Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

MNJTF ta miƙa tubabbun 'yan Boko Haram 46 ga ƙasar Chadi

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Jami'an Custom sun kama wasu kayayyaki da aka yi fasa ƙwaurinsu zuwa Najeriya

    Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya reshen jihar Kebbi ta ce ta samu nasarar ƙwace wasu abubuwa da aka yi fasa ƙwaurinsu zuwa ƙasar na miliyoyin kuɗi.

    Baban kwantirolan hukumar mai lura da jihar, Ben Oramaluga ne ya bayyana haka ranar Asabar a lokacin taron manema labarai a birnin Kebbi.

    Ya ce jami'an hukumar sun kama ƙullin tabar wiwi 371, da ƙwayar 'diazepam' kwali 98.

    Mista Oramaluga ya ƙara da cewa sun kuma kama fatar jakuna 1080, da buhu 37 na shinkafar waje, da dilar kwanjo 16, da man fetur kimanin lita 30 da wata ƙaramar mota kirar Toyota Corolla.

    Babban kwantirolan jihar ya ce ƙwayar da suka ƙwace an ƙiyasta kuɗinta ya kai sama da miliyan 90.

    Ya ƙara da cewa jami'ansa sun kuma kama wani mutum da suke zargi da hannu a shigar da tabar zuwa ƙasar, inda ya ce za su miƙa shi da ƙwayoyin hannun hukumar NDLEA mai yaƙi da sha da safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

  2. Masu zanga-zanga sun yi zaman dirshan a fadar gwamnatin Chile

    Rahotanni daga Chile sun ce ɗaruruwan masu zanga-zangar adawa da gwamnati sun yi zaman dishan a harabar fadar shugaban kasar dake Santiago babban birnin kasar.

    Mas zanga-zangar sun taru ne domin bayyana takaicinsu game da yawaitar cin hanci a cikin gwamnati.

    Sun kuma nemi shugaban ƙasar Gabriel Boric mai sassaucin ra'ayi ya yi murabus, bayan wasu masu goyon bayan gwamnati sun shiga zanga-zangar.

    A farkon wannan watan ne wani minista ya yi murabus bayan zargin 'yan jam'iyyarsa da hannu a musayar kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba

  3. Mnangagwa ya lashe zaɓen Zimbabwe

    Hukumar zaben Zimbabwe ta ayyana shugaba Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar da kashi 53 na ƙuri'un da aka kaƙa.

    Mnangagwa ya doke babban abokin hamayyarsa Nelson Chimasa wanda ya samu kashi 44 na ƙuri'un.

    Masu sanya idanu daga EU a zaɓen sun ce an yi amfani da rikici da razanarwa wajen tsoratar da masu zaɓe.

    Babbar jam'iyyar adawa ta ki sanya hannu a kan takardar sakamakon zaben, sannan ta kaurace wa wajen da aka bayyana sakamakon zaben.

    Tun da farko kafofin yada labaran ƙasar sun ruwaito cewa jam'iyyar Mista Mnangagwa ta samu nasarar lashe kashi biyu cikin uku na kujerun majalisar dokokin kasar.

    Shugaban ƙasar zai fuskanci sabbin matsalolin da suka dabaibaye ƙasar ciki har da hauhawar farashi da rashin aikin yi da kuma cin hanci

  4. Maraba lale

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da hutun karshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo halin da duniya ke ciki, musamman Najeriya da makwabtan kasashe.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmy na sada zumunta.

    Mu je zuwa....