Akwai ruɗani game da 'wasikar' da Sheikh Dahiru Bauchi ya rubuta kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Sai da safenku

    Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Ana ci gaba da zanga-zanga a Serbia don neman a je zagaye na biyu na zaɓe

    Serbia

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ci gaba da zanga-zanga a babban birnin Serbia, inda masu fafutuka ke neman a yi zagaye na biyu na zaɓen makon jiya.

    Masu sa ido na ciki da wajen ƙasar sun ce an tafka maguɗi a zaɓen, kuma yanzu haka manyan ƴan adawa bakwai suna yajin cin abinci don nuna rashin amincewa da zaɓen.

    Shugaban Serbia, Aleksander Vucic, ya yi watsi da sukar da ƴan adawar suka yi, ya kuma ce ƙasashen waje na neman shiga harkokin siyasar ƙasar.

    Tuni dai shugaba Putin da Firaiministan Hungary suka yi maraba da iƙirarin da jam'iyyarsa tayi na samun nasara a zaɓen.

  3. Masar ta gabatar da wani tayin matakai uku don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta - Rahotanni

    Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Larabawa da na Isra’ila sun ce ƙasar Masar ta gabatar da wani tayin matakai uku da za su kai ga cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin mutanen da Hamas ke tsare da su a Gaza.

    Rahotannin sun ce kashin farko na shirin zai ƙulla tsagaita wuta ta mako biyu, da faɗaɗa ta zuwa mako uku ko huɗu a gaba, da kuma sakin 40 daga cikin mutanen da ake tsare da su, da suka haɗa da mata da ƙananan yara.

    A nata ɓangaren Isra’ila za ta saki fursunoni ɗari daga cikin waɗanda take tsare da su.

    Idan yarjejeniyar ta tabbata dai, za a janye tankokin yaƙin Isra’ila, da kuma bayar da damar shigar da kayan agaji cikin Gaza.

  4. Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

    Hatsarin mota

    Asalin hoton, Getty Images

    Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu a ranar Asabar a wani hatsarin mota a garin Kwanar Gujungu da ke karamar hukumar Taura na jihar Jigawa.

    Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Dutse, a yau Lahadi.

    Shiisu ya ce hatsarin ya afku ne a ranar Asabar da misalin karfe 12:00 na rana, inda motoci biyu, kirar Honda saloon mai lamba NSR 469 AE, da wata motar Golf mai lamba AUY 292 XA suka yi karo da juna.

    Ya ce motar Honda na ɗauke da fasinjoji biyar, sai direbanta mai suna Abdullahi Muhammad, yayin da motar Golf kuma ke ɗauke da fasinjoji huɗu, da direban Safiyanu Mamu.

    Ya ce tawagar ma’aikatan hedikwatar ‘yan sanda ta Taura sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai waɗanda abin ya shafa zuwa babban asibitin garin Taura, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsu.

    Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ahmadu Abdullahi, a madadin sauran jami'an rundunar, ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa ƴan uwansu tare da addu'ar Allah ya gafarta musu.

  5. Hukumar zaɓen Kongo ta yi watsi da zargin tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasar

    Zaɓen Kongo

    Shugaban hukumar zaɓen Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya yi watsi da zargin tafka maguɗi a zaben ƙasar, inda ya ce ya gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen.

    Ɗaya daga cikin manyan ƴan takarar shugabancin ƙasar, Moise Katumbi ya yi kiran a gudanar da sabon zaɓe, kuma ya ce yana da shaidar da ke tabbatar da cewa an tafka maguɗi.

    Sai dai shugaban hukumar zaɓen, Denis Kadina ya shaida wa BBC cewa babu gaskiya a iƙirarin ƴan adawar.

    Ya yi kira ga mutane da su kare ƙuri'ar su saboda suna sane da abinda suka zaɓa.

    Har yanzu dai ba a sanar da sakamakon zaɓen ba.

  6. NDLEA ta kama uwa da ɗanta kan safarar kwayoyi a Legas

    Kwayoyi

    Asalin hoton, NDLEA/X

    Hukumar NDLEA da ke yaki da sha da hana safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ta ce ta kama wata mata mai shekara 70, Selifat Funke Cole, da ɗanta, Babajide Ayorinde Cole, bisa laifin safarar miyagun kwayoyi.

    An kama mutanen biyu ne a Legas a ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba.

    Cikin sanarwa da mai magana da yawun NDLEA Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi, ya ce hukumar ta kai samame a wani gida a unguwar Mushin da ke Legas inda ta kama waɗanda ake zargin ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 117.900.

    “A ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, jami’an NDLEA sun kai samame wani gida a unguwar Mushin a Legas, inda aka kama wata mata mai suna Selifat Cole mai shekaru 70 da ɗanta, Babajide Cole ɗauke da tabar wiwi mai nauyin 117.900,” inji shi.

    Ya ce NDELA tare da haɗin gwiwar jami'an kwastam sun kama kwayoyin Tramadol miliyan bakwai da rabi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, inda ya kara da cewa an yi safarar kayan ne zuwa cikin ƙasar.

    Ya ce an shigo da kwayoyin ne a ranar Juma'a, 22 ga watan Disamba cikin wani jirgin saman Turkiyya.

    Babafemi ya kuma ce sun gano katan 258 na sinadarin codeine da kuma kwali takwas na kwayoyinsa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Ku yi fata mai kyau ba tare da la'akari da mawuyacin hali da ake ciki ba - Akpabio ga ƴan Najeriya

    Akpabio

    Asalin hoton, PRESIDENT OF THE SENATE/TWITTER

    Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da yin fata ba tare da la'akari da mawuyacin hali da suke ciki ba.

    Cikin sakon Kirsimeti da ya aika wa mabiya addinin Kirista, wanda mai taimaka masa kan fannin yada labaru, Eseme Eyiboh ya fitar, Akpabio ya buƙace su da su yi addu'a da yin fata mai kyau saboda haihuwar Yesu Almasihu, inda ya ce Najeriya za ta shawo kan matsaloli da take fuskanta.

    Ya ce wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki, musamman saboda matakai da gwamnati ta ɗauka kan ɓangaren tattalin arziki, za su zamo alheri nan gaba da kuma kawo ci gaba a faɗin ƙasar.

    A cewar Akpabio, Kirsimeti lokaci ne na yin koyi da koyarwar Yesu Kiristi, wajen nuna kauna da kuma zaman lafiya da juna.

    "A madadin iyalina da ƴan mazaɓata, majalisar dattawa da kuma ta wakilai, ina miƙa sakon murnar bikin Kirsimeti ga dukkan Kiristoci.

    Ya buƙaci ƴan Najeriya da kada su cire rai kan shugabanninsu, musamman ma gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

    Akpabio ya ce yana da kwarin gwiwar cewa da haɗin kan ƴan Najeriya, gwamnati mai ci za ta share hawayen ƴan ƙasar nan ba da jimawa ba.

  8. Beijing na fuskantar tsananin sanyi da zubar kankara

    Beijing

    Asalin hoton, Reuters

    Beijing, babban birnin China na fama da tsananin sanyi da kuma zubar kankara.

    Sanyin ya tsananta a wannan wata na Disamba, inda rabon a fuskanci haka tun 1951.

    Hukumar kula da yanayi ta ƙasar yanayi ya yi ƙasa da maki 10 na ma'aunin celsius cikin kwanaki tara a jere.

    A cewar rahotanni, dutsar kankara da ke zuba ta rufe wasu tituna har da layin dogo na jiragen ƙasa.

    Ana sa ran ci gaba da fuskantar yanayin sanyi a Beijing har nan da kwanaki masu zuwa.

    kankara

    Asalin hoton, EPA

    kankara

    Asalin hoton, EPA

  9. Muhimmancin abarba ga lafiyar ɗan'adam

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo

    Masana harkokin cimaka sun ce abarba na ƙunshe da wasu sinadarai da ke taimaka wa jikin ɗan'adam, musamman wajen ƙarin kuzari.

    Masanin abinci Nuhu Jibrin Bala ya ce abarba na da sinadarin Vitamin C mai gina garkuwar jiki.

    Haka nan, tana da sinadarin da ke samar da harza wanda shi kuma ke taimaka wa jiki daidaituwa, sannan ya taimaka wajen niƙa abinci a cikin mutum.

    Sai dai kuma, ya ce ya kamata mutanen da ke fama da saurin lalacewar ciki ko kuma gudawa su guji abarba. Su ma masu ɗauke da cutar ulcer, ya kamata su haƙura da abarba musamman maras zaƙi.

  10. Isra'ila na shan wahalar gaske a yaƙin Gaza - Netanyahu

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Firaminista Benjamin Netanyahu ke nan lokacin da yake jagorantar zaman majalisar ministocinsa ranar Lahadi a birnin

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa na fuskantar "wahalar gaske" a yaƙin da take yi a Zirin Gaza.

    Rundunar sojin ƙasar ta ce an kashe mata ƙarin dakaru 14 a yankin na Falasɗinawa tun daga ranar Juma'a, inda jimillarsu ta zama 153 tun bayan fara kai hare-hare ta ƙasa a zirin.

    Asabar na ɗaya daga cikin mafiya muni ga dakarun - amma Netanyahu ya ce dakarunsa "ba su da wani zaɓi" illa su ci gaba da fafatawa.

    "Wannan safiya ce [Lahadi] mai wuya bayan shafe rana guda ana tafka faɗa mai wuyar gaske," in ji shi.

    A gefe guda kuma, ma'aikatar lafiya a Gaza - ƙarƙashin mulkin Hamas - ta ce an kashe ƙarin mutum 166 cikin awa 24 da suka wuce a Gaza.

    Ta ce an kashe sama da Falasɗinawa 20,000 - akasarinsu mata da ƙananan yara, tare da raunata wasu 54,000 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

  11. Ina sane da sadaukarwar da kuke yi saboda sauye-sauyen gwamnatina - Tinubu

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce yana sane da irin "sadaukarwar" da 'yan ƙasar ke yi game da sauye-sauyen da gwamnatinsa take aiwatarwa tun bayan hawansa mulki a watan Mayu.

    Cikin saƙon Kirsimeti da ya aika wa mabiya addinin Kirista, shugaban ya nemi 'yan Najeriya su yi amfani da lokacin bikin da kuma hutu wajen "lura da 'yan uwa saboda akwai waɗanda za su iya shiga cikin ƙunci, ko makoki, ko kuma waɗanda suka gaza cimma wani burinsu".

    Haka nan, ya bayyana 2023 a matsayin "shekarar sauyi a ƙasarmu", yana mai cewa "ina sane cewa sauye-sauyen da suka zama tilas da muke aiwatarwa don samun ƙasa mai yalwa da arziki sun jawo sadaukarwa ta musamman".

    Ya ce: "Ina ƙarfafa muku gwiwa cewa nan gaɓa kaɗan, cikin jajircewarmu, za mu wayi gari cikin wata rana mai cike da zaman lafiya, da cigaba mai ɗorewa."

    Ya kuma nemi 'yan Najeriya su yi amfani da damar wajen yi wa dakarun ƙasar maza da mata addu'a . "Allah ya kare su, ya mayar da su wajen iyalansu lafiya," in ji shi.

    Wannan ne bikin Kirsimeti na farko da shugaban zai yi a kan karagar mulki, wadda ta zo wa 'yan Najeriya cikin ƙalubalen cire tallafin man fetur, da tsadar kayayyaki, da taɓarɓarewar matsalar tsaro.

