Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Isra'ila ta ce yaƙin Gaza ya shiga sabon mataki bayan datse layukan sadarwa

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Dangin mutanen da Hamas ke garkuwa da su na neman ganawa da gwamnatin yaƙi ta Isra'ila

    'Yan uwan Isra'ilawan da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su a Gaza sun ce sun shafe dare cikin "babbar zaƙuwa" sakamakon hare-haren da rundunar sojin Isra'ila ta tsananta a kan Zirin na Gaza.

    Cikin wata sanarwa a safiyar yau, 'yan uwan mutanen sun nemi ministan tsaron Isra'ila da mambobin majalisar yaƙi ta ƙasar su gana da su cikin gaggawa.

    "Daraen da ya gabata ya zama mafi muni a wajenmu. Ba mu iya barci ba tsawon dare saboda munanan hare-hare a kan Gaza, abin da ya sa muke fargaba game da halin da mutanen da ake riƙe da su ke ciki, waɗanda harin zai iya shafa," a cewar sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa kai hari ta ƙasa zai saka rayuwar tsararrun cikin haɗari.

  2. Mun kai wa tungar Hamas 150 hari - Sojin Isra'ila

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai wa tungar Hamas 150 hari da ke ƙarƙashin ƙasa yayin luguden wutar da ta yi da tankoki ta ƙasa.

    ta kuma tabbatar da gwabza yaƙi da mayaƙan Hamas.

    Wakilin BBC a Gaza ya ce ya ga ruwan wuta mai tsanani a arewacin Gaza irin wanda ba a taɓa gani ba.

    Kazalika, rundunar ta ce hari ta sama ya kashe ya wani kwamandan Hamas mai suna Issam Abu Rukbeh, wanda ake zargi da tsara harin da mayaƙa masu sauka ta lema suka kai cikin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

  3. Sojojin Isra'ila na cikin Gaza har yanzu

      • Marubuci, Jeremy Bowen
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International Editor

    Abin da ke faruwa a safiyar nan shi ne dakarun Isra'ila sun mayar da hankali kan arewacin Zirin Gaza, a unguwar Beit Hanoun, tare da dannawa zuwa kudanci.

    Rundunar ta isra'ila ba ta ƙara komai ba kan abin da ta faɗa a daren jiya - suna ƙara tsananta hare-haren da suke kaiwa.

    Mun gani a bidiyon da ke fitowa daga Gaza a safiyar nan, da kuma abin da ido ka iya gani daga kan iyakar Gaza, hujjojin da ke nuna ruwan wuta mai tsanani.

    Katse layukan sadarwa na nufin abu ne mawuyaci a iya sanin takamaiman abin da ke faruwa - misali, da safiyar nan na yi magana da Malajisar Ɗinkin Duniya (MDD) wadda ta samu ta yi magana da ofishinta da ke kudancin Gaza ta wayar da ke amfani da tauraron ɗan'adam.

    Amma yayin da layukan sadarwa ke katse, ba za su iya tuntuɓar sauran ofisoshinsu ba waɗanda ke kula da ayyukan agaji - waɗanda yanzu suka dakatar gaba ɗaya - don su ji halin da suke ciki.

  4. Ɓarnar da hare-haren Isra'ila suka yi cikin dare

    Waɗannan hotunan na nuna irin ɓarnar da luguden wutar Isra'ila ya yi a Birnin Gaza a tsakar daren da ya gabata.

    A jiya Juma'a rundunar sojin ta ce za ta tsananta hare-haren, inda a yau ta tabbatar cewa ta kai hari ta ƙasa kuma har yanzu dakarunta na cikin garin a arewacin Gaza.

  5. Ƙasashen duniya sun amince da ƙudirin tsagaita wuta a Gaza

    Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya amince – da gagarumin rinjaye – wani ƙudiri da ke neman tsagaita wuta nan take bisa muradan ayyukan jin-ƙai a Zirin Gaza.

    Ƙudirin – wanda kasar Jordan ta gabatar a madadin rukunin kasashen Larabawa a yammacin jiya Juma'a – ya kuma yi Alla-wadai da dukkan wasu ayyukan tarzoma a kan fararen hula na Falasdinawa da Isra'ila, ciki har da dukkan "hare-haren ta'addanci da kuma na ba-ji-ba-gani".

    Ƙudirin ya yi kira a bai wa fararen hula kariya sannan a shigar da kayan agaji Gaza ba tare da iyaka ba.

    Ƙasashe 120 ne suka kaɗa ƙuri'ar amincewa, 14 suka ƙi nuna goyon baya, yayin da 45 suka ƙaurace wa jefa ƙuri'ar.

    Ba lallai ne a yi aiki da ƙudirorin Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ba, amma suna ɗauke da alhakin sanin ya kamata ga ɗaukacin mambobin MDD.

  6. Labarai da dumi-dumi, Hare-haren Isra'ila a arewacin Gaza sun yi munin da ba mu taɓa gani ba

      • Marubuci, Rushdi Abualouf
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporting from Khan Younis, Gaza

    Hare-haren da Isra'ila ta kai kan Birnin Gaza da tsakar dare sun kai wani mataki da ba mu taɓa gani ba, in ji wakilin BBC Rushdi Abualouf.

    Ana iya ganin harasan wuta na tashi zuwa sararin samaniya - da alama suna amfani da bama-bamai ne daban-daban.

    A wani asibiti da ke nan, direbobi sun faɗa min cewa ba sun kasa yin magana da kowa, saboda haka sai suka yi ta kai kan su wurin da ake kai hare-haren.

    Akwai kiɗimewa a ko'ina, hatta a nan Khan Younis, inda ba a kawo harin sosai, yayin da mutane ke ƙoƙarin tuntuɓar 'yan uwansu a sauran yankuna don jin lafiyarsu, amma kuma an katse layukan sadarwar.

    Yanayi ya hautisne gaba ɗaya.

  7. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da hantsin Asabar tare da fatan kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa lafiya.

    Umar Mikail ne zai kawo muku rahotoni daga sassan duniya, musamman game da halin da ake ciki a hare-haren da Isra'la ke kai wa Zirin Gaza da kuma martanin mayaƙan Hamas a kan ƙasar.

    Ku biy mu.