Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Fiye da mutum 20 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Neja

Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Abdullahi Bello Diginza

  1. Ma'aikatan lafiya 400,000 sun yi kaɗan a Najeriya - Minista Pate

    Ministan Lafiya da walwalar al'umma na Najeriya Farfesa Ali Pate ya ce ma'aikatan lafiya 400,000 sun yi ƙadan a Najeriya, idan aka yi la'akari da buƙatarsu da ake yi a ƙasar.

    Pate ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja a ranar Asabar, bayan wata tattaunawa da aka kwashe kwana uku ana yi tsakaninsa da sauran hukumomi da ke ƙarƙashin ma'aikatar lafiya.

    Ma'aikatar ce ta tsara wannan tattaunawa domin fito da wata sabuwar hanya da za a gyara tsarin lafiya a ƙasar.

    A cewar Pate waɗannan ma'aikata 400,000 da ake magana sun haɗa da ma'aikatan lafiya da ma su jinya da unguwar zoma da masu haɗa magunguna da masu aiki a ɗakunan gwaji da sauran ma'aikatan da ke taimakawa a ɓangaren lafiya.

    "Ba za su isa ba, ko kuna zaton wannan adadin zai iya kula da lafiyar mutum miliyan 220 da ke Najeriya.

    "Adadin likitocin da muke da shi a Najeriya ya yi ƙasa sosai da wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ya kamata kowacce ƙasa likitocinta sukai.

    "Akwai damar samar da ƙarin wasu. Ko kuma mu samar da sama da adadin da muke buƙata domin akwai ƙarancinsu a duniya, a yanzu haka akwai ƙarancin ma'aikatan lafiya miliyan 18 a faɗin duniya.

  2. Girgizar ƙasa ta shafi aƙalla mutum 300,000 a Marrakesh

    Sama da mutum 300,000 ne girgizar ƙasa ta shafa a Marrakesh da ƙauyukan da ke gefen garin a Morocco, kamar yadda ofishin jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana.

    Rahotanni sun ce ofishin na "bibiyar abubuwan da suke faruwa a Morocco sau da ƙafa kuma a shirye yake ya kai ɗauki".

    A wata sanarwa da ya fitar tun da fari ya ce, MDD ta ce a shirye take ta taimakawa gwamnatin Morocco a ƙoƙarin da take na shawo kan lamarin.

  3. An fara zaman makokin kwana uku a Moroko

    A jiya ne Sarkin Muhammad na shida ya ayyana zaman makokin kwana uku a faɗin ƙasar.

    Ya kuma bayar da umarnin kai taimakon tanti da abinci da sauran kayan agaji ga waɗanda suka tsira - sannan ya tura sojoji domin su taimaka wajen aikin ceto da ake ci gaba da yi.

    An sauke tutocin ƙasar zuwa rabi a kusan duka gine-ginen ƙasar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya rawaito.

  4. 'Rasha ta shafe daren Asabar tana ɓarin wuta a Ukraine'

    Magajin garin Kyiv, ya ce Rasha ta shafe daren Asabar ta na kai hare-hare a Ukraine da jirage marassa matuka.

    Vitali Klitschko ya yi kira ga mazauna birnin su ci gaba da kasancewa a inda suke fakewa, domin kaucewa hadari sakamakon gine-ginen da ke rushewa, saboda martamnin da ma'aikatar tsaron kasar ke maidawa.

    A wani sako da ya wallafa ta manhajar Telegram, Klitchko ya ce an tura jami'an daukin gaggawa yankunan da lamarin ya shafa.

    Shi ma shugaban sojin Kyiv, Sergiy Popko, ya ce baraguzan gini da suka fada kan wayar lantarki sun janyo gobara a gundumar Cheva-Shenki-Visky-chenki.

    A na ta ɓangaren Rasha ta ce ta harbo jirage marassa matuƙa takwas da Ukraine ta harba mata a Bahrul Aswad, kusa da yankin Crimea.

  5. Faransa na neman nuna turjiya kan umarninmu - Sojojin Nijar

    Gwamnatin soji a Nijar ta zargi Faransa da a bin da ta kira jan ƙafa wajen janye sojojin ta daga ƙasar.

    A wata sanarwa da sojin da sukai juyin mulki suka fitar, sun ce har yanzu babu alama ko shirin janye dakarun da aka cimma a farkon watan nan tsakanin su da kwamandan sojojin Faransa a yankin Sahel.

    Sanarwar ta ƙara da cewa tsohuwar uwar gijiyarta na nuna turjiya a fakaice kan batun.

    Dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashn biyu, sun bayan sojoji sun hamɓarar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum tare da tsare shi, tun a watan Yuli da ya wuce.

    An dai ta yin zanga-zanga musamman a birnin Yamai, ciki har da sansanin sojin Faransar da 'yan ƙasar suke kiraye-kiraye kan sojojin Faransar su fice daga Nijar.

  6. An shiga rana ta biyu a taron G20

    Firai Ministan India, Narendra Modi, na karɓar baƙuncin shugabannin ƙasashen duniya a babban dakin taro na Rajghat wanda aka gina domin girmamawa ga gwarzon ƙasar Mahatma Gandhi.

    Wannan na zuwa ya yin da aka shiga rana ta biyu da fara taron manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi na duniya wato G20.

    A jiya Asabar, G20 sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa kan yaƙin da ake yi a Ukraine, sai dai babu inda sanarwar ta ambato mayaya da kaddamar da yakin da Rasha ta yi a Ukraine.

    Abun mamaki ne ace an fitar da sanarwar hadin gwiwa gabannin kammala taron, wanda a ganin masu sharhi hakan na nufin shugabannin sun tattauna batun yakin Rasha da Ukraine tun gabannin fara taron.

    Nan gaba a yau ake sa ran shugabannin ƙasashen za su yi tattaunawa ta ƙarshe na taron.

  7. Girgizar ƙasar Moroko - Adadin waɗanda suka mutum ya haura 2,000

    Dubban 'yan Moroko ne suka shafe dare na biyu a kan tituna, inda hukumomin su ka ce adadin waɗanda suka mutu sakamakon girgizar ƙasa sun haura 2000.

    Ma'aikatar cikin gida ta ce, a kudancin Marrakesh ne girgizar ƙasar ta fi yin muni.

    Girgizar ƙasar ta shafe garuruwa, iyalai da dama sun maƙale a baraguzai gidansu, ma'aikatan agaji sun gagara isa yankunan sakamakon rashin hanya.

    Sarki Muhammad na Morocco, ya ayyana makokin kwanaki uku a kasar, tare da ba da umarnin taimakawa waɗanda lamarin ya shafa da waɗanda suka fice daga gidajensu domin tsira da rai.

    Rabon ƙasar ta fuskanci bala'in girgizar ƙasa tun wadda ta faru a shekarar 1960 a yankin Agadir, inda mutane 12,000 suka mutu.

  8. Barka da hantsi

    Ma su bibiyar wannan shafin barka da hantsi.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan an tashi kalau.

    Ni zan kasance da ku a tsawon wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu.