Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Kuɗin aikin hajjin 2024 na iya kaiwa naira miliyan biyar'

Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Abdullahi Bello Diginza

  1. Indiya ta gayyaci Tarayyar Afrika ta zama mamba a G20

    Yayin buɗe taro Firaiministan Indiya Modi ya gayyaci Tarayyar Afrika ta zama mamba ta dindindin a ƙungiyar G20.

    Mambobi da dama sun amince da sanya AU a wannan ƙungiya tun gabanin taron.

    Wannan wani mataki da Modi ya ɗauka wani ƙoƙari ne na mayar da Indiya muryar kudancin duniya.

  2. 'Za a gudanar da zaɓe a Gabon nan da shekara biyu'

    Sabon Firai Ministan Gabon, Raymond Ndong Sima, ya shaida wa BBC ya na fatan za a gudanar da zaɓe nan da shekaru biyu masu zuwa a ƙasar.

    Sojojin da suka hamɓarar da mulkin shugaba Ali Bongo sun yi alƙawarin gudanar da sahihin zabe, amma ba su ƙayyade lokaci ba.

    Mista Sima ya ƙara da cewa nan da kwanaki masu zuwa ne za a sanar da takamaimai lokacin da za a gudanar da zaben, bayan kammala taron da za su yi da jam'iyyun siyasar Gabon.

    Ya kara da cewa za a ɗauki lokacin kafin karfin fada ajin iyalan Bongo ya kau a Gabon, amma ya ce za a gurfanar da Mista Bongo gaban shari'a wanda a yanzu sojin da sukai juyin mulkin suka sake shi tare da ba shi damar barin ƙasar idan ya na muradi.

  3. Yadda shugabannin duniya suka isa taron G20

    Tun gabanin fara taron shugabanni daban-daban na duniya suka fara isa.

    Shugabannin Amurka da Burtaniya da Canada da Masar duka sun isa taron.

  4. An fara taron G20 a India

    A yau ake buɗe taron manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi na G20, wanda a bana kasar Indiya ke karɓar baƙunci, sai dai biyu daga cikin ƙasashen da ke sahun gaba wato Rasha da China ba su halarci taron ba.

    Tuni shugabannin ƙasashen suka fara taruwa a sabon ɗakin taron da aka gina a birnin Delhi.

    Shugabannin za su tattauna kan batutuwa masu muhimmanci ciki har da matsalar sauyin yanayi, da matsalolin da ƙasashe masu tasowa ke fuskanta, sai dai ana sa ran yaƙin da Rasha ta ƙaddamar a Ukraine ya mamaye taron.

    Da alama akwai kyakkyawan fata, ganin yawancin shugabannin kasashen sun amince da buƙatar Firai Ministan Narendra Modina ta gayyatar ƙungiyar Tarayyar Afirka domin shiga cikinsu su tashi daga G20 zuwa G21.

  5. Barka da safiya

    Ma su bibiyar wannan shafin barka da hantsi.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan an tashi kalau.

    Ni zan kasance da ku a tsawon wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu.