Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Isra'ila a Gaza: An kwashe jarirai bakwaini 31 daga Asibitin Al-Shifa

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. WHO ta kira al-Shifa da 'sansanin mutuwa'

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya bayyana asibiti mafi girma a Gaza na Al-Shifa da cewa ya zama "sansanin mutuwa", bayan ficewar ɗaruruwan mutane daga cikinsa

    Tawagar haɗin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya ƙarƙashin jagrancin WHO ta samu ziyartar asibitin na tsawon sa'a guda bayan sojojin Isra'ila sun mamaye shi tare da tilasta kwashe marasa lafiya.

    Tawagar ta ce ta ga hujjojin da ke nuna kai hare-haren makami da harbe-harben bindiga, tare da gano wani babban kabari a ƙofar shiga asibitin, wanda aka shaida musu cewa gawarwaki 80 aka binne a ciki.

    A kwanakin baya-bayan nan ne sojojin Isra'ila suka kai samame asibitin, a wani ɓangare na abin da suka kira ''kai hari kan mayaƙan Hamas".

    Sai dai ba ta bayyana wata ƙwaƙƙwarar hujjar da za ta tabbatar da iƙirarin nata na cewa mayaƙan ƙungiyar na gudanar da ayyukansu a hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da ke ƙarƙashin asibitin.

  2. Netanyahu ya yi watsi da kiran tsagaita wuta

    Firamistan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya yi watsi da kiran dakatar da wuta tsakaninsa da Hamas.

    Mista Netanyahu ya nanata cewa zai amince da tsagaita wuta na wucin gadi a matsayin musaya idan Hamas ta sako dukkan Isra'ilawan da ta ke yi garkuwa da su.

    Ya ce ''mutane da dama a duniya sun yi kiran kar mu shiga Gaza, amma mun shiga. Sun ce kar mu shiga birnin Gaza, nan ma mun shiga, sun ce kar mu shiga Al-Shifa nan ma mun shiga. Dan haka babu batun tsagaita wutar dindindin sai dai ta wucin gadi''

    Sai dai jaridar Washington Post, ta rawaito Isra'ila da Hamas da Amurka na gab da cimma matsayar sako mata da yaran.

  3. Taiwan ta ce jiragen China takwas sun ƙetara iyakarta

    Hukumomin Taiwan sun ce jiragen China takwas sun ƙetare iyakar da ta zama mallakinta.

    Hakan na faruwa ne kwanaki huɗu bayan tattaunawa kan makomar tsuburin tsakanin shugaba Joe Biden na Amurka da shugaban China Xi Jinping.

    Rahotanni sun ce jiragen saman na yi wa jirgin ruwan yaƙi na China rakiya.

    A ranar Laraba shugabannin biyu sun shafe awa huɗu suna tattaunawa a birnin California.

    Kuma Mr Xi ya shaida wa shugaba Biden cewa batun Taiwan shi ne babban abu mai hatsarin gaske a dangantaka tsakanin China da Amurka.

  4. Ukraine ta ce Rasha ta ci gaba da yin luguden wuta a Kyiv

    Hukumomin birnin Kyiv na Ukraine, sun ce an shiga rana ta biyu da Rasha ke yi musu luguden wuta ta sama da jirage marassa matuka.

    Shugaban sojin Kyiv Serhiy Popko, ya wallafa a shafinsa na Telegram cewa motoci da dama da ba sa ɗauke da makamai sun dunfaro birnin ta hanyoyi daban-daban, lamarin da ya janyo kararrawar ankarar da mahukunta kan dunfarowar abokan gaba ta fara ƙara.

    Mista Popko ya ƙara da cewa sun yi nasarar kakkaɓo jirage marassa matuƙa har 10.

    Tun da fari Rasha ce ta fara rawaito Ukraine ta harbo jirage marassa matuka har 8 a wajen wata gunduma da ke birnin Moscow.

    Magajin birnin Moscow, Sergei Sobyanin, ya ce babu wanda lamarin ya shafa bare asarar rai, ko jikkata.

  5. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi lafiya, tare da fatan kasancewa da a wunin yau domin kawo muku labarai da rahotoniin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Ku leƙa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.