Turkiyya na shirin kafa asibitocin wucin-gadi a Masar don kula da Falasɗinawa
Wani jirgin ruwan Turkiyya ɗauke da kayayyakin kafa asibitocin wucin-gadi, ya isa gaɓar ruwan Masar da ke kusa da mashigar Rafah.
Jirgin ya taho da injinan lantarki, da motocin daukar marasa lafiya, da sauran kayan kula da lafiya zuwa gaɓar ruwan Al Arish da zimmar kafa asibitoci na wucin-gadi takwas, a cewar kamfanin labarai na AFP.
Shi ne jirgin ruwa irinsa na farko da ya isa Masar, tun bayan fara yaƙi a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba - lokacin da Hamas ta kai hari cikin Isra'ila tare da kashe aƙalla mutum 1,200 da kuma yin garkuwa da sama da 200.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce asibitiin Gaza mafi girma na Al-Shifa "ya daina aiki". Sauran cibiyoyin lafiya na ba da irin wannan rahoton sakamakon ƙarancin lantarki, da man fetur, da kuma fargabar hare-hare.
Wani jami'in lafiya na Turkiyya ya faɗa wa AFP cewa Masar ta bai wa ƙasarsu damar kafa asibitocin a yankin Al Arish, wanda ke da nisan kilomita 40 daga mashigar Rafah - wadda ta haɗe Masar da Zirin Gaza.