Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kotu ta yi watsi da ƙarar Atiku da Peter Obi

Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Kotu ta yi watsi da ƙorafin LP kan rashin aika sakamakon zaɓe ta laturoni

    A ci gaba da karanto hukuncin ƙorafe-ƙorafen jam'iyyar LP, kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yi watsi da ƙorafin rashin aika sakamakon zaɓe ta laturoni.

    Jam'iyyar ta yi ƙorafin cewa hukumar INEC ba ta aika dukkan sakamakon zaɓe ta laturoni ba kamar yadda ta yi alƙawari.

    To sai dai Mai Shari'a Haruna Tsammani ya ce ba dole ne sai ta aika sakamakon ta laturoni ba, yana mai cewa fashin baƙin da kotun ta yi wa tanade-tanaden dokar zaɓe ta 2022, INEC tana da hurumin yin hakan, amma bai zama wajibi a kanta ba.

  2. Kotu ta kori ƙorafin samun kashi 25 na ƙuri'un Abuja

    Hukuncin da Mai shari'a Haruna Tsammani ke ci gaba da karantowa, ya ce kotun ta kori ƙorafin da Peter Obi da jam'iyyar LP suka yi cewa akwai buƙatar sai ɗan takara ya samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a Abuja, kafin ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

    Kotun ta ce mazaunan Abuja, ba su da wata alfarma ta musamman kamar yadda masu ƙorafin suka yi iƙirari.

    Tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadin cewa dole sai takara ya samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a kashi biyu cikin uku a jihohin ƙasar da Abuja, kafin ya samu nasarar zama shugaban ƙasa.

  3. Ana ci gaba da karanto hukuncin ƙarshe kan jam'iyyar LP

    Har yanzu alƙali da ke jagorantar hukunci kan ƙararrakin zaɓe na ci gaba da karanto hukuncin jam'iyyar LP.

    Mayan Jam'iyyun adawa a Najeriyar ne dai suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar nasarar da Bola Tinubu na APC ya yi a zaɓen shugaba ƙasar da ya gabata cikin watan Fabrairu.

    Tun da farko kotun ta yi watsi da ƙarar jam'iyyar APM, tana mai cewa ƙarar da jam'iyyar ta shigar, batu ne da ya shafi harkokin da ake la'akari da su kafin zaɓe, don haka kamata ya yi ta shigar da ƙarar a gaban babbar kotu.

    Cikin hukuncin LP da Alƙalin ya karanto ya ce LP ta kasa gamsar da kotun da hujjojin da take da su kan ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu na APC a zaben shugaban ƙasa.

    Jam'iyyar LP na zargin INEC da rage mata adadin ƙuri'u tare da ƙara wa jam'iyyar APC mai mulki a lokacin zaɓen shugaban ƙasar.

    To sai dai kotun ta ce jam'iyyar ta kasa faɗin adadin ƙuri'un da ta samu kafin ta ce a rage mata, haka kuma kotun ta ce jam'iyyar ba ta bayyana sunayen rumfunan zaɓen da aka yi abain da ta yi iƙirarin.

  4. Kotu ta soke zaɓen sanatan APC inda ta bai wa 'yar takarar PDP nasara a Kogi

    Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke zamanta a jihar Kogi ta soke nasarar Sanata Abubakar Ohere, a matsayin ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.

    Haka kuma kotun ta ayyana Natasha Akpoti-Uduagan ta jam'iyyar PDP a matsayin wadda ta lashe zaɓen da aka gudanar cikin watan Fabrairu.

    Jagoran alƙalan kotun Mai shari'a K. A Orjiako ya ce kotun ta gamsu da hujjar da aka gabatar cewa an ƙara wa Ohere ƙuri'u a rumfunan zaɓe guda tara cikin ƙaramar hukumar Ajaokuta.

    Yayin da kotun ta ce an rage wa Natasha ƙuri'u da gangan a hukumar zaɓe da kuma wasu rumfunan zaɓe uku da ba a shigar wa 'yar takarar ba a ƙaramar hukumar.

    Bayan da kotun ta kammala tattara alƙaluman ne ta ayyana Natasha ta jam'iyyar PDP a matsayin wadda ta yi nasara a zaɓen bayan da kotun ta ce ta samu ƙuri'a 54,074, yayin da ta ce Sanata Ohere ya samu kuri'a 51,291.

  5. 'LP ta kasa gamsar da kotu da hujjoji'

    Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta ce jam'iyyar LP ta kasa gamsar da kotun da hujjojin da take da su kan ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu na APC a zaben shugaban ƙasa.

    Jam'iyyar LP na zargin INEC da rage mata adadin ƙuri'u tare da ƙara wa jam'iyyar APC mai mulki a lokacin zaɓen shugaban ƙasar.

    To sai dai kotun ta ce jam'iyyar ta kasa faɗin adadin ƙuri'un da ta samu kafin ta ce a rage mata, haka kuma kotun ta ce jam'iyyar ba ta bayyana sunayen rumfunan zaɓen da aka yi abain da ta yi iƙirarin.

    Haka kuma LP ta yi zargin yin aringizo a zaɓen, sai dai kotun ta ce jam'iyyar ta kasa yin bayanin wuraren da aka yi aringizon ƙuri'un ba.

  6. Ghana za ta samu ƙarin bashin dala miliyan 600 daga IMF

    Ministan kuɗin Ghana Ken Ofori-Atta ya ce yana da ƙwarin gwiwwa cewa ƙasar za ta samu ƙarin dala miliyan 600, a matsayin kashi na biyu na bashin da Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF ke bai wa ƙasar kafin ƙarshen shekarar nan.

    A cikin watan Mayu ne Ghana ta sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da IMF da zai ba ta damar samun bashin dala biliyan uku a cikin shekara uku domin taimaka mata wajen magance matsalolin tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.

    Tuni kasar ta karɓi rukunin farko na kudin da ya kai dala miliyan 600, to sai dai dole gwamnatin ƙasar ta dauki wasu matakai da za su ba ta damar samun rukuni na gaba na kuɗaɗen.

    Gwanatin ƙasar ta ce za ta sake nazarin matakan cikin watan Nuwamba.

    Mista Ofori-Atta ya ce akwai alamun samun ci gaba a harkokin tattalin arzikin ƙasar.

  7. An shiga hukuncin ƙarar jam'iyyar LP

    Kotun da ke sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa Najeriya ta shiga ƙarar jam'iyyar LP domin yanke hukunci kan ƙarar da jam'iyyar ta shigar tana ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata.

    Jam'iyyar LP na daga cikin jam'iyyun adawar da ke ƙalubalantar nasarar da INEC ta ce Bola Tinubu na APC ya samu a zaɓen shugaban ƙasar na watan Fabrairu.

    Tun da farko kotun ta yi watsi da ƙarar jam'iyyar APM, tana mai cewa ƙarar da jam'iyyar ta shigar, batu ne da ya shafi harkokin da ake la'akari da su kafin zaɓe, don haka kamata ya yi ta shigar da ƙarar a gaban babbar kotu.

    Dan takarar jam'iyyar, LP Peter Obi ne ya zo na uku a zaɓen da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

  8. Shugaban mulkin sojin Gabon ya gana da ɗan takarar jam'iyyar adawa

    Shugaban mulkin sojin Gabon Janar Brice Oligui Nguema ya gana da ɗan takarar jam'iyyar adawa Albert Ondo Ossa a wani yunƙuri na tuntuɓar ɓangarori domin sake gina ƙasar

    Mista Ossa ne babban ɗan takarar jam'iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasar da sojoji suka yi watsi da shi bayan kifar da shugaban ƙasar Ali Bango a makon da ya gabata.

    Shugabannin mulkin sojin na zawarcin jam'iyun adawa domin shiga gwamnatinsu.

    Mista Ossa dai ya ƙaurace wa bikin rantsar da Janar Nguema ranar Litinin.

    Yana mai iƙirarin cewa shi ne ya samu nasara a zaɓen da sojojin suka yi watsi da shi, dan haka shi ya kamata a rantsar a matsayin sabon shugaban ƙasar.

    Ganawa tsakanin jagororin biyu alama ce da ke nuna cewa jam'iyyar adawa na da rawar da za ta taka a gwamnatin sojojin.

  9. Kotu ta kori ƙarar APM

    Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ta kori ƙorar da jam'iyyar APM ta shigar gabanta tana neman a soke cancantar Bola Ahmed Tinubu, na jam'iyyar APC a zaɓen watan Fabrairu.

    Yayin da yake karanta hukunci Mai shari'a Haruna Tsammani da ke jagorantar alƙalan kotun biyar, ya ce ƙarar da APM ta shigar, batu ne da ya shafi harkokin da ake la'akari da su kafin zaɓe, don haka kamata ya yi ta shigar da ƙarar a gaban babbar kotu.

    Jam'iyyar APM ta shigar ƙarar a kan Bola Ahmed Tinubu da Hukumar Zaɓe ta INEC da kuma Kabiru Masari, mutumin da ɗan takarar APC a wancan lokaci ya fara gabatar wa INEC a matsayin wanda ke mara masa baya kafin ya sauya shi da Kashim Shettima.

    Haka kuma jam'iyyar tana ƙalubalantar ɗaukar Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa ne. Tana cewa maye shi a gurbin Kabiru Masari, ya saɓa wa tsarin mulki.

    Kotun dai ta ce ko kaɗan APM ba ta da hurumin na shiga cikin harkar da ta shafi jamiyyar APC

  10. Ɗaya daga cikin abubuwa uku da zai iya faruwa a zaman kotun

    Manyan 'yan siyasar Najeriya ciki har da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugabannin jam'iyyun APC da PDP da wasu gwamnonin ƙasar duk sun halarci zaman kotun na yau inda za a yanke hukunci kan karar da 'yan adawa suka shigar kan nasarar Bola Tinubu na APC.

    Abu uku zai iya faruwa a yau:

    • Kotun za ta iya tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a zaben 2023 tare da korar karar baki daya
    • Kotun za ta iya soke zaben gaba daya, ta ce a sake wani.
    • Kotun za ta iya soke sakamakon zaben wadansu jihohin domin a sake zabe a wadannan jihohin.
  11. Kotu ta tafi hutun minti 15

    Kotun da ke sauraron ƙararakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya ta sanar da tafiya hutun minti 15 domin ci gaba da yanke hukuncin ƙararrakin da ke gabanta.

    Mai shari'a Haruna Tsammani da ke jagorantar sharia'r ne ya sanar da tafiya hutun bayan dogon lokaci da ya ɗauka yana karanta hukunci wasu daga cikin shari'un da ke gaban kotun.

    A hukuncin da kotun ta yanke kafin tafiya hutun ta kori ƙorafin jam'iyyar APM da ke neman a soke cancantar Bola Ahmed Tinubu, na jam'iyyar APC a zaɓen watan Fabrairu.

    Shi ne hukunci na farko a cikin hukunce-hukunce guda uku da kotun za ta yanke yayin zamanta na yau Laraba.

    Jam'iyyar APM ta shigar ƙarar a kan Bola Ahmed Tinubu da Hukumar Zaɓe ta INEC da kuma Kabiru Masari, mutumin da ɗan takarar APC a wancan lokaci ya fara gabatar wa INEC a matsayin wanda ke mara masa baya kafin ya sauya shi da Kashim Shettima.

    Kotun za ta yanke hukunci kan manyan jam'iyyun adawa na PDP da LP suka shigar gabanta suna kalubalantar nasarar Tinubun

  12. Abin da mutane ke cewa kan hukuncin kotun zaɓe a Najeriya

    Yayin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ke ci gaba da zamanta domin yanke hukunci a Najeriya, 'yan ƙasar dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan hukuncin da kotun za ta yanke.

