Ƙarshen rahotonni
Nan za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Za mu kawo muku wasu sababbi gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ke fatan mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Nan za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Za mu kawo muku wasu sababbi gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ke fatan mu kwana lafiya.
Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas, ta naɗa wata tawaga da za ta tattauna da sojojin mulkin Nijar bayan juyin mulkin watan Yuli.
Yayin taron da ta gudanar a Abuja babban birnin Najeriya, Ecowas ta ce za ta duba yiwuwar rage takunkuman da ta sanya wa ƙasar idan sojoji suka amince da mayar da mulki ga farar hula cikin ƙanƙanin lokaci.
Shugabannin ƙasar Benin, da Saliyo, da Togo ne za su jagoranci tattaunawar, inda za su matsa wa sojojin na Nijar wajen amincewa da jadawali "mai yiwuwa kuma na ɗan lokaci" don mayar da mulki ga farar hula.
Wakilin BBC ya ce wannan mataki ya sha bamban da wanda Ecowas ta ɗauka a watan Agustan da ya gabata, wanda ta yi barazanar ɗaukar matakin soja kan sojojin mulkin idan ba su sauka daga mulki ba nan take.
A kwanan nan, Burkina Faso, da Nijar, da Mali suka amince da kafa wani ƙawancen tsaro da kuma haɗaka ta siyasa.
Ana ganin Ecowas za ta yi fargabar ƙawance tsakanin waɗannan ƙasashe uku da sojoji ke mulki tsakaninsu da ƙasar Rasha.
Kungiyar haɗin kan ƙasashen gabashin Afirka ta Igad ta ce ɓangarori biyun da ke yaƙi da juna a Sudan za su yi tattaunawar ido da ido domin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce jagororin biyu sun amince a kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar tattaunawar diflomasiyya.
Sanarwar ta ce shugaban RSF da aka kira a waya yayin tattaunawar ya ce shi ma ya amince cewa za a iya kawo ƙarshen yaƙin ne ta hanyar zama a tebirin sulhu.
Wakilin BBC ya ce a baya an yi ta ƙoƙarin tattaunawar samar da zaman lafiya amma hakan ya ci tura, wadda aka yi a baya ta shigar da kayan agaji ma ba ta ɗauki wani dogon lokaci ba.
Sama da mutum miliyan shida ne suka rasa muhallansu a Sudan sanadin yaƙin da aka fara tun a watan Afrilu.
Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD a Palasdinu ya zargi Isra'ila da koƙarin kora mazauna Gaza su koma Masar.
Janar Phillippe Lazarrini ya shaida wa wata jaridar Amurka cewa umartar Falasdinawa da aka yi su koma kudancin daga arewaci da ake yaƙi alama ce ta farko kan wannan zargi.
Abu na biyu kuma shi ne tursasa musu komawa iyakar Masar da aka yi daga kudancin Gaza saboda yawan hare-hare.
"Muna ta cewa mutane su koma wurarensu na ainihi da suka fito. Amma tambayar a nan ina za su je? an lalata musu komai," in ji shi.
Ya ƙara cewa idan aka ci gaba da haka za a wayi gari babu Bafalasdine ko daya a Gaza.
Joradan ma ta yi irin wannan zargi a ranar Lahadi, sai dai kakakin gwamnatin Isra'ila ya musanta hakan.
Misrawa na kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa, wanda ake sa ran Shugaba Abdul Fattah al-Sisi zai lashe a karo na uku.
Duk da ƙarancin goyon bayan da yake da shi a ƙasar, Misrawa ba su da wani zaɓi mai yawa a zaɓen da ake ganin Mista Sisi zai sake samun zangon mulki na shekara shida.
'Yan adawa na ƙarafin cewa ba su iya yin adawa a fili saboda yadda ake yawan tanƙwara su.
Duk da cewa akwai mutum uku da ke yin takara da shugaban, mutane da yawa na ganin za a murɗa sakamakon zaɓen don bai wa Sisi nasara.
Firaministan Qatar ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da matsa wa Isra'ila da Hamas lamba don su sake ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta "duk da wuyar lamarin".
