Isra'ila ta ce yaƙin Gaza ya shiga sabon mataki bayan datse layukan sadarwa
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa musamman kan yaƙin Gaza da Isra'ila.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowo domin kawo muku wasu sabbin labaran.
Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Hamas na son a saki fursunoninta da ke Isra'ila kafin ta saki mutanen da ta yi garkuwa da su
A jawabinsa na farko tun bayan fara yaƙin ranar 7 ga watan Oktoba, shugaban kungiyar Hamas a Zirin Gaza, Yahya Sinwar, ya buƙaci a saki fursunonin ƙungiyar Hamas da ke tsare a gidajen kurkukun Isra'ila kafin su saki duka mutanen Isra'ila da ƙungiyar ke garkuwa da su.
Cikin wata sanarwa ta aka wallafa a shafin intanet na ƙungiyar, Sinwar, ya ce "a shriye muke wajen gaggauta yin musanyar fursunoninmu da ke tsare a gidajen yarin maƙiyanmu da mutanensu da ke hannunmu.''
Labarai da dumi-dumi, Kada ka zarge mu da aikata laifukan yaƙi - Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce a yanu sojoji da manyan kwamandojin na "Zirin Gaza, kuma an baza su ko'ina a yankin".
Tun da farko shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan, ya zargi Isra'ila da aikata laifukan yaƙi.
Firaministan na Isra'ila bai kama sunan Erdogan ba, amma ya ce "Kada ka zargemu da aikata alifukan yaƙi, idan kana tunanin za ka zargi sojojinmu da aikata laifukan yaƙi wannan munafurci ne, Mu ne ke da sojoji mafiya tsafta a duniya."
Ya ce rundunar sojin ƙasar na ɗaukar matakan da suka dace wajen kare fararen hula, tare da zargin Hamas da aikata laifukan ci zarafi ta hanyar "amfani da mutane a matsayin garkuwa".
Ma'aikatar lafiya a Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas, ta ce fiye da mutum 7,600 aka kashe a Gaza tun bayan da Isra'ila ta fara kare hare-haren bom a yankin.
A ranar Juma'a Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce kashi 40 na wadanda ka kashe ƙananan yara ne.
Hamas ta kashe fiye da mutum 1,400 a hare-haren da ta kai Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, mafiya yawansu fararen hula, ciki har da mata da ƙananan yara.
Netanyahu ya ce samame ta kasa ne mataki na biyu na yaƙi
Firaminista Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce samamen soji ta ƙasa a Gaza shi ne mataki na biyu a yaƙin da ƙasarsa ke yi da kungiyar Hamas.
Mista Netanyahu ya ce ƙarin dakarun ƙasa sun tafi wurin da ya kira "cibiyar ɓata-gari", yana nufin Gaza, domin su "wargaza' Hamas tare da maido da mutane da ta yi garkuwa da su.
Erdogan ya ce zai ayyana Isra'ila da mai 'aikata laifukan yaƙi'
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya kira hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza da ''kisan kiyashi''.
Yayin da yake jawabi cincirindon mutane a birnin santambul, Mista Erdogan ya ce ƙasashen yamma ƙawayen Isra'ila su ne ke ingizata wajen aikata abin da ya kira "laifukan yaƙi".
"Isra'ila, za mu ayyana ki a matsayin mai aikata laifukan yaƙi a duniya. Muna shirin yin haka, kuma za mu gabatar da Isra'ila ga duniya a matsayin mai aikata laifukan yaƙi", in ji Erdogan.
Shugaban na Turkiya ya ci gaba da kare matsayinsa na ƙin amincewa da ayyana Hamas a matsayin "ƙungiyar ta'addanci".
Matsayin da ƙasashen Amurka da Birntaniya da wasu wuraren suka ɗauka kan ƙungiyar.
Erdogan na jawabin ne a gaban taron ɗimbin jama'a da ya ce sun kai mutum miliyan 1.5
Waɗanda suka halarci taron sun riƙe tutar Falasdinawa da ta ƙasar Turkiya.
Taron - wanda aka kira babban tattakin goyon bayan Falasɗinawa - an gudanar da shi ne a filin jirgin sama na Ataturk, inda Erdogan ke gudanar da gangaminsa a baya-bayan nan.
A ranar Asabar, ya sake nanata sukarsa ga ƙasashen Yamma, kan ƙin kiran tsagaita wuta a Gaza.
Shugaban na Turkiyya ya kuma kira ƙasashen musulmai na duniya da su haɗa kai.
Netanyahu ya gana da iyalan waɗanda ake garkuwa da su
Asalin hoton, Government Press Office of Israel
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da mai ɗakinsa Sara sun gana da wakilan iyalan mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.
Netanyahu ya shaida wa mutanen cewa "Muna yin duk abinda ya kamata domin dawo da su gida,''. Ya ƙara da cewa "wannan na ɗaya daga cikin maƙasudin wannan yaƙi" .
"Ba za mu dakata da wannan yunƙuri ba, zai ci gaba koƙari, har sai haƙarrmu ta cimma ruwa", in ji Netanyahu.
Nan gaba kaɗan ne a yau Netanhayu zai yi jawabi a taron manema labarai tare da ministan tsaron ƙasar Yoav Gallant da Minista Benny Gantz.
Isra'ila ta gargaɗi mazauna arewacin Gaza cewa wurin ya zama "sansanin yaƙi" don haka su koma kudanci
Mai magana da yawun rundunar sojin isra'ila Daniel Hagari, ya aike da "roƙon gaggawa" ga al'ummar arewacin Gaza da birnin Gaza su tafi kudanci.
Ya ƙara da cewa "damar da aka ba su don yin haka, tana ƙurewa".
Mista hagari, ya wallafa gargaɗin ne a shafin X wanda mafiya yawan mazauna Gaza ba sa iya buɗewa sakamakon katsewar intanet
To sai dai sojojin na Isra'ila sun yi ta ajiye takardun da ke ɗauke da makamancin wannan gargaɗi a Gaza.
Takardun - waɗanda aka rubuta da harshen Larabci - na gargadin mutane cewa arewacin Gaza ya zama "sansanin yaƙi" don haka ba shi da taro, don haka mutane su fice zuwa kudancin yankin.
Rokokin da aka harba daga Gaza sun faɗa kudancin Isra'ila
A tsawon ranar Asabar , an yi ta harba rokoki masu yawa daga Zirin Gaza zuwa cikin Isra'ila.
Kafofin yaɗa laraban ƙasar sun ce wasu daga ciki sun faɗa ƙasar, daga ciki har da waɗanda suka faɗa birnin Ashkelon da ke kudancin ƙasar.
Inda wani roka da aka harba ya faɗa da asubahin ranar Asabar, to sai dai babu rahoton jikkata.
A ranar Asabar da rana ne aka girke na'urorin jiniya da ke ankararwa idan an harba rokokin a birnin Tel Aviv da garuruwan da ke kewaye.
Shafin intanet na kafar yaɗa labaran Ynet ta Isra'ila ya ce wani makamin roka da aka harba ya faɗa warin ajiye ƙananan motoci a kiryat Ono da ke wajen birnin tel Aviv, lamarin da ya sa motoci da dama suka tarwatse.
Ynet ya kuma ruwaito cewa wani mutum mai kimanin shekara 50 a Holon ya gigice sanadiyyar hayaƙi, yayin da wasu mutum biyu suka jikkata a birnin Tel Aviv.
Barcelona ta shiga jerin waɗanda Bellingham ya zura wa kwallaye
Isra'ila ta umarci jami'an diflomasiyyarta da ke Turkiya su koma gida
Ministan harkokin wajen Isra'ila, Eli Cohen, ya umarci jami'an diflomasiyyar ƙasarsa da ke Turkiyya su koma gida.
Cikin wani saƙon X da ya wallafa, Mista Cohen ya ce an ɗauki matakin ne bayan abin da ya kira ''kakkausar sanarwa" daga Turkiyya.
A yau ne shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kira hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza da "kisan kiyashi".
Kotu ta tabbatar da nasarar Fintiri a zaɓen gwamnan Adamawa
Asalin hoton, Facebook/Fintiri
Kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa ta tabbatar da nasarar Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri na jam'iyyar PDP a matsayin halastaccen gwamnan jihar.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da APC da 'yar takararta Aishatu Ahmed Binani suka shigar gabanta suna ƙalubalantar nasarar Fintiri.
Alƙalan kotun sun ce kotu ta yi watsi da ƙarar ne saboda lauyoyin masu shigar da ƙara sun kasa gamsar da kotun da hujjoji.
Tun da farko hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar cikin watan MAris a matsayin wanda bai kammala ba, inda aka ƙarasa zaɓen cikin watan Afrilu.
Inda INEC ɗin ta ayyana Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Ɓarnar da harin Isra'ila ya yi a sansanin Al-Shati da ke Gaza
Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Sansanin 'yan gudun hijira na Al-Shati da ke arewacin Gaza na cikin wuraren da hare-haren Isr'aila suka fi ɓarnatawa.
Wannan bidiyon da muka samu daga cikin sansanin ya nuna hayaƙi na tashi daga wasu daga cikin gine-ginen yayin da mutane ke ƙoƙarin share tituna tare da taimakon babbar mota.
Mutum kusan 90,000 ne ke zaune a sansanin.
Dubban 'yan Turkiyya sun amsa kiran Shugaba Erdogan na goyon bayan Falasɗinawa
Dubun dubatar 'yan Turkiyya ne suka fito tattakin nuna goyon bayansu ga Falasɗinawa a birnin Istanbul a yau Asabar.
Mutanen sun amsa kiran Shugaba Recep Tayyip Erdogan, wanda ya nemi su taru a Filin Jirgin Sama na Ataturk.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
'Wasu da ke kewaye da Tinubu ne ke hana a cire wa Nijar takunkumai'
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin:
Shirin Gane Mini Hanya na wannan makon ya yi tattaunawa ta musamman da Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, wanda sojoji suka naɗa.
