Barka da safiya
Maraba da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.
Za mu kawo muku yadda al'ummar jihohin Kogi (arewa ta tsakiya), da Bayelsa (kudu maso kudu), da Imo (kudu maso gabas) ke kaɗa ƙuri'u domin zaɓen sababbin gwamnoni a jihohin.
Wannan ne zaɓen gwamna na farko a Najeriya bayan babban zaɓe na 2023 da aka yi a watan Fabrairu da Maris.
Ku biyo ni Umar Mikail don sanin yadda zaɓen zai gudana.