Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Tinubu ya gana da Ganduje da manyan hafsoshin tsaro

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Abdullahi Bello Diginza and Rabiatu Kabir Runka

  1. Ambaliyar Libya: An dakatar da koyarwa na wucin-gadi

    Firaministan gwamnatin hadin kan ƙasa ta Libiya Abdul Hamid Al-Dabaiba ya dakatar da koyarwa a makarantu a duk fadin kasar na tsawon kwanaki 10, a wani mataki na nuna goyon baya ga 'yan ƙasar da ambaliyar ruwa ta shafa a ranar 11 ga watan Satumba.

    Gwamnatin hadin kan kasa ta kasar Libya mai hedkwata a Tripoli babban birnin kasar ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da yammacin jiya Laraba.

    Gwamnatocin Libya biyu masu gaba da juna, gwamnatin hadin kan kasa da kasashen duniya suka amince da su karkashin jagorancin firaministan Al-Dabaiba da kuma gwamnatin gabashin Libya, karkashin jagorancin firaminista Osama Hamad.

    Dukkansu suna gudanar da ayyukan mayar da martani a gabashin Libya da ambaliyar ruwa ta shafa.

    Sanarwar ta kara da cewa dakatar da koyo zai ba da damar yin amfani da makarantu a matsayin mafaka na wucin gadi ga waɗanda suka tsira daga ambaliya.

    • Ana fargaba fiye da mutum 20,000 sun mutu a bala'in ambaliyar Libya
    • 'Tamkar ambaliyar tsunami ce ta auka wa birnin Libya'
  2. MDD ta gano manyan kaburburan bai-ɗaya a Darfur

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta samu wasu sahihan rahotanni da ke tabbatar da wasu manyan kaburbura na bai-daya akalla 13 a ciki da wajen birnin El Geneina da ke yankin Darfur na yammacin kasar Sudan.

    Ofishin Majalisar da ke Sudan ya ce yana da yaƙinin waɗannan kaburbura na da alaka da hare-haren da dakarun RSF da mayaƙan Larabawa suka rinka kaiwa kan fararan hula.

    Ofishin ya ce, idan har aka tabbatar, to wannan zai kasance babban laifin yaki a kasar.

    Yankin Darfur da birnin Khartoum aka fi yi wa fararan-hula illa tun soma yaƙin Sudan a cikin watan Afrilu.

    • Yadda ƴan bindiga ke ƙona ƙauyuka ƙurmus a Darfur
    • Majalisar Ɗinkin Duniya za ta fara aikin jin-ƙai a Sudan
  3. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar wannan shafin barkan mu da war haka.

    Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza ne ke fatan mun tashi ƙalau.

    Ni ce zan jagorance ku a tsawon wannan wuni domin kawo muku labarai da rahotanni daga Najeriya da asashe mawabtanta da kuma sauran sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu.