Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƴan bindiga sun kashe limaman coci 23 a Kaduna - CAN

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Buhari Muhammad Fagge

  1. 'Mutum 1,700 ne suka mutu a asibitinmu'

    Daraktan Asibitin Wahda da ke Derna ya ce mutum 1,700 ne suka mutu a asibitin ya zuwa yanzu.

    Dr Mohammed Al-Qabisi wanda ke da asibiti a ɗaya daga cikin yankunan da lamarin ya fi shafa, yace sun riƙa ƙirga gawarwakin da aka shimfiɗar a ƙasa.

    "Akwai gawarwakin da ba a kai ga ganewa ba," in ji shi, waɗanda a cewarsa ake ɗauka hoto kuma ke ba su lambobi.

    Ana tsammanin ƙara samun gawarwaki sakamakon aikin ceton da ake ci gaba da yi, sai dai Dr Qabisi ya ce damuwarsa shi ne aikin ya fi ƙarfin ma'aikatansu, saboda ƙarancin kayan aiki.

    "Abubuwa sun munana; kuma asibitin a lalace yake," a cewarsa.

  2. Putin da Kim Jong Un sun haɗu a tashar harba kumbo ta Vosto-chny

    Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da takwarsan na Rasha Vladimir Putin sun hadu a tashar harba kumbo ta Vosto-chny da ke gabashin Rasha inda za su tattauna.

    Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Telegram na gwamnatin Kremlin, ya nuna shugabanni biyu na musabaha.

    Mista Kim, wanda ya shiga Rasha da jirgin kasa mai sulke a safiyar ranar Talata, ya samu rakiyar manyan hafsoshin tsaronsa a ziyara ketare ta farko da ya ke kai wa a cikin shekaru hudu.

    Wakiliyar BBC da ke aiko rahoto daga can ta ce kada ku yi tunanin za a samu bayanai kan duk wata haramtacciyar yarjejeniyar da za su ƙulla.

    Kasahen duniya dai na nuna rashin gamsuwa da sabuwar alaƙar wadannan kasashe biyu.

    • Putin da Kim: Abokai a lokacin neman makamai
  3. Rema ya doke Davido, Burno Boy, Wizkid da kuma Ayra Starr

    Matashin mawaki a Najeriya wanda ke tashe, Rema ya lashe kyautar waka mafi shahara a salon 'Afrobeats' saboda wakarsa mai suna 'Calm Down' a bukin karamma mawaka na MTV Video Music Awards.

    Ya doke sauran manyan mawaka a Najeriya irinsu Burna Boy, Davido, Wizkid, Fire Boy da kuma Ayra Starr domin lashe wannan kyautar a ranar Talata.

    Kawo yanzu an saurari wakar 'Calm Down' fiye da sau biliyan daya a manhajar Spotify.

    An gudanar da bikinne a Newark da ke New Jersey a Amurka

  4. Faransa ta haramta sayar da iPhone 12 a cikin ƙasarta

    Hukumomi a Faransa sun umurci kamfanin Apple da ya daina sayar da wayoyinsa na iPhone 12 a ƙasar, suna iƙirarin tana fitar da tururin radiyeshan (radiation) mai yawa sama da wanda Tarayyar Turai ta amince wayoyi su iya fitarwa.

    Hukumar sa ido kan tururin sinadaren radiyeshan na ƙasar ANFR ta sanar da Apple shawarar da ta yanke bayan ta gudanar da gwaje-gwaje.

    Kamfanin na Amurka yana da kwanaki goma sha biyar don sabunta manhajarsa wadda hukumomin Faransa suka ce zai rage tururin radiyeshan na wayar zuwa matakan da za a amince da su.

    Idan kamfanin Apple bai cika wannan wa'adin ba, gwamnati ta ce za ta dakatar da sayar da dukkan wayoyinsa na iPhone 12 a ƙasar.

    Har yanzu dai kamfanin Apple bai mayar da martani ba.

    • An sayi tsohuwar wayar iPhone kusan naira miliyan 32
  5. Ƴan bindiga sun kashe limaman coci 23 a Kaduna - CAN

  6. Labarai da dumi-dumi, Sama da mutum 5,000 sun mutu a ambaliyar ruwan Libya

    An gano sama da gawarwaki 5,000 a birnin Derna na kasar Libiya da ambaliyar ruwa ta shafa, kamar yadda wani minista a gwamnatin gabashin Libiya ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Hichem Abu Chkiouat, ministan sufurin jiragen sama, ya ce ana sa ran adadin waɗanda suka mutu zai karu, kuma mai yiwuwa ma ya ninka.

    • 'Tamkar ambaliyar tsunami ce ta auka wa birnin Libya'
    • Ambaliyar ruwa ta shafi sama da mutum 500,000 a Najeriya
  7. Hotunan ɓarnar da mummunar ambaliyar ruwa tayi a Libya

    Ana ci gaba da gudanar da bincike da ceto a kasar Libya da ambaliyar ruwa ta auka wa.

    Ga wasu hotunan ɓarnar da ambaliyar ruwan ta yi.

  8. Koriya ta Kudu da Japan sun ce Koriya ta Arewa ta harba makamai biyu masu linzami

    Koriya ta Kudu da Japan sun ce Koriya ta Arewa ta harba makamai biyu masu linzami daga gabar tekunta da ke gabashin ƙasar.

    Japan ta ce tana zargin shu'umin makamin ya faɗa a wajen yanki na musamman da take harkokin kasuwancinta.

    Kwamitin tsaro na MDD dai ya haramtawa Koriya ta Arewa gwajin irin wannan makami, da sauran ayyukan da suka shafi makaman nukilliya.

    • Koriya ta Arewa: Harba makamai masu linzami 10 ya razana makwabtanta
    • Kumbon leƙen asirin Koriya ta arewa ya faɗa cikin teku
  9. An kashe masu fafutukar kare muhalli 177 a faɗin duniya

    Wata ƙungiyar fafutuka ta wallafa wani rahoton da ke cewa an kashe mutane 177 a sassan duniya a bara saboda kokarinsu na kare muhalli.

    Ƙungiyar Global Witness ta ce kashi kusan 90 cikin 100 na wannan kisa an aikata shi ne a yankin Latin Amurka kuma galibin wadanda ake kashewa 'yan Colombia ne - sai Brazil da Mexico da Honduras.

    Wata mai fafutikar kare muhalli Nadia Umana ta ce daga watan Nuwamban 2021 zuwa Agusta 2022 an kashe masu magana da yawun kungiyarmu hudu, kuma gaskiya lamarin akwai tsoratarwa.

    A rahotanta na shekara-shekara, ƙungiyar ta ce shugabannin gargajiyar yankunan aka fi yiwa wannan kisa.

    Ana dai alakanta masu hako ma'adinai ta haramtacciyar hanya da sare bishiyoyi domin yin katako da aikata wannan kisa.

    Sannan ƙungiyar ta ce ko a kasashen Afirka da Asiya da Gabas ta tsakiya ana cin karo da wannan matsalar.

  10. Abin da muka sani kan ambaliyar ruwa a Libya ya zuwa yanzu

    Ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta ce aƙalla mutane dubu 10 ne suka ɓata a gabashin Libya bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta ɗaiɗaita yankin.

    A birnin Derna da ke gabar teku inda aka samu ɓallewar madatsun ruwa biyu da gadoji hudu, an binne gawarwakin mutane da aka iya ganowa a rami guda.

    Hukumar agajin gaggawa ta yankin na cewa akalla mutum dubu biyu da dari uku ne suka mutu.

    Hotunan bidiyo sun rinƙa nuna yadda ruwa ya malale unguwanni da kuma barnar da ya yi.

    Har yanzu dai ba a kai ga tantace girman barnar da ambaliyar ta haddasa ba.

  11. Barka da safiya

    Masu bibiyar wannan shafin barkan mu da war haka.

    A'isha Salisu Babangida da Buhari Muhammad Fagge ne ke fatan mun tashi ƙalau.

    Ni ce zan jagorance ku a tsawon wannan wuni domin kawo muku labarai da rahotanni daga Najeriya da asashe mawabtanta da kuma sauran sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu.