Hare-haren Isra'ila sun kashe gomman Falasɗinawa ranar Juma'a da dare

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. 'Ɓangarorin da ke rikici da juna a Yemen sun amince da buƙatar tsagaita wuta'

    Yemen

    Asalin hoton, EPA

    Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar Yeman Hans Grundberg, ya ce ɓangarorin da ke rikici da juna a ƙasar sun amince da shirin tsagaita wuta.

    An kashe dubban ‘yan ƙasar ta Yemen a kusan shekaru goma da aka kwashe ana yaƙi tsakanin ‘yan tawayen Houthi da Iran ke mara wa baya.

    Mista Grundberg ya ce hakan zai bayar da damar biyan ma'aikata albashi da buɗe hanyoyi a yankunan da ƴan tawaye suke rike da su da kuma komawa fitar da mai.

  3. Harin ƴan tawaye ya kashe fararen hula 20 a Burundi

    Gwamnatin Burundi ta ce harin 'yan tawaye a wani gari da ke yammacin ƙasar ya kashe fararen hula ashirin.

    Ƙungiyar Red Tabara ta sanar da ɗaukar alhakin kai harin, ta kuma kara da cewar ta kai hari sansanin soji tare da kashe jami'an tsaro 10.

    Ƴan tawayen sun fara yakar gwamnatin Burindi tun lokacin da shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar da aniyar tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar karo na uku a shekara ta 2015.

    Ƴan tawayen waɗanda suka addabi ƙasar da hare-hare a baya-bayan nan, sun yi sansani a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.

  4. Isra'ila ta ce ta kama ɗaruruwan ƴan ƙungiyar Hamas da Islamic Jihad

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta ce ta kama ƴan ƙungiyar Hamas da Islamic Jihad 200 a cikin makon da ya gabata tare da kai su cikin ƙasarta don yi musu tambayoyi.

    Wata sanarwa da Isra'ilar ta fitar, ta ce wasu daga cikin waɗanda ake zargin sun ɓoye a cikin fararen hula, inda suka miƙa wuya bisa raɗin kansu.

    Isra'ila ta ce an kama mayaka Falasɗinawa 700 tun bayan kaddamar da farmakin soji da kuma mamaye Gaza da nufin kawar da ƙungiyar Hamas.

    Hamas ta ce Isra'ila na kashe mata da yara. Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da iƙirarin ba.

    A baya dai Isra'ila ta jaddada cewa ta ɗauki matakin kaucewa asarar rayukan fararen hula.

    Fiye da mutane 20,000 ne aka kashe yayin da 53,000 suka jikkata a Gaza tun bayan kaddamar da harin ramuwar gayya da Isra'ila ta yi zuwa Gaza, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas.

    Sanarwar ta a ranar Asabar ta ce an kashe wasu mutane 201 tare da jikkata wasu 368 a ranar Juma'a kaɗai.

  5. Jirgi mara matuki ya kai wa jirgin ruwan dakon kaya hari a tekun Indiya

    Indiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jirgi mara matuki ya kai wa jirgin ruwan dakon kaya a gaɓar tekun jihar Gujarat da ke yammacin Indiya a ranar Asabar.

    Jirgin ruwan ɗauke da tutar ƙasar Laberiya yana da alaka da Isra'ila, a cewar wani kamfanin tsaron teku mai suna Ambrey, kuma yana kan hanyarsa daga Saudiyya zuwa Indiya.

    Harin ya haddasa gobara a cikin jirgin wanda aka samu nasarar kashewa, amma babu wanda ya jikkata cikin ma'aikatan jirgin kusan 20.

    Hakan dai na zuwa ne bayan jerin hare-haren da jiragen ruwa marasa matuka da na rokoki da ƴan tawayen Houthi da Iran ke mara wa baya suka kai kan jiragen ruwa a tekun Bahar Rum.

    Ƙungiyar da ke iko da yawancin sassan ƙasar Yemen, ta kai hare-hare da jirage marasa matuka da makamai masu linzami sama da 100 kan jiragen ruwa 10, a cewar jami’an Amurka.

    Ƴan tawayen sun yi iƙirarin cewa Isra'ila suke kai wa hari saboda yaƙin Gaza.

