Ana ci gaba da mayar da martani a Najeriya kan hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe na ranar Laraba, wanda ya bai wa Shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima nasara.
Kotun dai ta kori buƙatar masu ƙorafi da ke neman soke cancantar zaɓen Bola Tinubu da mataimakin nasa.
Kuma jim kaɗan bayan fitowa daga kotun, mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima wanda ya halarci zaman kotun na tsawon wunin rana, ya yi kira ga masu ƙorafin da cewa su zo su mara baya ga gwamnatinsu don yin tafiya tare da nufin ciyar da al'ummar Najeriya gaba.
A cewarsa, lokacin siyasa ya wuce, kamata ya yi 'yan adawar su ba da dama ga gwamnati ta mayar da hankali wajen sauke nauyin da 'yan Najeriya suka ɗora mata na kawo sauƙi a rayuwarsu, musamman a wannan lokaci na matsin rayuwa.
Sai dai, Kashim Shettima ya yi amfani da wannan damar wajen yin wasansu na Fulani da Bare-bari, inda ya ce zai saya wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar awaki, ya mayar da shi garinsu, ya je ya yi kiwo.
Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan yanke hukuncin kotun ƙararraƙin zaɓen shugaban ƙasar ranar Laraba.
Bayan ya yi kira ga abokan hamayyarsa a siyance da su haɗa hannu wajen ciyar da Najeriya gaba, ɗaya daga cikin 'yan jarida ya tambaye shi ko zai yi wa Atiku ritaya a siyasance kamar yadda ya taɓa ambatawa a lokacin yaƙin neman zaɓe?
"A yanzu mun shiga lokacin mulki, mun wuce batun zaɓe. Atiku Abubakar dattijon ƙasa ne da nake matuƙar girmamawa", in ji tsohon gwamnan na Borno.
"Duk wanda ya san irin wasan barkwancin da ke tsakanin ƙabilar Fulani da ta Kanuri ya san cewa ina da damar tsokanarsa yadda na ga dama".
“Don haka ba za mu mayar da Atiku Dubai ko Morocco ba, a maimakon haka zan mayar da shi Fombina, in saya masa awaki da kaji domin ya yi kiwo''.
Duk da haka ya kuma ce: "Haƙiƙanin gaskiya, Atiku dattijon ƙasa ne. Najeriya tana buƙatarsa''.
“Ƙwarewa ba abu ne da za ka sayo a kasuwa ba. Za mu ƙaru da ƙwarewarsa wajen gina ƙasarmu, siyasa ta ƙare yanzu maganar gwamnati ake yi".
-
Mene ne asalin wasan da ke tsakanin Barebari da Fulani?
-
Ina neman afuwar Musulmai kan kalamaina – Kashim Shettima