Yarjejeniyar mako ɗaya da aka ƙulla ta sa an sako gomman mutanen da Hamas ke tsare da su da kuma fursunonin Falasɗinawa da Isra'ila ta kama, wanda Qatar ta jagoranci ƙullawa.
Da yake magana a taron Doha yau Lahadi, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani ya ce an sako mutanen ne daga Gaza ba don ƙarfin sojan Isra'ilba ba, sai don tattaunawar da aka yi.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da tattaunawar shiga tsakani duk da hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa, waɗanda ke "rufe ƙofofin sasantawa" don cimma manufar. Amma ba za mu yanke ƙauna ba," in ji al-Thani.
Ma'aikatar lafiya ta Gaza - ƙarƙashin ikon Hamas - ta bayar da rahoton cewa kusan Falasɗinawa 18,000 ne mutu sakamakon hare-haren Isra'ila tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.
Al Jazeera ta ruwaito mai magana da yawun ma'aikatar Ashraf al-Qudra yana cewa an raunata wasu aƙalla 49,500.
Ya faɗa kafar talabijin ɗin cewa cikin awa 24 da suka gabata, an kashe mutum 297 tare da jikkata 550.
Ƙasashen Turai da dama sun haramta ayyukan ƙungiyar Hamas, inda suke kallonta a matsayin ta 'yan ta'adda. Amma MDD tana ɗaukar alƙaluman da take fitarwa a matsayin a matsayin sahihai.
Firaministan Falasɗiinawa Mohammad Shtayyeh ya nemi ƙasashen duniya su saka wa Isra'ila takunkumai saboda luguden wutar da take yi a kan Zirin Gaza.
Da yake magana a taron Doha na Qatar - tare da sauran shugabanni - Shtayyeh ya ce: "Bai kamata a ƙyale Isra'ila ta ci gaba da karya dokokin ƙasashen duniya ba."
"Babbar damuwarmu ba wai ranar kammala yaƙin ba," kamar yadda kafar Al Jazeera ta ruwaito shi yana bayyanawa. "Yanzu ne. Muna son a kawo ƙarshen ɓarna da kuma kisan ƙare-dangin da ake yi a yau."
Shtayyeh ya kuma shawarci MDD "ta nema ƙarara cewa dole ne a kawo ƙarshen mamayar da Isra'ila take yi wa yankunan Falasɗinawa".
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya shaida wa shugaban Rasha Vladimir Putin cewa bai gamsu da matsayin da Moscow ta ɗauka ba a yaƙin Gaza.
A ranar Juma'a ne Rasha ta goyi bayan ƙudurin gaggauta tsagaita wuta a Gaza a taron kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duiya.
A lokacin tattaunawar da suka yi ta waya da safiyar yau Lahadi, Netenyahu, ya soki ''ƙawance mai hatsari'' da ke tsakanin Rasha da Iran.
Natenyahu ya gaya wa Putin cewa duk ƙasar da aka kai wa hari irin na 7 ga watan Oktoba to dole ne ta mayar da martani da aƙalla irin matakin da ta ɗauka.
Firaministan na Isra'ila ya bayyana jin ɗaɗinsa kan yadda Rasha ta yi yunƙuri har aka saki 'yan ƙasarta biyu da ke cikin mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.
A nata ɓangare fadar gamnatin Rasha ta ce a shirye ƙasar take wajen bayar da duk wata gudunmowa da za ta kawo ƙarshen tashin hankalin.
Sannan shugaba Putin ''ya sake jaddada matsayinsa na rashin amincewa da kuma Allah wadai da duk wani nau'in ta'addanci''
Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum 16 tare da jikkatawa su 17 a jihar Kaduna.
Rahotonni sun ambato kwadandan Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadurra ta Najeriya mai lura da jihar Kabir Nadabo na cewa hatsarin ya auku ne a ƙauyen Audu Jhangon da ke kan babban titin Abuja zuwa Kaduna
Ya ce hatsarin ya auku ne da asubahin ranar Lahadi lokacin da wata babar motar daf, ta ƙwace wa direbanta tare da faɗa cikin rami.
“Rahotonnin farko da muka samu sun nuna cewa direban na tsakiyar gudun wuce kima'', in ji Nadabo.
Ya ce tuni jami'an hukuar suka kai ɗauki domin tseratar da mutanen da lamarin ya shafa.
“Hatsarin ya rutsa da mutum 65, inda mutum 27 suka jikkata, yayin da 16 suka mutu''.
Ya ce tuni aka kai waɗanda suka jikkata asibiti domin ba su kulawar gaggawa.
Hatsarin mota dai wata babbar matsala ce a titunan Najeriya, da ke laƙume rayukan 'yan ƙasar masu yawan gaske a kowace shekara.
Matsalar da masana ke alaƙantawa da rashin kyawun titunan ƙasar, da kuma rashin bin ƙa'idojin tuki daga ɓangaren direbobi.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ''yakin da ake yi a Gaza ya yi mummunar illa ga fannin lafiya''.
Yayin da yake jawabi a wajen wani taro a birnin Geneva, Dakta Ghebreyesus ya ce fannin lafiya a Gaza na kan hanyar durƙushewa.
Ya ƙara da cewa matakan da Isra'ila ta ɗauka na tilasta wa Falasɗinawa komawa ƙananan garuruwa na ƙara haifar da yanayin cututtuka masu tarin yawa tare da yaɗuwarsu.
Shugaban na WHO ya ce a wasu wuraren a Gaza mutum 750 ne ke amfani da wurin wanka ɗaya, sannan mutum 150 na amfani da ban ɗaki guda.
''Kuma a yanzu asibitoci 14 ne - daga cikin 36 da ke Gaza - ke iya yin aiki, su ma ba yadda ya kamata ba, biyu a arewaci da kuma 12 a kudanci'', in ji shi.
''Yanayin da ma'aikatan jinya ke ciki babu daɗin ji- waɗanda dama tun 2018 ke cikin mawuyacin hali'', in Dakta Ghebreyesus.
Ya ƙara da cewa WHO, tana da bayanan kai hare-hare 449 kan cibiyoyin lafiya a Zirin Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, da 60 a Isra'ila, tun ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da yaƙin ya soma.
Shugaban Najeriya kuma shugaban ƙungiyar Ecowas, Bola Tinubu ya yi kira ga shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma da su fifita samar da shugabanci nagari ga mutanen yankin, saboda a cewarsa shi ne kawai hanyar inganta da ci gaban tattalin arzikin yankin.
Yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron ƙungiyar da aka gudanar a birnin Abuja na Najeriya, shugaba Tinubu ya ce tsarin shugabanci nagari ne zai magance tarin matsalolin da al'umomin ƙasashen yankin ke fama da su, kamar inganta rayuwa da samar da kyakkyawan yanayin samar da gaba mai ɗorewa.
Shugaban na Najeriya ya ce samar da shugabanci nagari ne zai iya magance matsalolin yunwa da talauci da rashin tsaro da rashin aikin yi da rashin daidaito da sauran matsalolin da suka yi wa yankin katutu.
''Ya kamata mu samu nasarar magance wasu matsalolin juyin mulkin soji a yankinmu''. in ji Tinubu.
Ya ci gaba da cewa lokaci ya yi da za a ƙarfafa tsarin dimokraɗiyya da mutuntu haƙƙoƙin talakawan yankin na zaɓar shugabannin da suke so.
"Yankinmu ya amince da ɗaukar tsaurara matakai ga duk wata ƙasa da ke cikin ƙungiyarmu da ta yi yunƙurin kawar da halastacciyar gwamnatin da talakawa suka zaɓa'', in ji Tinubu.
Yayin da takunkuman da za mu ɗauka ga ƙasa za su haifar da wasu matsalolin, yana da muhimmanci mu fahimci cewa muna koƙari ne wajen kare wa talakawa haƙƙoƙinsu tare da mutunta 'yancinsu.
Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Radda ya shiga tawagar jami'an tsaro don daƙile wani harin da 'yan bindiga suka suka ƙauyen Zakka da ke ƙaramar hukumar Safana a jihar.
