Douye Diri na PDP ya lashe zaɓen gwamnan jihar Bayelsa

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Mukhtari Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu za mu dawo da wasu sababbi.

    Ahmad Tijjani Bawage da Mukhtar Adamu Bawa ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Ministan tsaron Isra'ila ya ce Hamas ta rasa iko a Gaza

    Ministan tsaron Isra'ila ya ce Hamas ta rasa iko a Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Yoav Gallant na jawabi ne a wani bidiyo da aka watsa a gidajen talabijin ɗin Isra'ila.

    A cewar kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ce: "Ƴan ta'adda na tserewa zuwa kudanci. Fararen hula na wasoso a sansanonin Hamas."

    "Ba su da imani kan gwamnati yanzu," in ji Gallant.

  3. Falasɗinawa 'yan Birtaniya sun nemi ganawar gaggawa da Sunak

    Prime minister Rishi Sunak

    Asalin hoton, Reuters

    Wata kungiyar Falasdinawa 'yan Birtaniya ta aika wasika ga Firaministan Birtaniya Rishi Sunak inda suka nemi yin taron gaggawa da shi.

    Cibiyar neman tabbatar da adalci ga Falasdinawa ta duniya (CJP) ce ta aika wasikar "a madadin al'ummar Falasdinawa mazauna Birtaniya da iyalansu da kuma makusantansu da ke zaune a Gaza”.

    Kungiyar ta ce kiraye-kirayen a dakatar da yaki saboda muradin ayyukan jin kai "bai wadatar ba" kuma da rashin kiran a tsagaita wuta, gwamnati "tana jefa danginmu a cikin hatsari kuma hakan na ba da gudunmawa wajen samun matsalar jin kan dan'adam da ba a taba ganin irinsa ba".

    “Ta kuma yi biris da muryoyinmu a matsayinmu na 'yan Birtaniya wadanda ke da abokai da dangi suna fuskantar hare-hare a Gaza," wasikar ta kara da cewa.

    BBC ta tuntubi ofishin Firaminista don jin ta bakinsu.

    A baya, Rishi Sunak ya ce yana goyon bayan "dakatawar takanas" a rikicin, don ba da damar kai agajin jin kan dan'adam zuwa Gaza, "wanda yake daban da tsagaita wuta".

    Tun da Hamas ta kai hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba, Firaministan Birtaniya ya kai ziyara zuwa Isra'ila kuma ya ce yana goyon bayan 'yancin Isra'ila "gaba daya wajen kare kanta, bisa tanadin dokokin kasashen duniya".

  4. Alonso ya yi kwazo irin wanda Guardiola ya yi a Bayern a 2015

  5. Na zaɓi tafiya Gaza yin faɗa amma ban san cewa ko zan koma da rai ba - Ɗan Isra'ila

    Gaza-Isra'ila

    Asalin hoton, IDF

    Yakir, ɗan ƙasar Isra'ila mai shekaru 33, an kira shi ne tare da dubun-dubatar sojojin wucin gadi, bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, inda aka kashe mutane 1,200 tare da yin garkuwa da wasu 240.

    "Ban faɗa wa 'yan uwana cewa zan shiga cikin Gaza ba, ba na son su damu," in ji shi.

    "Ban san irin aikin da zan je nayi ba, ko in ma zan dawo da rai."

    Yakir ya ce ya ba da kansa a gaba don gudanar da ayyukan kuma ya shaida min cewa yana fafutukar rayuwa ne a duniyar da babu Hamas a cikinta - wadda Isra'ila da Birtaniya da sauran ƙasashe ke ɗauka a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda.

    Yana magana ne sa’o’i kaɗan kafin a fara aikin, kuma ya ce ya samu izini daga manyansa na yin magana da BBC.

  6. An samu kifewar kwale-kwale a Taraba

    Kifewar kwale-kwale

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana can ana ci gaba da neman mutanen da haɗarin jirgin ruwa ya rutsa da su a ƙaramar hukumar Ibbi a jihar Taraba.

    Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeirya (NEMA) ta ce an gano wasu gawawwaki tare da ci gaba da neman waɗanda ake zargin haɗarin jirgin ya rutsa da su.

    Darektan kula da ayyukan ceto na NEMA, Dr Bashir Garga, ya ce mutanen da haɗarin jirgin ruwan ya rutsa da su sun taso ne daga Ibbi zuwa Ɗan Anacha a cikin daren jiya.

    Ya ce bayanai da suka tattaro, sun gano cewa haɗarin ya afku ne sakamakon wani abu mai ƙarfi da jirgin ya daka a tsakiyar kogin yana tsaka da tafiya.

    Wannan dai na zuwa ne makonni da aka sami makamancin irin wannan haɗarin na jirgin ruwa a yankin ƙaramar hukumar Karim Lamiɗo a jihar ta Taraba da ya yi sanadiyar mutuwar 17 tare da ceto sama da mutum 20, inda har yanzu ba a kai ga gano 63 ba.

    Hakan ne ma ya sa gwamnatin jihar haramta dukkan tafiye-tafiyen jiragen ruwa da daddare a faɗin jihar.

  7. Mun ɗauki matakan tsaro gabanin hukuncin shari'ar gwamnan Kano - 'Yan sanda

    Ƴan sandan Kano

    Asalin hoton, Kiyawa/Facebook

    Rundunar 'yan sandan Kano ta ce ta dauki dukkan matakan da suka zama dole a muhimman wurare don tabbatar da tsaron rayuka da na dukiyar al'umma, gabanin hukuncin da kotun daukaka kara za ta yanke a kan zaben gwamnan jihar.

    Matakin mai yiwuwa na nuna cewa, ranar sanar da hukuncin wannan shari'a ta gabato, ko da yake har yanzu, kotun ba ta fitar da bayani ga jama'a a kan ranar yin hakan ba.

    Tun ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba ne, kotun daukaka kara da ke zama a Abuja, ta kammala sauraron bahasi daga duk bangarorin da ke cikin shari'ar da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya daukaka, bayan kotun sauraron korafin zaben gwamnan Kano tun da farko ta soke nasarar da ya samu.

    Abba Kabir dai yana kalubalantar hukuncin karamar kotun ne wanda ya bai wa Nasir Yusuf Gawuna nasara.

    Sanarwar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ranar Litinin, na cewa jami'ansu da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro da ke aiki a Kano sun tura isassun ma'aikata da kayan aiki zuwa wasu muhimman wuraren da suka tantance a jihar.

    Rundunar ta kuma yi kira ga al'ummar jihar Kano, su guji shigar da kansu cikin duk wani abu da zai kai ga karya doka.

    Ana kallon wannan shari'a ta Abba Kabir Yusuf na NNPP da jam'iyyar APC mai dan takara, Nasir Yusuf Gawuna a matsayin daya daga cikin shari'o'i mafi muhimmanci da jan hankali bayan zabukan 2023, bisa la'akari da muhimmancin jihar a siyasance, wadda ta kubuce daga hannun jam'iyya mai mulki, ta fada hannun jam'iyyar adawa ta NNPP.

    • Kotun ɗaukaka ƙara ta kammala sauraron shari'ar zaɓen gwamnan Kano
    • Zargin cin hanci ya yi wa kotun zaɓen Kano dabaibayi
  8. Yadda ƴan bindiga suka tilastawa mazauna garuruwan Zamfara ƙaura daga gidajensu

    Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa mutane da dama na ƙaura daga garuruwansu zuwa wasu wurare na daban saboda fargabar kai musu hari.

    ‘Yan bindiga dai na ci gaba da afkawa garuruwan Jangebe da Gwaram da ke karamar hukumar Mulki ta Talatar Mafara da ke jihar, inda har suka kashe na’ibin limanin Jangebe tare da sace mutane da dama.

    Ku latsa ƙasa domin sauraron rahoton Zubairu Ahmad Kasarawa.

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton
  9. Maguire ya ce rashin barin United ya sa yana komawa kan ganiya

  10. Babu gudu ba ja da baya kan shiga yajin aiki a ranar Talata - NLC

    NLC

    Asalin hoton, Getty Images

    Gamayyar ƙungiyar ƙwadago a Najeriya NLC ta ce babu gudu ba ja da baya kan yajin aiki da za ta fara daga gobe Talata, 14 ga watan Nuwamban, 2023.

    Wata sanarwa da NLC da takwararta ta TUC suka fitar, ta ce an bai wa dukkan rassanta da kuma mambobi ke faɗin jihohi umarnin shiga yajin aikin.

    Ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da yin yajin aiki har sai gwamnatoci a dukkan matakai sun yi abin da ya kamata.

  11. Burin 'yan Kogi ga zaɓabɓen Gwamna Usman-Ododo

  12. Faɗan matsafa ya janyo mutuwar mutum uku a Ogun

    Ogun

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar mutum uku a wani faɗa tsakanin ƙungiyoyin matsafa a karamar hukumar Sagamu na jihar.

    Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Omolola Odutola, ta tabbatar da cewa an kama wasu mutum uku da ake zargi da hannu a lamarin.

    Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ƙungiyoyin matsafan sun gwabza kazamin faɗa a daren Juma’a, wanda ya kai ga harbin mutane biyu a unguwar Latawa da ke Sagamu.

    Mazauna garin sun ce "sun ji karar harbe-harbe da sanyin safiyar Asabar."

    Idan dai ba a manta ba a kalla mutane 20 ne aka kashe a watan Satumba lokacin da ‘yan wasu ƙungiyoyin matsafa na Eiye da Aiye suka yi arangama, ciki har da wasu ‘yan makaranta uku.

    • 'Yan sanda sun fara dirar mikiya kan masu yaɗa jita-jitar 'matsafa masu shan jini'
    • Matsafa sun yanke sassan jikin wasu yara a Tanzania
  13. Tinubu ya yaba wa INEC kan yadda ta gudanar da zaɓukan baya-bayan nan

    Tinubu

    Asalin hoton, Bola Tinubu/FACEBOOK

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, da gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa, da kuma Usman Ododo na Kogi murnar nasarar da suka yi a zaɓen gwamna na jihohin da aka yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

    Shugaba Tinubu ya yaba wa masu zaɓe a Imo, da Kogi, da kuma Bayelsa kan yadda suka fito suka yi zaɓe, inda ya ce hakan ya tabbatar da ɗorewar dimokuraɗiyya da kuma karfin al’umma wajen tsara yanayin siyasar ƙasar.

    Tinubu ya ce sakamakon zaɓen ya nuna muradin al’umma, yana mai jaddada cewa dimokuraɗiyya na ƙara bunƙasa.

    Shugaban ya kuma yaba wa hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) bisa namijin ƙoƙarin da ta yi wajen samar da daidaito ga dukkan ‘yan takara da jami’an tsaro da suka tabbatar da doka da oda a lokacin zaɓen.

    Ya buƙaci waɗanda suka samu nasarar da su fifita buƙatun jama’a a kan komai.

  14. An bai wa 'yan Kenya hutu domin su shuka bishiya miliyan 100

    Kenya transplant

    Asalin hoton, KEN MUNGAI/BBC

    An bai wa ƴan Kenya hutu na musamman domin shuka bishiya miliyan 100 a wani ɓangare na zimmar gwamnatin ƙasar na ganin an shuka bishiya biliyan 15 a cikin shekara goma.

    Hutun zai bai wa 'dukkan wani ɗan Kenya damar shuka bishiya", a cewar ministar muhalli Soipan Tuya.

    Shugaba William Ruto ya jagoranci shirin shuka bishiyan a garin Makueni da ke gabashin ƙasar.

    Ya buƙaci kowane ɗan Kenya ya shuka akalla bishiya biyu, domin kai wa miliyan 100 da ake hankoro.

    Gwamnatin ƙasar ta ce hakan zai taimaka wajen yaƙi da sauyin yanayi.

    Ta ce itatuwa na taimakawa wajen dakile ɗumamar yanayi ta hanyar fitar da gurɓataccen hayaki na carbon.

    Gwamnatin ta ce za ta samar da bishiyoyi miliyan 150 a makarantu.

    An aike da ministoci zuwa sauran larduna domin jagorantar shirin tare da gwamnonin larduna da kuma was jami'an gwamnati.

    Sai dai, da wuya mutane da yawa, musamman ma a birane su shiga shirin na shuka bishiya, inda za su yi amfani da hutun domin yin wasu ayyukansu.

    • Gwamnatin Jihar Sokoto za ta shuka bishiya miliyan biyu
    • Za a shuka bishiyoyi biliyan shida a daminar bana a Habasha
  15. 'Duk asibitoci da ke arewacin Gaza sun daina aiki'

    Mataimakin ministan lafiya a Zirin Gaza da ke karkashin ikon Hamas, Youssef Abu Rish, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa dukkanin asibitocin da ke arewacin Gaza sun daina aiki.

    Ana ci gaba da gwabza faɗa a ‘yan kwanakin nan a kusa da wasu muhimman asibitoci.

    An kwashe wasu da yawa - yayin da ake ƙoƙarin kwashe wasu a lokaci kuma da ake fuskantar ƙarancin man fetur, ruwa, abinci da magunguna.

  16. Sojojin Isra'ila 44 ne suka mutu tun bayan fara mamayen kasar a Gaza - IDF

    Rundunar sojojin Isra'ila ta fada a ranar Litinin cewa karin sojojinta guda biyu suka mutu a yakin da suke gwabzawa a arewacin Gaza.

    A cewar, kafofin yada labaran Isra'ila, adadin sojojin kasar da aka kashe tun bayan fara mamayen Isra'ila na kasa sun kai 44.

    Sojojin Isra'ila sun ce suna ci gaba da kai samame a wajen sansanin 'yan gudun hijira na Al-Shati da ke yamma da Birnin Gaza.

    Israeli soldiers

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, .
  17. Bidiyon Falasdinawa na gasa burodi a cikin baraguzai

    Bayanan bidiyo, Gasa gurasa a cikin baraguzai a kudancin Gaza

    Mutane a Khan Younis, na kudancin Gaza, na amfani da wadansu dabaru don gasa gurasar da za a ci a tsakiyar gine-ginen da aka rugurguza.

  18. Ingila ta gayyaci matashin Man City Lewis a karon farko

  19. Magoya bayan PDP sun yi zanga-zanga a Abuja kan soke zaben 'yan majalisar wakilai na Filato

    Rahotanni sun ce masu zanga-zanga fiye da 1000 ne suka nufi Kotun Koli da ke Abuja a ranar Litinin, don shigar da korafi a kan rashin gamsuwarsu da hukuncin Kotun Daukaka Kara, da ta soke nasarar 'yan majalisar wakilai hudu na jam'iyyar adawa ta PDP daga jihar Filato.

    Masu zanga-zangar karkashin jagoranci kungiyar Coalition for Justice in Africa, CJA dauke da rubuce-rubuce a kyallaye da alluna, sun gabatar da wasikar nuna baci rai ga Alkalin Alkalan Najeriya, Mai shari'a Olukayode Ariwoola.

    A cewar masu zanga-zangar kotun daukaka karar, da hukuncinta, ta ruguza kudurin masu zabe na jihar Filato, lokacin da ta ayyana 'yan takarar da suka fadi zaben 'yan majalisar wakilai na ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin wadanda suka yi nasara.

    A baya-bayan dai, magoya bayan jam'iyyar PDP na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a jihar Filato a kan hukuncin kotun daukaka kara da ya rusa zaben 'yan majalisar wakilan PDP guda hudu.

    Rahotanni sun ce kotun ta kafa hujjar rusa zabukan ne a kan takaddamar da PDP ta yi fama da ita, ta kafin zaben.

  20. An nada Fabregas kociyan Como ta Italiya na rikon kwarya