Amurka ta sanya wa wani babban jami'in RSF na Sudan takunkumi
Amurka ta ƙaƙaba wa wani babban jami'in rundunar mayaƙan RSF na Sudan takunkumi sakamakon rikicin ƙasar.
An sanya wa Abdelrahim Dagalo, mataimakin shugaban rundunar takunkumi kan cin zarafin ɗan'adam a lokacin yaƙin da rundunar ke yi da sojojin Sudan.
Amurka ta sanar da matakin ne ranar Laraba, a wani martani da ta yi kan mummunan rikici da aka samu a yankin Darfur da ke yammacin ƙasar, inda aka zargi RSF da haɗa kai da ƙungiyar 'yan tayar da ƙayar baya ta yankin.
Amurka ta zargi Mista Dagalo da laifukan da suke da alaƙa da cin zarafin ɗan'adam, irin su "fyaɗe da kashe mutane saboda ƙabilarsu".
Masu sanya ido kan yaƙe-yaƙe da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama da shaidu na zargin RSF da hannu da rikicin yankin Darfur.