Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Motocin agaji sun hau layin shiga Gaza kafin tsagaita yaƙi a safiyar Alhamis

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Abdullahi Bello Diginza, Umaymah Sani Abdulmumin and Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotonni

    Nan za mu gintse kawo rahotonni a wannan shafi a yau Laraba.

    Mu haɗu da ku gobe da safe don samun wasu sababbin rahotonnin.

    Mu kwana lafiya.

  2. Kotun Isra'ila ta kori ƙarar neman soke yarjejeniyar tsagaita yaƙi a Gaza

    Wata babbar kotu a Isra'ila ta kori ƙarar da aka shigar gabanta da ke ƙalubalantar yarjejeniyar da Isra'ila da Hamas suka ƙulla ta tsagaita wuta ta kwana huɗu.

    Yarjejeniyar za ta fara aiki da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar gobe Alhamis agogon Gaza. Ta tanadi cewa Isra'ila za ta saki fursunonin Falasɗinawa 150 da take tsare da su, akasari mata da matasa. Hamas kuma ta saki Isra'ilawa 50 cikin kwana huɗu.

    Kotun ta ce yarjejeniyar ta siyasa da diplomasiyya ce. 'Yan uwan waɗanda Hamas ta kashe ne a harin da ta kai a watan da ya gabata suka shigar da ƙarar.

    Masu ƙarar sun ce sakin fursinonin Falasdinawa zai iya janyo ƙaruwar kai hare-hare nan gaba.

    Wakiliyar BBC ta ce an iya gano 34 daga cikin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su wadanda matasa ne ƴan ƙasa da shekara 18 kuma cikinsu har da yaro dan kasa da shekara ɗaya da haihuwa.

  3. Switzerland za ta haramta ayyukan Hamas da goyon bayanta

    Gwamnatin Switzerland ta sanar da cewa za gabatar da dokar da za ta haramta "ayyukan" ƙungiyar Hamas ko kuma nuna mata kowane irin goyon baya a cikin ƙasar.

    Wata sanarwar gwamnati ta bayyana ƙudirin a matsayin "wanda ya fi dacewa ga yanayin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya tun daga ranar 7 ga watan Oktoba" lokacin da Hamas ta kai hari cikin Isra'ila.

    "Dokar za ta bai wa hukumomin tarayya damar daƙile duk wani abu da ya shafi Hamas ko kuma goyon bayan da take da shi a Switzerland," a cewar sanarwar.

    Ana tsammanin ƙudirin zai samu amincewar jam'iyyar Swiss People's Party mai tsattsauran ra'ayi da ke son a haramta Hamas da kuma goyon bayan "'yancin Isra'ila na kare kan ta".

    Gwamnatin ƙasar ta kuma yi kiran a kiyaye rayukan fararen hula a Gaza, tana mai cewa tsahirtawa don ba da agaji "ya zama dole".

  4. Labarai da dumi-dumi, Red Cross za ta ziyarci mutanen da Hamas ke riƙe da su - Netanyahu

    Yayin taron manema labaran da yake gabatarwa yanzu haka, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce daga cikin abubuwan da yarjejeniyar tsahirta yaƙi ta ƙunsa har da kai wa Isra'ilawan da Hamas ke tsare da su a Gaza ziyara.

    Friaministan ya ce za a ƙyale ƙungiyar agaji ta Red Cross ta kai wa sauran mutanen da Hamas ɗin ke riƙe da su ziyara waɗanda ba su cikin waɗanda za a saki.

    "Ina tsammanin Red Cross za ta yi aikinta, kuma ta ziyarce su gaba don ba su magungunan da suke buƙata," in ji shi.

  5. Tinubu ya yi alhinin mutuwar mutum 17 a hatsarin mota a jihar Neja

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al'ummar jihar Neja sakamakon rasuwar mutum 17 a harsarin mota.

    Hatsarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Magama, inda ya ritsa da mutum 229 da ke cikin wata babbar mota.