Cikin wata sanarwa da satakaren yaɗa labaran gwamnan, Kaula Mohammed, ya fitar, ya ce tawagar jami'an tsaron ta samu nasara kuɓutar da wani mutum mai shekara 33 da 'yan bingidar suka kama a lokacin da suka kai harin.
Sanarwar ta ce, da farko gwamnan ya je Safana ne domin ƙaddamar da wani shirin tallafi da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Abduljalal Runka, ya shirya a lokacin da ak yi wa jami'an tsaro kiran gaggawa kan harin da 'yan bindigar suka kai ƙauyen na Zakka.
Bayan samun rahoton ne kuma, sai gwamna ya gaggauta katse taron da yake halarta, inda nan take ya nufi ƙauyen tare da sauran jami'an tsaro.
“Gwamna Radda tare da wasu mambobin tawagarsa sun i sahun jami'an tsaro da suka haɗar da 'yan sanda da sojojin saman rundunar Hadarin Daji, da na ƙasa, da kuma jami'an tsaron sa-kai da ya ƙaddamar'', in ji sanarwar
An yi arangama da 'yan bindigar kafin su tsre zuwa cikin tsaunuka.
“Bayan fafatawa mai zafi na tsawon miti 30 da 'yan bindigar, jami'an tsaron sun samu nasarar kuɓutar da wani mutum mai shekara 33''
Sanarwar ta kara da cewa 'yan bindigar sun tsere ba tare da kashe wasu daga cikinsu ba.
Bayan daƙile hari ne kuma, Gwamna Radda ya bayar da umarnin gaggauta kai mutumin da aka ƙubutar asibiti bayan da 'yan bindigar suka harbe shi a ƙafa, in ji sanarwar.
Dama dai gwamnan ya sha yin alwashin shiga daji domin yaƙar 'yan bindiga a lokutan yaƙin neman zaɓensa.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce ƙasahen yankin Yammacin Afirka ne suka fara rungumar tsarin mulkin dimokraɗiyya hannu bibbiyu a nahiyar Afirka.
Yayin da yake gabatar da jawabi a taron da ƙungiyar shugabannin ƙasashen yankin Yammacin Afirka, Ecowas, shugaba Tinubu ya ce Ecowas na da martaba a idanun duniya saboda yadda take tallafa wa siyasa da zaman lafiya da tsaron yankin.
''Muna buƙatar ƙara nuna kishi ga ci gaban yankinmu, mu samar da yanayin shugabanci mai kyau, da tsarin zirga-zirga mai tsafta tsakanin ƙasashen yankinmu, domin samun ci gaban al'umominmu'', in Shugaban na Najeriya.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa shugaban Laberiya bisa amincewa da shan kaye da ya yi a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar cikin watan da ya gabata.
Ya ce abin da shugaban na Laberiya ya yi wani abin koyi ne da shugabannin ƙasashe za su koyi da shi, yana mai cewa tsohon shugaban Najeriya Good Luck Jonathan ne ya fara yin irin wannan abin a yaba na amincewa da shan kaye a 2015.
Shugabannin ƙasashen ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, Ecowas sun fara gudanar da babban taron ƙungiyar karo na 64 a Abuja babban birnin Najeriya.
Shugaban Najeriya kuma shugaban ƙungiyar Bola Tinubu ne ke karɓar baƙuncin taron, wanda ya samu halartar shugabani da ministocin ƙasashen yankin.
Akwai kuma jakadiyar Amurka mai kula da ƙasashen Afirka da shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar.
Ana sa ran taron zai mayar da hankali kan matsalolin da yankin yammacin Afirka ke fuskanta kama daga na juyin mulki da kuma tattalin arziki.
Kazalika batun takunkuman da ƙungiyar ta kakaba wa Nijar na daga cikin batutuwan da ake sa ran taron zai mayar da hankali a kai.
Taron ECOWAS ɗin da aka yi na ƙarshe ya mayar da hankali ne kan halin da Nijar ta tsinci kanta bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yulin 2023 wanda ya janyo hambarar da gwamnatin zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum.
