Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ecowas ta kafa sharaɗin rage wa Nijar takunkumai

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Hikayata 2023: Labarin BAƘIN KISHI

    A wannan mako mun kawo muku labarin Bakin Kishi na Aisha Abdullahi Yabo, wadda ta zo ta biyu a gasar Hikayata ta bana.

    Ta rubuta labarin nata ne kan yadda mata ke rufe idanunsu, a kan kishi, ta yadda suke abubuwan da daga baya za su yi da-na-sani

  2. An buƙaci sojojin Isra'ila su ci gaba da kai hare-hare Gaza

    Shugaban rundunar sojin Isra'ila ya sake zaburar da sojojinsu a kan su ƙara ƙaimi a Gaza.

    Janar Herzi Halevi, ya shaida wa dakarunsu a yayin wani taro a birnin Kudus cewa akwai alamomin da ke nuna cewa Hamas ta fara sanyi bayan watanni biyu da aka shafe ana ruwan bama-bamai a Zirin Gaza.

    ga wasu bidiyo na nuna yadda Falasɗinawa ke miƙa wuya ga sojojin Isra'ila a arewacin Gaza.

    To amma akwai alamar tambaya akan wani bidiyo ɗaya nuna yadda wani mutum ya ajiye maƙaminsa a gaban sojojin.

    Wasu bidiyo biyu da aka nuna sun ci karo da juna bayan da aka nuna wani mutum na miƙa makaminsa ɗaya da hannunsa na hagu ɗayan kuma da hannunsa na dama.

  3. Amurka za ta sayar wa Isra'ila makamai

    Amurka ta amince da a gaggauta sayar wa Isra'ila makamai, batun da aka jima ana muhawara a kansa a majalisar dokkin ƙasar.

    Takaddamar da aka yi tsakanin mambobin jam'iyyar Republican da na Democrats kan tsaron iyakar kasar da Mexico a majalisar shi ne ya hana amincewa da bai wa Isra'ila da Ukraine taimakon da suke buƙata.

    Daga cikin makaman akwai tankokin yaƙi 13 da sauran taimakon soji da kuɗinsu zai kai fiye da dala miliyan dari.

    Cikin wani jawabi da ya gabatar, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya tabbatar wa majalisar cewa akwai buƙatar Amurka ta taimaka wa Isra'ila don ta kare kanta.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a wannan safiya ta Lahadi, domin kawo muku labaran wasu abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya.

    Kada ku manta da tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.

    Ku biyo mu...