    Jam'iyyun adawar ƙasar ne dai suka shigar da ƙarar suna ƙalubalantar nasarar da hukumar INEC ta ce Bola Tinubu na APC ya samu a zaɓen da aka gudanar cikin watan Fabrairu.

    Ga abin da wasu 'yan ƙasar ke cewa a shafukanmu na sada zumunta sada zumunta.

    Babawo Mato Mai'adua ya ce ''Mu dai muna jira mu ji yadda hukuncin zai kaya

    Shi kuwa Idris Shuaibu cewa ya yi "mun bar wa Allah zaɓi"

    A nasa ra'ayi Nasar Rabo cewa ya yi

  13. Masar na buƙatar rage haihuwa don kauce wa ƙalubalen rayuwa - Sisi

    Shugaban ƙasar Masar Abdul Fattah al-Sisi ya ce ƙasarsa na buƙatar rage yawan haihuwa domin kauce wa manyan matsalolin da ke tunkarar ƙasar.

    Shugaba Sisi ya ce ya kamata ƙasar ta taƙaita yawan haihuwa zuwa 400,000 a shekara, maimakon fiye da haihuwa miliyan biyu da ake samu a ƙasar kowace shekara, domin samun damar yi wa 'yan ƙasar ayyukan more rayuwa da samun ayyukan yi.

    Mista al-Sisi ya yi watsi da maganar da ministan lafiyar ƙasar ya yi, cewa samun 'ya'ya na daga cikin 'yancin ɗan'adam.

    "Wane 'yanci, bayan suna janyo wa mutane ƙarin wahala? a ƙarshe duka al'umma ne da ƙasarmu za su sha wahalar".

    "Ya kamata mu san yadda za mu yi da wannan 'yancin, in ba haka ba kuwa mu ƙirƙirar wa kawunanmu wahala".

    Ya ƙara da cewa Ƙasarsa za ta koikoyi China kan tsarin haihuwar ɗa ɗaya ga kowaɗanne ma'aurata, "tun da dai Chinan ta samu nasarar rage yawan al'ummarta".

    Daga shekarar 2000, yawan al'ummar Masar ya ƙaru da miliyan 40, inda a yanzu yawan al'ummar ƙasar ya kai miiyan 150, kamar yadda alƙaluman hukumomin ƙasar suka nuna.

    Mista al-Sisi ya kuma shawarci sauran ƙasashen Afirka su rungumi matakin rage yawan jama'a, kasancewar nahiyar na fama da ƙarancin abubuwan da jama'ar ke buƙata domin su rayu.

  14. Kotu ta kori ɗaya daga cikin ƙorafe-ƙorafen jam'iyyar APM a kan Tinubu

  15. Babbar kotun Faransa na nazarin dokar haramta sanya abaya a makarantu

    Babbar Kotu a Faransa na nazari kan ba da umarnin gaggawa da zai dakatar da haramci da gwamnatin ƙasar ta yi kan sanya abaya a makarantun ƙasar da aka yi wa Musulmi.

    Lauyoyin ƙungiyar Musulmi ta ƙasar na cewa wannan haramci ya saɓa ƙa'ida da tauye 'yancin addini.

    A rana ta farko da soma aikin wannan doka, an kori gwamman mata gida daga makarantu saboda sanya abaya da kin amincewa su sauya suturarsu.

    Shugaban ƙasar Emmanuel Macron ya ce bai kamata wajen neman ilimi ya nuna wani ɓangare na addini ba, ministoci na ganin akwai buƙatar wasu makarantu su gwada fito da tsarin sanya kayan makaranta.

    Mireille Clapot jami'ar jam'iyya mai mulki, ta kuma ce haramcin ya yi daidai da manufar ƙasar na kauce wa fifita addin

    "Wannan mataki ba shi da alama da wariya da nuna bambanci, kuma wannan na da nasaba da tunaninmu na cewa addini ba shi da alaƙa da tsarinmu kuma bai kamata ya riƙa shiga harkokin rayuwar mutane ba, musamman a fannin ilimi", in ji ta.

    Rigar abaya ta kasance suturar da ake samun ƙaruwar amfani da ita a makarantun Faransa, abin da ya riƙa haddasa rabuwar kawuna a siyasanse.