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta samu nasara halaka wasu 'yan bingida a jihar Naija ciki har da wani gawurtaccen ɗan bindiga da ya jima yana addabar jama'a, mai suna Yellow Jambros.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fita mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaranta, Air Commodore Edward Gabkwet, ta ce 'yan bindigar sun gamu da ajalisun ne a ranar Laraba 6 ga watan Disamba a gundumar Galadima Kogo, a daidai lokacin da suke yunƙurin tsallaka kogi zuwa yankin Wurukuvhi na ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna mai makwabtaka.
Kafin kisan nasu, an yi ta bin diddigin Yellow Jambros, tare da mabiyansa waɗanda suka taso daga jihar Zamfara a kan babura 13 inda suka nufi Kusasu na ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Naija.
Sanarwar ta ce da suka isa Kusasu, wasu ƙarin babura biyar sun shiga tawagar tasu, inda suka zama babura 18, daga nan kuma suka nufi kogin Jikudna.
''Da isarsu kogin ne 'yan bindigar suka hau kwale-kale tare da baburansu 18 da nufin tsallakawa, suna tsaka da kogin ne kuma aka bayar da umarnin kai musu hari'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Air Commodore Edward Gabkwet ya ce an samu nasarar ƙaddamar da harin yadda aka tsara shi, inda aka kashe Yellow Jambros da sauran yaransa tare da lalata baburan da kuma nutsar da kwale-kwalen.
''Duk da cewa tafiyar 'yan bindiga cikin ayari ba abu ne da aka saba gani ba, musamman da rana tsaka, Yellow Jambros tare da yaransa ba su yi tsammanin kai musu hari ta sama ba, saboda suna tunanin sojoji sun dakatar da kai hare-hare ta sama saboda da abin da ya faru na harin kuskure kan fararen hula a Tudun Biri, don haka suke son yin amfani da wannan damar'', in ji Edward Gabkwet.
Ya ƙara da cewa Yellow Jambros tare da yaransa sun sha ƙaddamar da hare-hare tare da yin garkuwa da mutane da kuma kashe su a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna da kuma wasu garuruwa a jihohin Kaduna da Naija da Katsina da kuma Zamfara.
A watan Oktoban 2020 'yan sandan Zamfara suka kama wani gawurtaccen ɗan bindiga mai suna Mohammed Sani, wanda ya kashe fiye da mutum 50, saboda sun kasa haɗa masa kuɗin fansar da ya buƙata daga gare su.
A lokacin da 'yan sandan ke tuhumarsa ya yi iƙirarin cewa shi yaron Yellow Jambros ne, wanda ke samar masa da jabun tufafin sojoji da na 'yan sanda da bindigogi da sauran makaman da yake buƙata.
Shin kun san abin da ke nufi da asusun ajiyar ƙasashen waje, amfaninsa da kuma irin taimakon da yake yi wa tattalin arzikin ƙasa?
A wannan shiri - wanda Badamasi Abdulkadir Muktar ya gabatar - an kuma amsa tambaya kan gabatar da sabuwar shaida a Kotun Koli.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya ce ya ji takaicin yadda kwamitin tsaro na majalisar ya kasa amincewa da ƙudurin dakatar da wuta a Gaza.
António Guterres ya bayyana kwamitin tsaro na majalisar da ''gajiyayyen kwamiti'' wanda ya kasa samar da hanyoyin magance matsalolin duniya ciki har da yaƙin Ukraine da Mynmar, da kuma na yankin Gabas ta Tsakiya.
Yayin da yake jawabi a birnin Doha na Qatar, Mista Guterres ya ce ''daraja da kimar'' kwamitin na ci gaba da zubewa a idanun duniya, amma ya ce duk da haka ''ba zan gajiya ba''.
A ranar Juma'a ne, Amurka ta ƙi amincewa da goyon bayan ƙudurin dakatar da wuta a Gaza da aka kaɗa ƙuri'a a kansa a kwamitin tsaro na MDD.
Amurkan dai ta kare matakin da cewa ƙudurin na da hatsari kuma babu gaskiya a cikinsa.