  12. Akwai ruɗani game da 'wasikar' da Sheikh Dahiru Bauchi ya rubuta kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano

    Sheikh Dahiru Bauchi

    Ga alamu akwai ruɗani da kuma rabuwar kai game da sahihancin wasiƙar da aka ce jagoran ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi, ya rubuta yana neman Kotun Ƙolin Najeriya ta yi adalci a shari'ar zaɓen gwamnan jihar Kano.

    A ranar Juma'a ne wasiƙar mai ɗauke da sa hannun shehin malamin ta karaɗe shafukan intanet da kwanan watan 1 ga watan Disamban 2023, wadda kuma aka rubuta wa Babban Alƙalin Najeriya Olukayode Ariwoola.

    A ranar Asabar ɗaya daga cikin 'ya'yan malamin mai suna Naziru Dahiru ya tabbatar wa da BBC Hausa cewa da gaske mahaifinsa ne ya rubuta wasiƙar.

    Sai da kuma, jim kaɗan bayan wasu kafofin yaɗa labarai sun wallafa labarin, Sheikh Bashir Dahiru - wani daga cikin 'ya'yan malamin - ya faɗa wa BBC Hausa cewa takardar ba ta gaskiya ba ce.

    "Yadda kuka ga takardar nan haka muka gan ta, shehi ya ce ba shi ne ya rubuta ta ba, bai san da ita ba," kamar yadda ya bayyana a hirar da aka yaɗa a labaran BBC na safiyar yau Lahadi.

    Har wa yau, an ji wani saƙon murya ta Sheikh Dahiru Bauchi da kansa yana musanta rubuta wasiƙar, yana mai cewa bai san da ita ba kuma ba daga wajensa ta fita ba.

    A gefe guda kuma, Naziru Dahiru Bauchi ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Facebook - mai suna Naziru Tahir - ranar Lahadi yana jaddada iƙirarin cewa shi ne ya kai wa kotun ƙoli wasiƙar da hannunsa bayan mahaifin nasa ya amince da ita.

    "Ni ne wanda shehi ya aika na kai wasiƙa wajen babban alƙali wadda take yawo a soshiyal midiya [shafukan sada zumunta], kuma na kai, sun ba ni takardar cewa sun karɓa," a cewarsa.

    Sai dai ya tabbatar da cewa shi ne da kansa ya je ya nemi mahaifin nasa ya saka baki a batun shari'ar don ya yi kira da a yi adalci.

    "Manyan ƙasa suna ta saka baki, suna kiran a yi adalci, shi ne muke neman izininku ku ma ku ja hankali lallai cewa ba a son abin da zai taɓa Kano, idan wani abu ya taɓa Kano zai taɓa ƙasa duka," kamar yadda aka ji Nazirun yana faɗa wa mahaifin nasa ta waya a cikin bidiyon da ya wallafa.

    Sai dai ba a ji amsar da mahaifin nasa ya ba shi ba kafin ya katse sautin, kuma kalaman nasa sun yi kama da waɗanda wasiƙar ta ƙunsa.

    Wasiƙar Dahiru Bauchi

    Asalin hoton, Social Media

  13. Amurka ta ce ta daƙile hari a Tekun Maliya daga 'yan tawayen Houthi

    Houthi

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Hoton wani jirgi maras matuƙi na boge da mayaƙan Houthi suka ƙirƙira a Yemen

    Rundunar sojan Amurka ta ce wani jirgin ruwan yaƙinta ya harbo jirage marasa matuka hudu a cikin tekun Bahar Maliya, wadanda aka harba daga yankunan kasar Yemen da ke karkashin ikon Houthi.

    'Yan tawayen na Houthi na samun goyon bayan Iran, waɗanda ke iko da kashi mai yawa a Yemen tun bayan fara yaƙin basasa.

    Rundunar ta bayyana haka ne a shafin ta na dandalin X, inda ta ƙara da cewa an kai wa wani jirgin dakon ɗanyen mai na ƙasar Gabon,mai ɗauke da tutar ƙasar Indiya hari. Sai dai babu wanda ya ji rauni.

    Ko a ranar Juma'a, ma'aikatar tsaron ta Amurka ta zargi Iran da ƙaddamar harin jirgi maras matuƙi kan wani jirgin dakon mai a gaɓar Tekun Indiya.

  14. Za mu ci gaba da yaƙi a Gaza har sai mun cimma muradanmu - Netanyahu

    Benjamin Netanyahu

    Asalin hoton, EPA

    Rundunar sojin Isra'ila ta ci alwashin ci gaba da yaƙi a Gaza, amma ta amince cewa yaƙin na da "wahala" kuma ba ya "sauri".

    Mai magana da yawun rundunar ya faɗa a ƙarshen makon nan cewa sun faɗaɗa "farmaki ta ƙasa a arewaci da kudancin Gaza".

    A gefe guda kuma, Amurka ta ce Shugaba Biden ya yi magana da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu kuma "ya jaddada buƙatar" kare rayukan fararen hula.

    A martanin da ya mayar, Netanyahu ya ce za su ci gaba da yaƙin har sai sun cimma dukkan muradan da suka sa a gaba.

    Kazalika, rundunar ta sanar da cewa an kashe ƙarin sojojinta tara a harin da suka kai Gaza, wanda ya kawo jimillar dakarunta da aka kashe a cikin Gaza zuwa 154.

    Isra'ila ta ce ta kama mayaƙan Hamas 700 tun bayan da ta fara kai hare-hare da zimmar kawar da ƙungiyar.

    Sai dai Hamas ta ce akasarin waɗanda Isra'ila ke kashewa mata ne da ƙananan yara.

  15. Sabbin matakan tsaro da muka ɗauka a Najeriya - Minista Matawalle

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Shirin Gane Mini Hanya:

    Filin Gane Mini Hanya na wannan makon ya tattauna da Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle game da matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

    A hirar tasa da Awwal Janyau, ministan ya ce daga cikin matakan har da bai wa sojoji umarnin farautar 'yan fashin daji ba tare da sun jira umarni daga Abuja ba.

  16. Birtaniya za ta aika da jirgin ruwan yaƙi zuwa Guyana

    Jirgin ruwan yaƙi

    Asalin hoton, PA Media

    Biritaniya za ta aike da jirgin ruwan yaƙi zuwa asar Guyana a wani mataki na nuna goyon bayan diflomasiyya da kuma soja ga kasar da ta yi wa mulkin mallaka a yankin Latin Amurka.

    Matakin na zuwa ne bayan makwabciyarta Venezuela ta sabunta ikirarinta na tsawon shekaru 100 kan wani yanki na Guyana da ake takaddama a kai.

    Ministan harkokin wajen Biritaniya ya yi alkawarin ba da goyon bayan ƙasarsa ga Guyana a ziyarar da ya kai kudancin Amurka a farkon makon nan.

    Wakilin BBC ya ce Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya yi barazanar mamaye yankin Esquibo mai arzikin mai, lamarin da ya haifar da fargabar mamaya da kuma yaƙi.

  17. Hamas na zargin Isra'ila da yi wa Falasɗinawa 130 kisan gilla a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar Hamas ta zargi sojojin Isra'ila da aiwatar da kisan gilla a zirin Gaza.

    Cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce ta samu bayanan shaidun gani-da-ido na cewa sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa sama da 137 a arewacin yankin da kuma Birnin Gaza, suka sanya su cikin manyan ramuka tare da harbe su.

    Wakilin BBC ya ce sun kuma zargi sojojin na Isra'ila da kashe ƴan jarida sama da 100, da mata masu ciki a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa asibiti a arewacin Gaza.

    Rundunar sojin ta Isra'ila ta ce ba ta da masaniya kan lamarin.

    Hamas ta ce hukuncin kisan wani ɓangare ne na kisan kiyashin da Isra'ila ke yi wa al'ummar Falasdinawa.

  18. Maraba

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye.

    Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan hantsi na Lahadi.