    Inda jam'iyyu masu tsatsauran ra'ayi ke tursasa batun haramci kan rigar, yayin da masu sassaucin ra'ayi ke nuna matukar damuwarsu kan 'yanci mata manya da kanana Musulmi

  16. Yajin aikin NLC ya shiga rana ta biyu

    Gamayyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta shiga rana ta biyu na yajin aikin gargaɗi da take yi a ƙasar.

    NLC ta shiga yajin aikin gargaɗin ne ranar Talata sakamakon cire tallafin man fetur, lamarin da ƙungiyar ta ce ya jefa 'yan ƙasar cikin matsin rayuwa.

    Tuni dai yajin aikin ya fara tasiri a wasu sassan ƙasar, inda aka samu rahotonnin ɗaukewar wutar lantarki a wasu sassan ƙasar, sakamakon yajin aikin.

    A wasu jihohin ƙasar da dama ma'aikata ba su fita wuraren aikinsu ba.

    Kungiyar dai ta nuna rashin amincewarta da matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

  17. An fara zaman a kotun ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa

    Kotun sauraraon ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya ta fara ɗaukar hamara gabanin yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen zaɓe da jam'iyyun adawa suka shigar gabanta.

    Jam'iyyun PDP da LP ne suka shigara da ƙara suna ƙalaubalantar nasarar da Bola Tinibu na APC ya samu a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar cikin watan Fabrairun wanna shekara.

    Tuni wakilan jam'iyyu suka fara isa kotun domin sauraraon hukuncin da kotun za ta sanar.

    Daga ɓangaren wadanda ake ƙara tuni mataimakin shugaban ƙasar Sanata kashim Shettima da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da gwamnan Yobe Mai Mala Buni da gwamnan Kogi Yahaya Bello.

    Sai gwamnan Nasarawa Abdullahi A Sule da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Malam Nuhu Ridadu da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila da wasu kusoshin jam'iyya mai mulki suka isa kotun.

    A ɓangaren jam'iyyar adawa tuni shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa Amb. Umar Illiya Damagun da gwamnan Bauchi sanata Bala Muhammad na PDP da wasu manyan kusoshin jam'iyyar suka hallara.

    A ɓangaren jam'iyyar LP mai magana da yawun jam'iyyar Dakta Yunusa Tanko shi ma ya hallara a harabar kotu.

    Ana sa ran 'yan takarar jam'iyyun adawa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na jam'iyyar LP za su halarci zaman ktoun don jin irin hukuncin da kotun za ta yanke.

    Bayan kammala zaɓen shugabna ƙasar ne dai jam'iyyun adawar suka shigar da ƙarar suna ƙalubalantar nasarar da hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ce Bola Tnubu na APC ya samu.

    Kotun wadda ke zamanta a Abuja, za ta sanar da hukunci kan ƙararrakin da wasu 'yan takara a zaɓen 25 ga watan Fabrairun 2023, suka shigar gabanta.

    Atiku Abubakar, jagoran adawa a Najeriya, da Mista Peter Obi, ɗan takarar da ya zo na uku da kuma jam'iyyar APM, duka suna ja da kan sakamakon da ya bai wa Bola Tinubu nasara a zaɓen.

  18. Gwamnatin Brazil za ta taimaka wa waɗanda guguwa ta yi wa ɓarna

    Shugaban Brazil ya ce gwamnati za ta taimaka wa jihar Rio Grande do sul inda sama da mutane 20 suka rasa rayukansu sakamakon tsawa mai karfi.

    Guguwa mai ƙarfi da ruwan sama sun sanya dubban mutane tserewa daga muhallansu.

    Da dama daga cikin waɗanda suka mutu mazauna garin Macuum ne.

    Magajin garin yace akwai fargabar samun ƙaruwar waɗanda suka mutu sakamakon wannan bala'i da ya afka wa yankin.

  19. Sallama

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da safiyar ranar Laraba.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku labaran abu buwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.