Firaministan ya taɓo batutua da dama, ciki har da batun cire musu takunkuman da Ecowas ta ƙaƙaba wa ƙasar bayan juyin mulkin da sojojin suka yi a watan Yuni.
Ya yi zargin cewa akwai "wasu ƙwararru" na kusa da Shugaban Najeriya Bola Tinubu "da ke mayar da hannun agogo baya" game da takunkuman a matsayinta na jagorar Ecowas.
Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe sun kai 7,703, in ji hukumomi a Gaza
Ma'aikatar lafiya a Zirin Gaza ta ce Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a hare-haren da take kaiwa sun kai 7,703 zuwa yanzu.
Rahoton na baya-bayan nan ya ce cikin wannan adadi akwai ƙananan yara 3,500.
Sai dai har yanzu ba mu san adadin mutanen da aka kashe ba a hare-haren tsakar dare a kan Zirin na Gaza.
Me ke kawo ciwon kai na Migraine da mata suka fi yi?
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin:
Cikin shirin Lafiya Zinariya da ke tattaunawa kan lafiyar mata da yara, a wannan makon ya taɓo batun ciwon kai na Migraine wanda alƙaluma suka nuna cewa mata ne suka fi yin sa.
Shirin da Habiba Adamu ta shirya kuma ta gabatar ya bayyana abubuwan da ke haddasa shi da kuma yadda ake maganin sa.
A yi sauraro lafiya.
Mun kasa tuntuɓar abokan aikinmu saboda katse layukan sadarwa a Gaza - Ƙungiyoyin agaji
Asalin hoton, EPA
Ƙungiyoyin agaji na duniya sun koka game da kasa tuntuɓar abokan aikinsu da ke Zirin Gaza bayan an katse kusan dukkan layukan sadarwa.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya ce sun kasa magana da ma'aikatansu da asibitoci, waɗanda suke da fargaba a kansu.
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ƙara da cewa rashin layukan sadarwar sun sa motocin ɗaukar marasa lafiya ba su iya kaiwa ga mutanen da suka ji rauni.
Ya roƙi masu ruwa da tsaki su matsa don a tsagaita wuta.
Shugaban Turkiyya Erdogan ya nemi 'yan ƙasarsa su fito macin goyon bayan Falasɗinawa
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi tir da hare-haren da Isra'ila ta kai cikin dare a Gaza waɗanda ya ce sun "ƙara ta'azzara halin da ake ciki".
Cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalin X, wanda aka sani a baya da Twitter, shugaban ya nemi 'yan ƙasarsa su fito zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa.
"A yau, ina gayyatar 'yan uwana zuwa babban maci don Falasɗinawa a Filin Jirgin Sama na Ataturk, Istanbul, inda za mu nuna goyon bayan Falasɗinawa da babbar murya a hare-haren da Isra'ila ke kai musu," in ji shi.
Ya ƙara da cewa "dole ne Isra'ila ta koma cikin hankalinta kuma ta dakatar da waɗannan hare-hare".
Da ma tuni dubban 'yan Tukriyya suka dinga nuna goyon bayansu ga Falasɗinawan duk ranar Juma'a tun daga fara yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba.
Zuwa yanzu, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 7,000 a Zirin Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa.
Isra'ilar na cewa tana kai harin ramuwar gayya ne bayan mayaƙan Hamas sun tsallaka iyaka tare da kashe mutum 1,400 a ƙasar.
Luguden wutar Isra'ila cikin dare ya lalata dubban gine-gine, in ji hukumar Hamas
Asalin hoton, EPA
Hare-haren Isra'ila na tsakar dare sun lalata gidaje masu yawa a Gaza, kamar yadda rundunar tsaron farar hula da agaji ta Hamas ta faɗa wa kamfanin labarai na AFP.
"An kuma lalata dubban gidaje," a cewar wani mai magana da yawun hukumar yana mai cewa luguden wutar ya "sauya fasalin" arewacin Gaza.
Zuwa yanzu ba mu samu wasu alƙaluma daga Gaza ba.
Sai dai hotunan da aka ɗauka da safiyar yau sun nuna yadda aka yi raga-raga da gidaje a arewacin, inda Isra'ila ta fi kai wa hari tun bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.
Jiragen yaƙin Isra'ila 100 ne suka yi wa Gaza ruwan wuta cikin dare
Asalin hoton, Getty Images
Jiragen yaƙin Isra'ila "kusan 100" ne suka yi wa Zirin Gaza ruwan wuta a tsakar daren da ya gabata, a cewar Hafsan Sojin Sama na Isra'ila Birgediya Gilad Keinan.
Cikin wani saƙo a dandalin X, dakarun Isra'ila sun ambato Keinan na cewa muradin sojin sama shi ne "lalata duk wani abu da ya shafi Hamas".
Har yanzu ba a san adadin mutanen da hare-haren suka kashe ko jikkata ba, yayin da Isra'ila ta katse layukan sadarwa da kuma intanet a zirin.