Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Tinubu ya gana da Ganduje da manyan hafsoshin tsaro

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Abdullahi Bello Diginza and Rabiatu Kabir Runka

  1. Rufewa

    Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Muna nan tafe da wasu sabbin rahotannin daga sassan duniya gobe da safe In sha Allah.

    Kafin goben, ku duba ƙasa domin karanta waɗanda muka kawo a yau.

    Kafin nan Rabiatu Kabir Runka ke cewa mu kwana lafiya

  2. An gurfanar da ɗan shugaban Amurka a gaban kotu

    Takardun kotu a Amurka sun nuna cewa an gurfanar da ɗan shugaba Biden, Hunter bisa zargin sa da laifin mallakar bindiga.

    Wannan dai shi ne karon farko da aka taɓa gurfanar da wani ɗan shugaban Amurka da ke kan Mulki.

    An tuhume shi da mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba yayin da ba ya cikin hayyacinsa sakamakon amfani da ƙwayoyi.

    Mista Hunter bai taba rike mukami a gwamnatin Amurka ba, amma akwai yiyuwar shari'ar sa za ta ɗauki hankali gabannin zaben shugaban ƙasa na shekara mai zuwa.

  3. Najeriya za ta biya kamfanonin jiragen sama bashin da suke bin ta

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umurci babban bankin ƙasar ya dinga shirya zama da masu harkar sufurin jiragen sama duk bayan wata uku don duba hanyar biyan su bashin kuɗaɗen waje da suke bin ƙasar da ya kai fiye da dala miliyon ɗari shida.

    A kwanan nan ne gwamnatin Najeriyar ta sasanta da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, bayan ƙasashen biyu sun dakatar da harkar sufurin jiragen sama a tsakanin su.

    Ministan sufurin Najeriya, Festus Keyamo ya ce "gwamnatin Najeriya ta damu sosai game da matsalolin da ake fuskanta a harkar sufuri, musamman matsalar ƙarancin kuɗaɗen waje, lamarin da ya janyo wa ƙasar wani abu mai kama da kantar biyan bashi, na kuɗaɗen wasu kamfanonin jirgin sama, na maƙuɗan kuɗaɗe da suka kai fiye da dala miliyan ɗari biyar.

    Kuma a halin da ake ciki, gwamnatin kasar ta dukufa wajen magance wannan matsala da ke yin tarnaki ga harkar sufurin jiragen sama.

    Gwamnatin Najeriyar dai ta ce ta yi wani shiri na inganta harkar sufurin jiragen sama a kasar, wanda zai ƙarfafa gwiwar ƴan kasuwa tare da ƙara inganta harkar baki ɗaya.

    Gwamnatin Najeriyar dai na daukar wadannan matakan ne a lokacin da ƙungiyar da ke kula da sufurin jiragen sama ta duniya ke kokawa game da gazawar gwamnatin Najeriya wajen biyan kamfanonin jiragen ƙasashen waje kuɗinsu da ya kai fiye da dala miliyan dari shida.

    Latsa alamar lasifika da ke ƙasa domin sauraron rahoton Ibrahim Isa

  4. An lalata wata garkuwar tsaron harin sama ta Rasha a yankin Crimea

    An sami rahoton fashewar abubuwa da dama a yammacin yankin Crimea da Rasha ta mamaye a Ukraine.

    Hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna gobara da hayakin da aka ce sun ɓullo ne daga kusa da yankin Yevpatoriya.

    Wata majiya a hukumar tsaro ta Ukraine ta shaida wa BBC cewa an lalata wani shingen tsaron hare-haren sama na Rasha.

    Ma'aikatar tsaron Rasha ba ta sanar da tabbacin wata barna ba amma dai ta yi maganar harbo jiragen yaki maras matuki tare da ikirarin dakile wani hari na daban da aka kai kan wani jirgin ruwan yaki.

  5. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 41 a Nijar

    Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 41 a daminar bana.

    Ambaliyar na faruwa ne sanadiyyar ruwan sama mai ƙarfi da ake samu a wasu sassan ƙasar.

    Rahoton da ofishin kare haƙiƙin jama'a na ƙasar ya fitar ya nuna cewar wasu daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu sun nutse ne a kogi ko rafuka yayin da wasu kuma gine-gine ne suka danne su.

    Rahoton ya kuma ƙara da cewa yankin Tahoua ne ya fi fama da matsalar inda mutum 15 suka rasa rayukansu.

    Sai Maradi inda mutum 11 suka mutu, yayin da mutum shidda suka rasa rayukansu a yankin Zinder.

    Tuni dai hukumomin kasar suka dauki matakai na taimaka wa waɗanda suka shiga mummunan hali sanadiyyar ambaliyar.

    Latsa hoton da ke ƙasa don sauraron rahoto kan ambaliyar ruwa a Nijar

  6. Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar tattara haraji ta FIRS

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya naɗa Hon. Zacch Adedeji a matsayin sabon shugaban riƙo na hukumar tattara haraji ta cikin gida ta Najeriya (FIRS).

    Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis.

    Shugaban ƙasar ya kuma umarci shugaban hukumar mai ci, Muhammad Nami ya tafi hutun ajiye aiki na wata uku, kamar yadda dokar aikin gwamnati ta tanada.

    Ngelale ya ƙara da cewa matakin ya fara aiki ne nan take.

    "An naɗa Hon Zacch Adedeji a matsayin shugaban riƙo na tsawon kwana 90 kafin a tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar na tsawon shekaru huɗu."

  7. Tinubu ya gana da Ganduje da manyan hafsoshin tsaro

    Shugaba Bola Tinubu ya gana da wani ayari ƙarƙashin jagorancin shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Abdullahi Uamar Ganduje a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja.

    Jaridar Punch ta ambata cewa ko da yake ba a bayyana manufar taron a bainar jama'a ba, amma dai ta fahimci cewa mahalarta sun gabatar da wata maƙala da ta ƙunshi muhimman shawarwari a kan hanyoyin da za a kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya a faɗin ƙasar.

    Jaridar ta ambato wata majiya na cewa taron wanda aka fara da tsakar ranar Alhamis ya buƙaci kasancewar manyan hafsoshin tsaron Najeriya saboda batun ya shafi al'amuran tsaron ƙasa.

    Rikicin manoma da makiyaya a Najeriya, ya yi sanadin mutuwar ɗumbin 'yan ƙasar a kan abincin dabbobi wanda ke daɗa ƙaranci sakamakon gurgusowar hamada da ɗumamar yanayi da bunƙasar jama'a, ke faɗaɗa buƙatun ƙasar noma.

  8. An sace gawar wani ɗan daban ƙasar Ecuador a maƙabarta

    Gawar wani riƙaƙƙen ɗan daban ƙasar Ecuador ta ɓata a cikin kabarinta da ke wata maƙabarta a Colombia, cewar 'yan sanda.

    An sanya gawar Junior Roldán a kabarin da ake kafewa a jikin bango cikin garin Envigado bayan an rasa wanda zai zo ya ce gawar makusancinsa ce.

    An gano gawar mutumin mai matsayi na biyu a Los Choneros, wata ƙungiyar 'yan daba a gidan yari da ta addabi ƙasar Ecuador, bayan harbe shi a cikin lardin Antioguia na ƙasar Colombia a watan Mayu.

    Ya tsere zuwa ƙasar Kwalambiya bayan har sau biyu an yi yunƙurin hallaka shi a mahaifarsa ƙasar Ecuador.

    An gano gawarsa da raunukan harsasai a ka cikin wani daji a ranar 6 ga watan Mayu.

    'Yan sanda sun yi zargin cewa mai tsaron lafiyarsa ne, wanda ya yi ƙoƙarin sace wasu maƙudan kuɗi daga shugaban 'yan daban ne, ya kashe shi, amma dai babu wani mutum da aka kama bisa alaƙa da wannan kisan kai.

  9. An dawo da lantarki a Najeriya

    An dawo da wutar lantarki a Najeriya, bayan ɗauke wuta a faɗin ƙasar sanadin durƙushewar babban layin lantarki na ƙasa da safiyar yau Alhamis.

    Lamarin dai ya haddasa rasa wutar lantarki ga kamfanonin raba lantarki a faɗin Najeriya.

    Sai dai an dawo da wutar, wadda ɗaukewarta ta shafi sassan Najeriya tsawon sa'o'i.

    Tun da farko dai Kamfanin tura wutar lantarki (TCN) ya tabbatar da durƙushewar babban layin lantarki na Najeriya, amma kuma ya ba da tabbacin cewa ana ƙoƙarin shawo kan lamarin.

  10. Hotunan barnar da ambaliyar ruwan Libiya ta haddasa a birnin Derna

    Ga wasu sabbin hotunan da suka bayyana irin barnar da ambaliyar ruwa a Libya ta haddasa a birnin Derna.

  11. Mitt Romney ya roƙi Biden da Trump su haƙura da takara a 2024

    Sanatan Amurka kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Mitt Romney ya yi kira ga Donald Trump da Joe Biden da su haƙura da takara a shekarar 2024 don bai wai sabbin ‘yan siyasa dama.

    Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan shirinsa na yin ritaya.

    Ya ce ya ɗauki matakin ƙin sake tsayawa takara a shekarar 2024 saboda lokaci ya yi da za a bai wa sabbin jini "damar zama shugabanni."

    Mista Romney, mai shekaru 76, ya shafe shekara 20 a harkokin siyasar Amurka, ciki har da gwamnan Massachusetts.

    A cikin 'yan shekarun nan, fitaccen ɗan jam'iyyar Republican ɗin ya zama mai sukar Biden da Trump.

    Zai ci gaba da rike mukaminsa har zuwa ƙarshen wa’adinsa na majalisar dattawa a watan Janairun 2025.

    A cikin wani bidiyo da Romney ke bayyana zaɓin nasa na ƙin sake tsayawa takara, wanda aka wallafa a shafukan sada zumunta a ranar Laraba da yamma, ya nuna cewa shekaru sun taka rawa wajen yanke shawararsa.

    • Zaben Amurka : Republican ta kama hanyar kwace Majalisar Wakilai
    • Kalubale shida ga yunkurin takarar Trump a wannan karon
  12. Ma'aikatan da suka rasa muhallansu na rayuwa a gidajen bulo

    Wasu gungun ma'aikata daga Sudan na cikin dubunnan da ambaliyar ruwan Libya ya rutsa da su kuma ya yi sanadin rasa matsugunansu.

  13. 'Za mu kawo wa Najeriya ɗaukin dala biliyan 2.5 don yaƙi yunwa'

  14. Afghanistan: China ta naɗa jakadan farko tun bayan da Taliban ta fara mulki

    Ƙasar China ta zama ƙasa ta farko da ta naɗa jakada a ƙasar Afganistan tun bayan da ƙungiyar Taliban ta karɓa mulki a shekarar 2021.

    Taliban ta ce naɗin Zhao Xing wata alama ce ga sauran ƙasashe na ƙulla alaƙa da gwamnatinta.

    Babu wata ƙasa da ta amince da gwamnatin Taliban da ake zargi da take hakkin bil'adama da dama a Afghanistan.

    Kasar China na daga cikin ƙasashen da suka fara hulɗa da su bayan sun hau karagar mulki a shekarar 2021.

    Ma'aikatar harkokin wajen kasar China a ranar Larabar ta bayyana cewa, Beijing za ta ci gaba da yin shawarwari da hadin gwiwa" da Afganistan, kuma manufarta game da kasar a bayyane take.

    Majalisar Dinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun yi Allah-wadai da ƙungiyar Taliban kan yadda take musgunawa mata.

    • A gurfanar da Taliban gaban kotu kan keta hakkin mata - Gordon Brown
    • Taliban ta zartar da hukuncin kisa na farko a bainar jama'a
  15. An kama mutumin da ya shafi jikin ƴar jarida tana tsakiyar ba da rahoto

    'Yan sandan ƙasar Sifaniya sun kama wani mutum bisa zargin taɓa wata 'yar jarida da iskanci, bayan ya shafa mata mazaunai ,tana tsakiyar ba da rahoto a tashar talbijin.

    Isa Balado na ba da rahoto ne a kan wani fashi da aka aikata a birnin Madrid ranar Talata, sai ya nufe ta kuma ga alama ya taɓa mata mazaunai, amma dai ya musanta hakan lokacin da ta tunkare shi.

    Misis Balado ta yi ƙoƙarin ci gaba da aikinta, amma sai mai gabatar da shirye-shiryen ya katse ta. "Isa, ki gafarce ni, na katse ki... wancan taɓa miki mazaunai ya yi ne?" Nacho Abad ya tambaya.

    'Yar jaridar dai ta tabbatar da haka, daga nan sai Mista Abad ya faɗa mata cewa ta ɗauki "sakaran" a kyamara, inda aka ga Isa Balado da mutumin, wanda har a lokacin yake tsaye kusa da ita, yana murmushi da dariya.

    "Yanzu idan kana son tambayar daga wacce tashar talbijin muke, dole sai ka taɓa min mazaunai? Ina tsakiyar ba da rahoto kai tsaye, ina cikin aikina," Misis Balado ta faɗa masa.

    Mutumin daga nan sai ya musanta cewa ya taɓa ta, kuma daidai lokacin da ya juya zai tafi sai ya yi yunƙurin yi mata wasan cakulkuli a kai.

    'Yan sanda daga baya sun ce an kama mutumin bisa zargin auka wa 'yar jaridar a lokacin da take gabatar da shirin talbijin kai tsaye, kamar yadda suka wallafa a wani saƙo cikin shafin X, tsohon dandalin Tuwita.

    Mediaset Espana, kamfanin da ya mallaki tashar talbijin ɗin, ya fitar da sanarwa, inda ya bayyana goyon bayansa ga Isa Balado bayan "lamarin da ta shiga wanda kwata-kwata ba za a lamunta ba", kuma "ƙarara ba zai taɓa amincewa da duk wani nau'in cin zarafi ko auka wa mutum ba".

    Ministar ƙwadago ta ƙasar Sifaniya, Yolanda Diaz ita ma ta yi jawabi game da lamarin, inda ta ce bai kamata ya ci bulus ba. Ta rubuta a shafin 'Yas: "Halayyar gardawa ce auka wa 'yan jarida da iskanci kamar haka, kuma masu halayyar ba sa ragawa hatta a kan idon kyamara."

    Wannan lamari na zuwa ne ana tsaka da wata dambarwa da ta jiɓanci nuna bambanci ga mata saboda jinsinsu, wanda tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya, Luis Rubiales ya janyo bayan ya sumbaci 'yar wasan da ta lashe Gasar cin Kofin Duniya a leɓɓanta.

    • 'Cin zarafin mace na cire mata yarda da amana'
  16. Najeriya na son ƙara yawan amfani da magungunan hana ɗaukar ciki da kashi 27%

    Gwamnatin Najeriya ta jaddada ƙudirinta na samun ƙarin masu amfani da magungunan hana daukar ciki zuwa kashi 27 cikin 100 nan da shekarar 2024.

    Babban Sakatare a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Daju Kachollom ce ta bayyana haka a wajen buɗe taron shekara-shekara na kwana biyu da ƙungiyar 'Society Family Health’s (SFH) Adolescent 360' (A360-Amplify) ta shirya, don ƙara nazari game da amfani da magungunan.

    Taron na mai taken: "ɗorawa a kan nasarorin da aka cimma a shirin bunƙasa lafiyar balagar masu tasowa a Najeriya”

    Kachollom, wadda Darakta a sashen kula da lafiyar iyali, Dakta Stella Nwosu ta wakilta, ta ce wannan matakin ba wai manufa ce kawai ba, amma alƙawari ne ga matasan kasar.

    “Wannan alƙawari ne na ƙarfafa matasa da ilimi da kayan aiki don yanke shawara mai kyau game da lafiyar jima'i da haihuwa".

    “Wannan shirin zai ba da fifiko mai ƙarfi kan Tsarin Dan Adam (HCD) da haɗa kai cikin tsarin kiwon lafiya da ci gaba na gwamnati.

    “Shirin ya samo asali ne ta hanyar fahimtar gamayyarmu cewa za a iya samun tasiri mai ɗorewa ta hanyar hada kai don tabbatar da "ɗorawa a kan nasarorin da aka cimma a shirin bunƙasa lafiyar balagar masu tasowa a Najeriya” ba tare da wani tangarɗa ba cikin yanayin kiwon lafiya.

    Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron ya ba da dama ga abokan tarayya da kuma masu ruwa da tsaki daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu don yin tunani kan sabbin hanyoyin da za a bi don dorewar shirin.

    • Mace ta dauki ciki sau biyu cikin kwana 10
    • Wasu mata sun shigar da ƙara saboda rashin basu damar zubar da ciki
  17. IMF na nazarin bai wa Sri Lanka bashin dala miliyan 3,000

    A yau Alhamis ne wata tawaga ta Asusun Bayar da Lamuni na duniya, IMF za ta isa Sri Lanka domin nazarin farko a kan bashin dala miliyan dubu uku da asusun zai bai wa ƙasar.

    Jami'an asusun za su duba irin tsare-tsaren da gwamnatin ƙasar ta yi na bunƙasa tattalin arzikinta a ƙarƙashin wani shiri na shekara huɗu da bankin na IMF ya amince da shi a watan Maris.

    Sri Lanka na bukatar ta gamsar da jami' an na IMF kafin dukkanin waɗannan maƙudan kuɗaɗe su shiga hannunta.

    A watan Maris ne IMF ya saki kashin farko na dala miliyan 330.

    A lokacin ziyarar ta kusan mako biyu , tawagar IMF za ta duba ta kuma yi nazari a kan shirin gwamnatin Sri Lankan na bunƙasa kudin haraji da take samu da kuma sabbin tsare-tsaren haraji da gwamnatin za ta ɓullo da su waɗanda ake sa ran gwamnatin za ta sanar a kasafin kuɗinta na gaba.

    Haka kuma gwamnatin ta Sri Lanka za ta gana da masu bayar da bashi na duniya domin sake tsarin yadda za ta biya basukan da ke kanta.

    Tuni daman dai ta roki masu bayar da bashin da su yafe mata kashi 30 cikin ɗari domin ta samu sauƙi.

    Yarjejeniyar ta IMF ta bai wa hukumomin Sri Lanka damar neman ƙarin bashi daga wasu kafofin na duniya masu bayar da bashin.

    To sai dai daga cikin sharuɗɗan da aka gindaya mata ana son ganin ta ɗauke tsauraran matakai na tsuke bakin aljihu wadanda ko alama ba za su yi wa talakawa daɗi ba, ciki kuwa har da rage ko janye tallafin man fetur

    Da haraji linki biyu da kuma sayar da wasu kamfanoni na gwamnati ga 'yan kasuwa

    A bara ne Sri Lanka ta ayyana cewa ta talauce, bayan da kuɗaɗenta na asusun ko-ta-kwana na waje suka ƙare, abin da ya haddasa matsloli na siyasa da tattalin arziki.

    • Abin da ya kamata ku sani kan asusun bayar da lamuni na duniya (IMF)
    • Ko bashin dala biliyan uku da Ghana za ta ciwo zai fitar da ita daga ƙangin tattalin arziƙi?
  18. Babban layin wutar lantarkin Najeriya ya durƙushe

    Babban layin wutar lantarki na Najeriya da kamfanin tura wutan lantarki (TCN) ke gudanarwa ya durƙushe a safiyar yau, Alhamis, lamarin da ya jefa kasar baki ɗaya cikin duhu.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa faɗowar na zuwa ne makonni kadan bayan da kamfanin tura wutar lantarki (TCN) ya yi bikin shafe sama da shekara guda ba a samu durƙushewar wutar lantarki a Najeriya ba.

    Wata sanarwar da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Enugu (EEDC) ya fitar, ta ce ɗurƙushewar ta afku ne da misalin karfe 12:40 na safe wanda ya yi sanadin daukewar wuta a faɗin ƙasar.

    “Saboda wannan lamarin na durƙushewar layin wutan lantarki a Nageriya, duk tashoshinmu na TCN ba su da wadatar tura wuta wanda hakan yasa ba za mu iya tura wuta ga abokan cinikinmu a jihohin Abia da Anambra da Ebonyi da Enugu da kuma Imo ba.”

    Wannan dai shi ne karon farko da aka fuskanci matsalar durƙushwar babbar layin wuta na ƙasa a karkashin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

    • Mene ne babban layin wutar lantarki na Najeriya kuma yaya yake aiki?
    • Abin da ya sa kamfanin dillancin wutar lantarki na Najeriya ya tafi yajin aiki
  19. Ba a bai wa kowannenmu naira miliyan 100 don rage raɗaɗi ba - Majalisar Wakilai

    Majalisar wakilan Najeriya ta musanta zargin da ke cewa kowane ɗan majalisa ya karɓi naira miliyan 100 daga gwamnatin tarayya a matsayin kuɗin rage raɗaɗi cire tallafi.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi, ya fitar ya bayyana iƙirarin - da mataimakin sakataren gamayyar ƙungiyar ƙwadogon ƙasar NLC, Christopher Onyeka ya yi - a matsayin zargi marar tushe.

    Mista Onyeka ya yi zargin cewa kowane ɗan majalisa ya karɓi naira miliyan 100 daga gwamnatin tarayya a matsayin tallafin rage raɗaɗi.

    Sanarwar ta Mista Rotimi, ta kuma buƙaci mataimakin sakataren NLC da ya fito ya nemi afuwar majalisar a bainar jama'a

    ''NLC a matsayinta na mai faɗa-a-ji a Najeriya ka iya rasa kimarta, idan aka same ta da amfani da ƙarya a cikin gwagarmayarta", in ji sanarwar.

    “Muna so mu bayyana cewa Mista Onyeka ya yi ƙarya a cikin iƙirarin nasa, domin kuwa babu inda 'yan majalisa suka karɓi wani kuɗi daga ɓangaren zartarwa a matsayin kudin rage raɗaɗi, saboda haka mun ɗauki wannan iƙirari a matsayin zargi marar tushe kuma abu ne da bai kamata ba''

    Mista Rotimi, ya ƙara da cewa "Muna so mu tunawa NLC da duka 'yan Najeriya cewa a cikin ƙasa da kwana 100 da ƙaddamar da majalisarmu ta 10, majalisar ta yi ƙoƙari wajen inganta jin daɗi da walwalar ma'aikata da sauran Najeriya".

    • Gamayyar ‘yan majalisar wakilai na adawa a Najeriya azarɓaɓi ne- Masana
    • Manyan abubuwa goma da sabuwar Majalisar Wakilan Najeriya za ta mayar da hankali kansu
  20. Ƙwararru a harkar fasaha na buƙatar a takaita amfani da AI

    Manyan kwararru a harkar fasaha tare da sanatocin Amurka sun gudanar da taro a birnin Washigton inda suka tattauna takaita yadda ake amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI.

    Manyan mahalarta taron sun hada da mai kamfanin Meta, Mark Zuckerberg da mai shafin Google Sundai Pichai da tsohon shugaban kamfanin Microsoft, Bill Gates.

    An yi wannan tattaunawa ne cikin sirri, amma kuma bayan taron, Mai kamfanin Tesla, Elon Musk, ya ce an cimma jituwa da fahimtar juna kan yadda za a takaita ayyuka, kuma taron ya kafa tarihi.

    Akwai fargabar Fasahar AI za ta taka rawa wajen yaɗa labaran boge ko ɓatar da mutane idan ba a tashi tsaye ba.

    • Masana na ganin Ƙirƙirarriyar basira ta AI ka iya kawo ƙarshen ɗan Adam
    • Manhajar ƙirƙirarriyar basira ta CHatbots ta kusa ta fi mutum kaifin basira