    Yawancin ƙungiyoyin jigilar kayayyaki na duniya sun dakatar da ayyukansu a tekun Bahar Maliya saboda karuwar hare-hare.

  6. Man United ta kara yin tuntuɓe a Premier League

    United

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta ci gaba da fuskantar kalubale a gasar Premier ta bana, inda West Ham ta doke ta da ci 2-0 a wasan mako na 18.

    West Ham ta ci kwallonta ta farko ne ta hannun Jarrod Bowen a minti na 72, kafin daga bisani Mohammed Kudus ya ƙara ta biyu a minti na 78.

    Rabon da United ta fuskanci irin wannan koma-baya tun 1930.

    Rashin nasara da ta yi a hannun West Ham ita ce ta 13 a dukkan fafatawa a kakar wasanni ta bana.

    Ƙungiyar ta Old Trafford ta kasa zura kwallo a cikin wasa huɗu a jere a dukkan fafatawa, wanda rabon haka tun watan Nuwamban 1991 lokacin kociyanta Sir Alex Ferguson.

  7. Abincin bikin Kirsimeti ya sa ma'aikatan kamfanin jirgin sama amai da gudawa

    Abincin kirsimeti

    Asalin hoton, Getty Images

    Sama da ma’aikatan kamfanin jirgin sama 700 ne aka yi imanin sun kamu da rashin lafiya sakamakon liyafar cin abincin Kirsimeti da kamfanin ya yi, in ji hukumomin lafiya a Faransa.

    Ma'aikata kamfanin jiragin saman a yammacin Faransa sun yi ta amai da gudawa.

    Ba a dai san abin da ke cikin abincin da suka ci ba a wurin bikin na Kirsimeti wanda kuma ya ruɗa musu ciki kafin isowar bikin.

    Kamfanin jirgin saman ya shaida wa BBC cewa kusan ma'aikata 100 ne suka kamu da rashin lafiya.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar, kamfanin ya ce yana haɗa kai da hukumomi don gano abin da ya ruɗa cikin ma'aikatansa da kuma tabbatar da hakan bai sake faruwa ba nan gaba.

    Kamfanin na da reshen kera jiragen sama mafi girma a duniya, kuma yana da ma'aikata 15,000 a ƙasashe biyar.

    Hukumomin lafiya ba su bayar da cikakken bayani game da ainihin abincin da ya ruɗa cikin ma'aikatan ba a liyafar cin abincin da aka yi a makon da ya gabata ba.

    Ana ci gaba da gudanar da bincike don gano abin da ke kunshe cikin abincin.

  8. Sojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 52 da aka yi garkuwa da su a Sokoto

    Sojoji

    Asalin hoton, Nigerian Army/X

    Rundunar sojin Najeriya ta Hadarin Daji ta sake kuɓutar da mutum 52 da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Isa na jihar Sokoto.

    Sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce ta samu nasarar ceto mutanen ne a ranar Juma'a 22 ga watan Disamba, a ci gaba da samame da take yi a maɓoyar ƴan ta'addan.

    Sojojin sun ce sun kuma samu nasarar kashewa tare da lalata wuraren da ƴan ta'ddan a kauyukan Saruwa, Kubuta, Gundumi da kuma dajin Bunwanga da ke jihar ta Sokoto.

    Mutanen da aka kuɓutar ɗin sun haɗa da maza 14, mata 32 da kuma yara guda biyu.

    Dakarun sun ce za a duba lafiyar mutanen kafin miƙa su ga hukumomi domin su sake haɗuwa da iyalansu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Hari ya kashe Falasɗinawa uku da raunata shida a sansanin Al-Bureij - PCRS

    Dakarun sojin Isra'ila sun kai wa wani gida hari tare da kashe mutum uku a tsakiyar Zirin Gaza, a cewar ƙungiyar agaji ta Red Crescent (PCRS).

    Ƙungiyar ta ce ta kwashe mutum shida da aka raunata da waɗanda aka kashe zuwa asibiti.

    An kai harin ne a sansanin 'yan gudun hijira na Al-Bureij.

  10. Hanyoyin kamuwa da cutar hangum da illolinta

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Shirin Lafiya Zinariya:

    Filin Lafiya Zinariya na wannan makon ya tattauna kan hanyoyin da yara ke kamuwa da cutar hangum mai kama da mura.

  11. An saki Emefiele daga gidan yari bayan ya cika sharuɗɗan beli

    Godwin Emefiele

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Godwin Emefiele ya bayyana a kotu ranar 17 ga watan Agusta kan zarge-zargen karya dokar sayen kayayyakin gwamnati

    Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya koma gida bayan ya cika sharuɗɗan belin da kotu ta ba shi.

    Mai magana da yawun Gidan Yari na Kuje da ke Abuja, inda aka tsare Mista Emefiele, ya tabbatar da cewa an saki tsohon gwamnan a yammacin Juma'a.

    Tun a ranar 22 ga watan Nuwamba ne Babbar Kotun Tarayya ta ba da belinsa kan naira miliyan 300 tare da gabatar da mutum biyu da ke da kadarori a unguwar Maitama da ke birnin na Abuja. Haka nan, kotun ta umarce shi da miƙa mata dukkan takardunsa na tafiye-tafiye.

    Lamarin na zuwa ne bayan wani rahoto da mai bincke na musamman, Jim Obazee, ya zarge shi da karya dokar kwangila da sayen kayayyakin gwamnati.

    Rahoton Obazee, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a watan Yuli don ya binciki CBN a ƙarƙashin mulkin Emefiele, ya zarge shi da amfani da wakilansa wajen sayen Bankin Union, da kuma yin amfani da ƙarfin ikonsa a cinikin bankunan Polaris da Keystone.

    Gwamnatin Tinubu na zargin tsohon gwamnan wanda ta dakatar a watan Yuni da aikata almundahanar kuɗi naira biliyan 1.2, zargin da ya musanta.

  12. Mace mai mahaifa biyu ta haifi 'yan biyu cikin kwana biyu

    Kelsey Hatcher da jariranta

    Asalin hoton, Andrea Mabry/ University of Alabama Birmingham

    Wata mace mai mahaifa da ba a saba gani ba ta haifi jarirai biyu cikin kwana biyu bayan ta shafe awa 20 tana naƙuda a Amurka.

    Kelsey Hatcher mai shekara 32 ta haifi jaririyar farko ranar Talata, ta haifi ta biyu Laraba asibitin Jamia'r Alabama da ke Birmingham.

    Da take bayyana haihuwar jariran da ta kira "ikon Allah" a shafinta na sada zumunta, Ms Hatcher ta yaba wa likitocin a matsayin "masu jajircewa".

    An bayyana jariran a matsayin 'yan biyu duk da cewa ba ranar haihuwarsu ɗaya ba.

    Tun da farko ta zaci za ta haihu ne a Ranar Kirsimeti, amma yanzu ta ce ta koma gida kuma za su yi "bikin ƙarshen shekara a gida".

    Tun tana shekara 17 aka shaida mata cewa tana da mahaifa biyu, yanayin da asibitin UAB ya fassara da cewa mata kashi 0.3 ne cikin 100 ke da shi.

    Kazalika, asibitin ya ƙara da cewa yiwuwar samun ciki a duka mahaifa biyun ba ta wuce ɗaya cikin miliyan ba.

    Likitan da ya karɓi haihuwar tata ya ce "an ɓarke da sowa a ɗakin" lokacin da jaririyar farko ta fito da misalin ƙarfe 7:45 na yammacin yankin a ranar 19 ga watan Disamba.

    Sai dai an ciro ta biyun ne ta hanyar tiyata sama da awa 10 bayan ta farko, da misalin ƙarfe 6:10 na safiyar washegari.

    Jariran Kelsey Hatcher

    Asalin hoton, @UABNews

  13. Sabbin matakan tsaro da muka ɗauka a Najeriya - Minista Matawalle

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Shirin Gane Mini Hanya

    Filin Gane Mini Hanya na wannan makon ya tattauna da Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle game da matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

    A hirar tasa da Awwal Janyau, ministan ya ce daga cikin matakan har da bai wa sojoji umarnin farautar 'yan fashin daji ba tare da sun jira umarni daga Abuja ba.

  14. Ƙungiyar agaji ta PRCS ta ce Isra'ila na tsare da ma'aikatanta tsawon wata ɗaya

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ma'aikacin agaji na PRCS yake taimaka wa wani dattijo a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan na Falasɗinu a watan Yulin 2023

    Ƙungiyar agaji ta Red Crescent Society a yankunan Falasɗinawa (PRCS) ta ce har yanzu dakarun Isra'ila na tsare da ma'aikatanta a arewacin Zirin Gaza.

    "Sama da wata ɗaya ke nan tun bayan kama abokin aikinmnu Awni Khattab, shugaban tashar motocin jinya ta PRCS a Khan Younis," in ji ƙungiyar cikin wani saƙo a dandalin X.

    "Muna neman ƙasashen duniya su matsa wa dakarun mamaya don sako abokan aikinmu nan take da kuma kare rayukansu."

  15. Ana makokin mutum 14 da ɗan bindiga ya kashe a Jami'ar Prague

    Prague

    Asalin hoton, EPA

    A yau ne ake gudanar da zaman makoki a Jamhuriyar Check bayan harin da aka kai ranar Alhamis a Jami'ar Prague.

    Za a sassauta tutocin ƙasar a gine-ginen gwamnati, za kuma a yi shiru na minti ɗaya da tsakar rana.

    Mutane goma sha huɗu ne wani ɗan bindiga ya harbe a jami'ar, wanda daga bisani shi ma ya kashe kansa.

    Ana kuma zargin ɗan bindigar ya kashe mahaifinsa a ranar, da wasu mutane biyu a wani daji da ke kusa da Prague a makon da ya gabata.

  16. CBN ya cire haramcin amfani da kuɗin crypto a bankunan Najeriya

    Kuɗin crypto

    Asalin hoton, Reuters

    Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma'a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

    CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

    "A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta'addanci," in ji sanarwar.

    "Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs)."

    Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

    Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu.

  17. 'Ƙudirin Kwamatin Tsaro zai taimaka duk da bai samar da mafita ba a Gaza'

    kwamitin tsaro na Kwamatin Tsaro na MDD

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Kwamitin Tsaro na Kwamatin Tsaro na MDD ya ce kodayake ƙudurin neman kai kayan agaji da suka amince da shi bai samar da mafitar siyasa ta nan take ba a Gaza, zai magance mummunar matsalar ayyukan jin-ƙai da ake fuskanta.

    Hose dola Gasca wanda ya ziyarci sansanin ƴan gudun hijirar Falasdinawa da ke kusa da mashigar Rafah, ya shaida wa BBC cewa babu wasu kalmomi da za a iya amfani da su wajen bayyana irin halin da ake ciki a yankin.

    "Ina tsammanin wannan wani mataki ne na cimma gagarumar nasara, musamman a ɓangaren shigar da kayan agaji, ina ganin an samu gagarumar nasara," in ji shi.

    A yammacin Juma'a ne Kwamatin ya amince da ƙudirin bayan mambobi 13 sun kaɗa ƙuri'ar amincewa, inda Amurka da Rasha suka ƙaurace wa ƙuri'ar.

  18. Hare-haren Isra'ila sun kashe gomman Falasɗinawa ranar Juma'a da dare

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Luguden wutar da Isra'ila ke yi a kan Zirin Gaza ya ci gaba babu ƙaƙƙautawa ranar Juma'a da dare, yayin da rahotonni ke bayyana sabbin hare-hare a yankuna da dama.

    Wani hari da aka kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat ya kashe aƙalla mutum 18, a cewar wata kafar yaɗa labarai ta Falasɗinawa.

    Sojojin Isra'ila sun umarci wasu mutanen da dama a sansanin Bureij su yi hijira zuwa kudancin Gaza yayin da suke ci gaba da kai hare-hare ta ƙasa.

    Duk da ƙudirin da Kwamatin Tsaro na MDD ya amince da shi na kiran kai kayan agaji masu yawa a Gazan, ƙudirin ya gaza wajen yin kiran a tsagaita wuta nan take.

    Kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ce an kashe mutum 18 ɗin ne yayin hari a kan wani gida da ke Nuseirat, inda kuma aka jikkata wasu gommai.

    Haka nan, hari ta sama ya lalata wata matatar ruwan sha a sansanin Jabalia da ke arewacin Gaza.

  19. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyarmu a BBC Hausa, barkanmu da hantsin Asabar. Barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye.

    Za mu kawo muku rahotonni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan safiya.