Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai gana da shugabannin wasu ƙasashe a gefen taron ƙungiyar G20 ta ƙasashe 20 mafiya girman tattalin arziƙi da za a yi a Indiya a watan Satumba.
Duk da cewa Najeriya ba ta cikin G20, maƙasudin tafiyar shi ne jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen zuwa Najeriya, wadda ita ce mafi ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, kamar yadda mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya bayyana.
Tinubu zai gana da shugabannin Brazil da Indiya da Koriya ta Kudu da Jamus a gefen taron da za a fara daga 9 zuwa 10 na watan Satumba.
Kazalika, Tinubu zai gana da wasu manyan 'yan kasuwa na Indiya.
Kamfanin sadarwa na Airtel, wanda kamfanin Indiya Bharti Airtel ya mallaka, shi ne na uku mafi girma a Najeriya, a cewar rahoton kamfanin labarai na Reuters.
Ministan kuɗin ƙasar ya faɗa a ranar Litinin cewa gwamnatin Bola Tinubu na neman hanyoyin ƙarfafa zuba jari fiye da dogaro kan bashi don samun damar ƙirƙirar ayyukan yi ga miliyoyin matasa.