamas a baya-bayan nan.

    Mista Netanyahu ya siffanta ba da umarnin kama shugabannin Isra'ila da ICC za ta yi a matsayin "abin takaici da zai jawo matsala a tsawon tarihi".

  19. Labarai da dumi-dumi, Ayatollah ya sanar da sabon shugaban riƙo na Iran

    Kamar yadda muka bayyana muku tun farko cewa Mohammad Mokhber ne zai zama shugaban riƙon ƙwarya na gwamnatin Iran, to a yanzu jagoran addinin ƙasar Ayatollah Khamenei ya sanar da hakan a shafinsa na X.

    Ya ce Mokhber zai hada kai da sauran bangarorin gwamnati - 'yan majalisa da kuma masu shari'a domin tabbatar da an gudanar da zaben sabon shugaban ƙasa a cikin kwanaki 50 masu zuwa.

  20. Kotun ƙolin Afirka ta Kudu ta haramta wa Zuma takarar ɗan majalisa

    Kotun ƙolin Afirka ta Kudu ta haramta wa tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma tsayawa takarar majalisar dokoki a babban zaben ƙasar da za a yi a mako mai zuwa.

    Kotun tsarin mulkin ƙasar ta ce hukuncin ɗaurin watanni 15 a gidan yari da aka yanke wa Zuma bisa samunsa da laifin cin mutuncin kotu ne yasa aka hana shi tsayawa takara.

    A shekara ta 2021 ne dai aka yanke wa Mista Zuma hukunci kan samunsa da laifin cin hanci da rashawa a lokacin shugabancinsa da ya suaka a shekarar 2018.

    Ya yi yaƙin neman zaɓe ne a karkashin tutar sabuwar jam’iyyar uMkhonto weSizwe (MK) da aka kafa bayan takun saka da jam’iyyar ANC mai mulkin ƙasar.

    Sakatare Janar na MK Sihle Ngubane ya ce jam'iyyar ta ji taƙaicin hukuncin, amma hakan ba zai shafi yakin neman zabenta ba.

    "Har yanzu shi ne shugaban jam'iyyar, hukuncin bai shafi yaƙin neman zabenmu da komai ba," in ji shi.

    Mista Ngubane ya kara da cewa, fuskar Mista Zuma za ta ci gaba da kasancewa a cikin takardar kada kuri'a a zaɓen na ranar 29 ga watan Mayu.