    Jami'in wayar da kai na hukumar kiyaye haɗurra, Bisi Kazeem, ya ce an yi nasarar ceto maza 206, da mace ɗaya, da ƙaramin yaro, waɗanda suka ji raunuka daban-daban.

    Shugaba Tinubu ya kwatanta hatsarin da tsautsayi "kuma ya nemi hukumar ba da agaji ta tabbatar an bai wa waɗanda suka ji rauni kulawar da suke buƙata", in ji wata sanarwa daga fadar shugaban.

  6. Ko Super Eagles za ta koma kan ganiya a neman shiga kofin duniya?

  7. An kori jaruma daga fim saboda wallafa sakon goyon bayan Falasdinawa

    An kori wata jarumar fim Melissa Barrera daga fitowar gaba ta wani fim mai dogon zango Scream bayan masu shirya fim din, sun ce sakonnin da take wallafawa don goyon bayan Falasdinawa a shafukan sada zumunta, na kin jinin Yahudawa ne.

    Tauraruwar a kai a kai tana wallafa sakonni game da rikicin Isra'ila da Gaza, ciki har da wani sako da ta sake yadawa wanda ke zargin Isra'ila da aikata "kisan kare dangi da shafe wata al'umma daga doron duniya".

    Kamfanin shirya fina-finai na Spyglass ya ce yana da manufar "rashin lamuntar kin jinin Yahudawa daidai da kwayar zarra".

    A lokaci guda, ita ma Susan Sarandon an watsar da ita daga harkokin shirya fim bayan ta gabatar da jawabi a wani taron nuna goyon bayan Falasdinawa.

    Daga Susan Sarandon, wadda ta bayyana a fim din Thelma & Louise, har zuwa kan jaruma Melissa Barrera 'yar Mexico, babu wadda ta mayar da martani kan lamarin.

    Sai dai, kafin ba da sanarwar fitar da ita, Melissa Barrera ta sake yada wani sako a shafinta na Instagram da ke cewa: "A karshe dai, na gwammace a cire ni saboda wanda na shigo da shi cikin harkokina a kan a shigar da ni saboda wanda na cire."

    Wasu masu bibiyar tauraruwar sun yi wa sakon fashin bakin cewa hakan yana nuni ne da batun korar ta daga fim din.

    Barrera ta jagoranci fina-finan Scream guda biyu a baya kuma ta bayyana a matsayin tauraruwa a wani fim mai suna Carmen da kuma wani baddalallen fim mai suna The Heights.

    Sauran sakonnin da tauraruwa Barrera ta sake yadawa a makonnin baya-bayan nan akwai wani kan yadda aka jirkita batun kisan kare dangin da aka yi wa Yahudawa na Holocaust "don bunkasa masana'antun kera makaman Isra'ila" da kuma wnai da ke cewa Gaza "a yanzu ta koma kamar wani sansanin azabtarwa ne".

  8. Manyan motocin agaji sun hau layin shiga Gaza kafin tsagaita yaƙi

    A watan da ya wuce, Isra'ila ta ƙyale motocin agaji 1,399 sun shiga Zirin Gaza ta Masar.

    Kafin fara yaƙin, adadi na tsakatsaki na motocin da ke shiga duk wata ya kai 10,000, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

    Cikin abubuwan da yarjejeniyar tsahirta yaƙin ta ƙunsa, za a ƙyale adadi mafi yawa na kayan agajin su shiga zirin.

    Hotunan da muka samu daga ɓangaren Masar na kan iyakar Rafah sun nuna yadda ake ta shirye-shiyen shiga Gaza da kayayyakin.

  9. Kociyan Argentina Scaloni zai yi murabus

  10. Najeriya da Jamus sun ƙulla yarjejeniyar samar da iskar gas

    Najeriya za ta ƙara yawan gas ɗin da take sayar wa Jamus bayan ƙasashen biyu sun ƙulla yarjejeniyar da za ta kai dala miliyan 500 kan makamashi mai tsafta.

    Fadar shugaban Najeriya ta ce an saka hannu kan yarjejeniyar ne yayin wani taron kasuwanci a birnin Berlin tsakanin kamfanin Riverside LNG na Najeriya da kuma na Jamus mai suna Johannes Schuetze Energy Import.

    "Shirin zai samar da tan 850,000 na makamashi daga Najeriya zuwa Jamus duk shekara, inda zai ƙaru zuwa tan miliyan 1.2," in ji David Ige, wani da ke cikin yarjejeniyar.

    Najeriya za ta fara jigilar gas ɗin zuwa Jamus karon farko a 2026.

    Su ma Bankin Union na Najeriya da kamfanin DWS Group na Jamus sun ƙulla yarjejeniya don kamfanin ya zuba jari a harkar makamashi mai tsafta a Najeriya.

    Kazalika, Jamus na magana da kamfanin lantarki na ƙasar mai suna Siemens don ya taimaka wa Najeriya wajen haɓaka wutar lantarkinta, a cewar kafar yaɗa labarai ta Deutsche Welle.

  11. Euro 2024: Waɗanda suka samu gurbi da masu buga cike gurbi

  12. An samu yamutsi yayin zanga-zanga kan hukuncin shari'ar gwamnan Kano

    Wani hargitsi ya tashi da yammacin ranar Laraba, lokacin da dandazon magoya bayan jam'iyyar NNPP suke gudanar da zanga-zanga a jihar Kano, dangane da hukuncin kotun daukaka kara da soke nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

    Wakilin BBC a Kano ya ruwaito cewa 'yan sanda sun tare masu zanga-zangar wadanda suka yi yunkurin zuwa gadar Kofar Nassarawa, bayan sun gudanar da wani taron addu'o'i a filin Kofar Dan'agundi.

    Hotuna a kafofin sada zumunta sun nuna yadda aka kona tayoyi a kan titin zuwa Jami'ar Bayero, lamarin da ya kawo tsaiko ga masu ababen hawa.

    Haka zalika, an yi jefe-jefe a lokacin hargitsin, 'yan sanda kuma sun harba hayaki mai sa hawaye.

    Bayanai sun ce an kama wasu daga cikin masu zanga-zangar, sannan an ga karin 'yan sanda a kan titin zuwa gidan gwamna.

    Daga bisani dai, kurar ta lafa.

    Magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da jam'iyyarsa ta NNPP sun yi kiran gudanar da abin da suka ce "taron addu'o'i" ne don nuna adawarsu ga hukuncin kotun daukaka kara wanda tun farko ya bai wa Nasiru Yusuf Gawuna nasara na jam'iyyar APC.

    Kotun wadda ta yi zamanta a ranar Juma'a 17 ga watan Nuwamba, ta yanke hukuncin cewa Abba Kabir Yusuf ba dan jam'iyya ba ne, don haka bai cancanci tsayawa takara ba.

    Sai dai, bayan fitar da kwafin takardar cikakken hukuncin a ranar Laraba, takaddama ta sake barkewa, inda 'yan jam'iyyar NNPP ke da'awar cewa su ma hukuncin ya ba su nasara a kan abokan kararsu.

    • Zargin cin hanci ya yi wa kotun zaɓen Kano dabaibayi
  13. Uganda za ta yi bincike kan baƙuwar cutar da ta kashe mutum 12

    Hukumomin lafiya a Uganda na bincike kan wata baƙuwar cuta da ta yi ajalin mutum 12 cikin makonni biyu a tsakiyar lardin Kyotera.

    Ƙuraje da ke yaɗuwa kan fito a jikin waɗanda cutar ta kama kafin ta yi ajalinsu a cikin ƴan makonni.

    Ma'aikatar lafiya ta Uganda ta tattara sabbin samfuran fata daga daya daga cikin majinyatan da suka mutu a wani babban asibitin yankin a makon jiya.

    Har yanzu ba a raba sakamakon binciken ga jama'a ba.

    Jami’an kiwon lafiya na yankin sun ce wasu majinyata na neman magani a wajen masu maganin gargajiya maimakon zuwa asibiti.

    Sun ce yana da matuƙar wahala a hana su yin hakan tun da ba a san cutar ba

  14. Isra'ila ta kashe mutum bakwai a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan - Ma'aikatar lafiyar Falasɗinu

    Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu ta ce Isra'ila ta kashe mutum bakwai a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ƙasar ta mamaye.

    Ta ce an kashe shida daga cikinsu a sansanin 'yan gudun hijira na Tulkarem sakamakon harin jirgi maras matuƙi na Isra'ila, in ji rahoton kamfanin labarai na Wafa.

    Kamfanin labaran ya ruwaito cewa an kashe wani Bafalsɗinen a unguwar Qalqilia.

  15. NNPP ta shigar da kara gaban Kotun Koli kan shari'ar gwamnan Kano

    Jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta shigar da kara gaban Kotun Kolin kasar inda take kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ya soke nasarar gwamna daya tilo da jam'iyyar ta samu a zaben watan Maris.

    NNPP ta shigar da karar ce inda ta kafa manyan hujjoji guda goma, tana neman kotun koli ta sake nazari kan hukuncin karamar kotun sannan ta warware ɓangarorin da suka bai wa Abba Kabir Yusuf rashin nasara.

    Haka zalika, ta nemi kotun ta tabbatar da bangarorin hukuncin da suka bai wa dan takararta, gwamnan Kano mai ci nasara.

    Daga cikin bangarorin hukuncin kotun daukaka kara da take kalubalanta kamar yadda wata takardar kotu ta nuna, NNPP ta yi ikirarin cewa sashe na 177 karamin sashe na c, bai fitar da ka'ida a kan kasancewar mutum dan jam'iyya ba.

    Sannan ta ce wani mutum daban ba shi da ikon tuhumar dan takarar da ya tsaya takara kuma ya ci zabe a inuwar wata jam'iyya, kasancewarsa dan jam'iyyar.

    • Dalilan APC huɗu na neman kotu ta soke zaɓen Abba Gida-Gida
    • Ba zan yi shiru ba kan mulkin Kano - Kwankwaso
  16. Sojin Isra'ila sun ce sun gano hanyoyin ƙarƙashin ƙasa 400 a Gaza

    Dakarun tsaron Isra'ila sun ce sun gano tare da lalata hanyoyin ƙarƙashin ƙasa 400 na Hamas tun farkon rikicin 7 ga Oktoba.

    Sun ƙara da cewa da yawa daga cikin hanyoyin ƙarƙashin ƙasan sun ratsa ta asibitocin fararen hula da makarantu da gidaje.

    Rundunar ta kuma wallafa hotunan hanyoyin domin tabbatar da iƙirarinta sai dai BBC ba ta iya tantancewa da kanta ba.

    Isra'ila ta sha zargin Hamas da yin amfani da fararen hula a Gaza, a matsayin garkuwa, abin da Hamas ta rika musantawa.

    • Abotar Bayahude da Bafalasɗine ta kawo zaman lafiya Gaza
  17. Dan majalisar Ghana ya nemi afuwar Maguire kan zolayar da ya yi masa a bara

    Wani dan majalisar dokoki na bangaren adawa a Ghana ya nemi afuwar Harry Maguire dan wasan baya na Manchester United, saboda kwatanta kwazonsa da rashin iya gudanarwar gwamnati a fannin tattalin arzikin kasar.

    Ghana dai na fama da matsalar hauhawar farashin da ya zarce kashi 35% da kuma taruwar bashi.

    Da yake neman afuwar, Isaac Adongo ya ce dan kwallon baya na Manchester United, Harry Maguire ya canza, har ma ya zama muhimmin dan wasa ga kungiyarsa.

    Dan majalisar na Ghana a bara ya yi zolaya da Maguire wanda ya ce ya zame wa Manchester alakakai da ke taimaka wa abokan hamayya ta hanyar cin kansu da kansu.

