Ana zargin matashi da kashe wasu mutum biyu ta hanyar tsafi a Bauchi
A Najeriya, rundunar 'yan sandan kasar tana gudanar da bincike kan wani matashi mai sana'ar gawayi da ke kauyen Taranka, na jihar Bauci, wanda ta damke bisa zargin kashe wasu mutum biyu 'yan asalin kauyen Dankunkuru na yankin karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.
Ana zargin matashin da kashe mutane ya na cin namansu, kuma an gano gawawwakin matasan biyu da ya binne a gidansa.
Rundunar 'yan sandan ta ce matashin mai suna Ibrahim Muhammad, mai shekara 40, na hannunta inda za a fadada bincike bisa zargin da ake masa.
SP Ahmed Mohammed Wakil, shi ne mai magana da yawun rundunar 'yan sandan a jihar Bauci, ya shaida wa BBC cewa matashin ya musanta dukkan zargin da ake masa, to amma ko a lokacin da aka kai shi ofishin 'yan sandan an same shi da jini a roba, to amma sai ya ce jini ne na bushiya da kurkuru ba jinin mutum ba ne, kuma da jinin ya ke amfani ya na maganin maciji.
SP Ahmed Wakil, ya ce koda suka je gidansa an ga adduna da fatanya da jini a cikin roba.
Ya ce, " Game da kaburburan da ake zargi ya binne matasa biyu da ya kashe, muna bincike a kai don gano gaskiyar komai."