    Bayaninsa ya sanya majalisar dokokin barkewa da dariya, lokacin da ya ce Ghana tana da abin da ya kira Maguire a bangaren tattalin arziki, yayin da yake zargin mataimakin shugaban kasa, Mahamudu Bawumia kan hauhawar farashi da dumbin bashin da ya taru a kan kasar.

    Gwamnatin Ghana dai na fatan cewa kamar dan kwallon Manchester United, tattalin arzikin kasar ma zai sake farfadowa sanadin wani bashin ceto kasar da tattaunawar da Ghana ke yi don sake lissafin bashin da ke kanta.

  18. Shugabanni na fata yarjejeniyar tsahirtawa za ta iya kawo karshen yaki a Gaza

    Kamar yadda muke kawo rahoto, an fahimci cewa matakin dakatar da fadan zai fara aiki daga gobe Alhamis da karfe 10 na safe, agogon Gaza.

    'Yan sa'o'i kalilan da suka wuce, ana ci gaba da kara mayar da martani kan harkokin diflomasiyya. Ga wasu muhimman muryoyi da muka ji.

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi maraba da yarjejeniyar dakatarwar, amma ya kara da cewa: "Wannan bai isa kawo karshen wahalar da fararen hula ke ciki ba" yayin da yake kira a kara kokari don ci gaba da sakin sauran mutanen da ake garkuwa da su sannan a tsagaita wuta a Gaza.

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce wannan al'amari wani "muhimmin mataki ne da ya dace, sai dai akwai bukatar kara kokari."

    Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce kasar na fatan yarjejeniyar za ta iya taimakawa wajen kawo cikakken karshen yakin, kuma ta "fara wani yunkuri na samar da zaman lafiya mai dorewa a kan ginshikin masalahar kafa kasa biyu."

    Can kuma, Sarki Abdullahi na Jordan yana jagorantar wata tattaunawa da Shugaban Masar Abdel Fattah al Sisi a kan yadda za a kawo karshen "aukawar Isra'ila kan Falasdinawa da yaki", wata sanarwar fadar Sakin ta ce.

  19. Labarai da dumi-dumi, Dakatar da yaki a Gaza zai fara aiki daga karfe 10 na safe a gobe

    BBC ta fahimci cewa yarjejeniyar da aka cimma domin dakatar da fada, za ta fara aiki daga karfe 10 na safiyar gobe Alhamis, agogon yankin daidai karfe 9 agogon Najeriya.

    Za a fara hakan ne da sakin mutanen da ake garkuwa da su daga tsakiyar rana zuwa yamma.

  20. Za mu yi ta gwagwarmaya har sai an tabbatar mana da kujerar gwamnanmu - NNPP

    Daya daga cikin jam'iyyun adawa a Najeriya wato NNPP ta nemi majalisar kula da alkalai ta kasa NJC ta yi bincike game da batun zaman gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf cikakken dan jam'iyyar mai rijista.

    Shugabancin jam'iyyar ya ce Abba Kabir ya yi rijista a ranar 27 ga watan Maris 2022 a mazabar Diso-Ciranci da ke karamar hukumar Gwale.

    NNPP ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai da ta kira a yau Laraba cikin Abuja, babban birnin kasar.

    Taron na zuwa ne kwanaki kalilan bayan hukuncin kotun daukaka kara da ya soke nasarar Gwamna Abba Kabir a zaben watan Maris, bisa hujjar cewa bai cika ka'idar tsayawa takara ba, saboda babu sunansa a rijistar NNPP a lokacin.

    NNPP ta ce za ta ci gaba da gwagwarmaya don ganin an tabbatar mata da kujerar gwamnan Kano.

    A cewarta, Abba Kabir Yusuf ya bi duk wani mataki na kasancewa dan jamiyya, kama daga tantancewar da aka yi a watan Mayun 2022, zuwa zaben fidda gwani a watan Yuni, wanda ya kai ga zabarsa a matsayin dan takarar NNPP.