Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
MNJTF ta miƙa tubabbun 'yan Boko Haram 46 ga ƙasar Chadi
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Mu kwana lafiya
Nan muka kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafi ba don labarai sun ƙare ba - kun san dai jiki da jini.
Amma za mu kawo muku wasu sababbi da suka shafi rayuwarku kai-tsaye a wani shafin daban a gobe, tun daga farar safiya zuwa darenta.
Umar Mikail ne yanzu ke cewa mu zama lafiya.
Babu dokar da ta ce sai na gama NYSC za a naɗa ni minista - Hannatu Musawa
Ministar Al'adu ta Najeriya Hannatu Musawa ta musanta zargin da ake yi mata na karya dokar ƙasa bayan naɗa ta a muƙamin duk da cewa ba ta kammala hidimar ƙasa ta NYSC ba.
Cikin wani martani da ta fitar a yau Lahadi, ministar 'yar jihar Katsina a arewacin Najeriya ta ce "babu wata doka da na karya".
"Dole ne na faɗa cewa babu wata doka a Najeriya da ta ce shugaban ƙasa ko wata hukuma ba za su iya naɗa mutumin da yake hidimar ƙasa a muƙami na siyasa ba," in ji ta.
Sai dai, mai magana da yawun hukumar National Youth Service Commission (NYSC), Eddy Megwa, ya faɗa wa Daily Trust cewa "ta karya doka kuma muna duba yiwuwar ɗaukar matakin da ya dace" a kanta.
A ranar Litinin 21 ga watan Agusta Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Hannatu - wadda yanzu haka take gudanar da hidimar ƙasar a Abuja - a matsayin minista tare da sauran mutum 45.
Hannatu ta tabbatar da cewa tun a 2001 aka tura ta hidimar ƙasar zuwa jihar Akwa Ibom amma ta ɗage aiwatarwa sai a 2023 ta ci gaba.
Ɗan adawar Zimbabwe ya yi iƙirarin cin zaɓe duk da nasarar Mnangagwa
Mutumin da ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasar Zimbabwe, Nelson Chamisa, ya yi iƙirarin cin zaɓe duk da sanar da shugaba mai-ci Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya yi nasara.
Wakilin BBC a birnin Harare, Shingai Nyoka, ya ce ba abin mamaki ba ne yadda zaɓen ya ƙare da cece-kuce.
Nelson Chamisa na jam'iyyar adawa ta Citizens Coalition for Change ya samu kashi 44 na ƙuri'un da aka kaɗa, kuma ya zargi hukumar zaɓen ƙasar da sanar da sakamakon boge - ba tare da bayar da wata hujja ba.
Su ma masu sa ido na ƙasashen waje sun soki nagartar zaɓen.
A gefe guda kuma, jam'iyya mai mulki ta Zanu PF ta shawarci 'yan adawar su nufi kotu, yayin da doka ta bai wa Mista Chamisa mako ɗaya don yin hakan. Amma bai bayyana ko jam'iyyarsa za ta yi hakan ba.
Yadda Musulmi suka adana kwafin Al-ƙur'ani mafi daɗewa a Afirka ta Kudu
Taliban ta hana mata shiga wurin shaƙatawa na Band-e-Amir a Afghanistan
Gwamnatin Taliban mai mulkin Afghanistan ta haramta wa mata zuwa wurin shaƙatawa na Band-e-Amir da ke lardin Bamiyan.
Ministan tarbiyya da ɗa'a na Afghanistan, Mohammad Khaled Hanafi, ya ce matan ba su son saka hijabi a wurin shaƙatawar.
Ya yi kira ga malamai da kuma 'yan Hisbar ƙasar su hana matan shiga har sai an cimma wata matsaya.
Band-e-Amir wuri ne da iayalai da yawa kan je kuma hana mata shiga zai sa da yawa su daina zuwa don shaƙatawa.
Hukumar kula da wuraren tarihi ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta siffanta shi da "wurin da Allah ya ƙirƙira da siffa ta musamman cike da ƙoramu da kuma ƙayatarwa".
Barcelona ta doke Villareal a nasararta ta biyu a La Liga
An bai wa Van Dijk jan kati a karon farko a Liverpool
Harin masu iƙirarin jihadi ya kashe yarinya a Mali
Wani hari da ake zargin mayaƙa masu iƙirarin jihadi da kaiwa ya kashe yarinya tare da raunata wasu mutum huɗu a birnin Timbuktu da ke Mali ranar Asabar.
Mai magana da yawun rundunar sojin Mali ya ce "da misalin ƙarfe 5:30 na yamma 'yan ta'adda...suka hari Timbuktu da makamin da ya faɗo kusa da kasauwa".
Fararen hula huɗu aka kai asibiti, yayin da wani jami'in gwamnati a yankin ya faɗa wa kamfanin labarai na AFP cewa "harin da 'yan ta'addan suka kai ya faɗa a tsakiyar birnin na Timbuktu" kuma ya kashe yarinya mai shekara 11.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka jikkata ɗin yarinya ce 'yar shekara huɗu, a cewar jami'in gwamnatin.
A ranar Litinin jami'an gwamnatin yankin suka faɗa wa AFP cewa mayaƙan sun yi wa garin ƙawanya tsawon kwanaki.
Hare-haren ƙungiyoyin masu alaƙa da al-Ƙaeda na ƙaruwa a Timbuktu yayin da dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya ke shirin ficewa daga ƙasar bayan shekara 10.
Masar da Habasha na ci gaba da tattaunawa kan hatsaniyar Kogin Nilu
Ƙasashen Habasha da Masar sun ce sun ci gaba da zaman tattaunawa a birnin Alƙahira domin kawo ƙarshen hatsaniyar da ta taso game da gina madatsar ruwa a Kogin Nilu.
Masar da Sudan da ke gefen kogin sun daɗe suna adawa da yunƙurin Habasha na gina tashar lantarki kan dala biliyan biyar saboda barazana ce ga ruwan sha a ƙasashen nasu.
Wakilan Masar da Habasha da Sudan sun hallara a Ƙahira ne don cimma yarjejeniyar da za ta ba su damar rarraba ruwan kogin a tsakaninsu.
Gina madatsar ruwan a kudancin Habasha ya fara ne fiye da shekara 10 da suka wuce.
A shekarar da ta gabata ta fara ba da wutar lantarki kuma ana ci gaba da cika madatsar, abin da ke harzuƙa Masar da Sudan ke nan.
Kusan dukkan ruwan da Masar ke amfani da shi daga Nilu yake zuwa, shi ya sa take kallon madatsar a matsayin babbar barazana.
Habasha na cewa aikin na da muhimmanci wajen samar wa miliyoyin 'yan ƙasar wutar lantarki da kuma rage talauci.
Sojojin Amurka sun mutu a hatsarin jirgi
Sojojin Amurka uku sun mutu sannan wasu 20 suka jikkata sakamakon hatsarin da jirgin helikwaftansu ya yi a Australiya yayin atasaye.
Jirgin MV-22B ya rikito ne a kan hanyarsa ta zuwa tsibirin Tiwi da ke arewacin Darwin. An ce biyar daga cikin sojojin sun ji jiki sosai.
Suna tsaka da gudanar da atasaye ne tare da wasu dakaru 2,500 daga Amurka, da Australiya, da Philippines, da East Timor, da kuma Indonesiya.
Sojojin Amurka ne kaɗai a cikin jirgin.
Man City ta lashe dukkan wasa uku da fara Premier League ta bana
Bellingham ne kan gaba a cin kwallaye a La Liga a 2023/24
MNJTF ta miƙa tubabbun 'yan Boko Haram 46 ga ƙasar Chadi
Rundunar dakarun ƙasashen da ke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram ta MNJTF ta samu nasarar karɓar tubabbun mayaƙan ƙungiyar su 46 tare da hannunta su ga hukumomin Chadi.
Babban kwamandan rundunar shiyya ta biyu Manjo Janar Djouma Youssouf Mahamat Itno, ne ya jagoranci miƙa tubabbn mayaƙan ga ƙasar Chadi.
An miƙa tsoffin mayaƙan ne a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar a Bagasola na ƙasar Chadi.
Ministan ayyukan gwamnatin ƙasar da kyautata zamantakewa na ƙasar Abdoulaye Mbodou Mbami ya ƙarbi tsofinmayaƙa a madadin gamnatin ƙasar.
Yayin da yake jawabi Manjo Janar Itno ya yi kira ga sauran mayaƙan ƙungiyar da su bi sahun waɗanda suka tuban, tare da ajiye makamansu, don rungumar zaman lafiya.
Wannan wani ɓangaren na yunƙurin rundunar MNJTF da hukumomin ƙasashen da ke fama da matsalar Boko Haram, na ganin cewa mayaƙan ƙungiyar sun ajiye makamai tare da komawa cikin al'umma domin ci gaba da rayuwa.
Kungiyar Boko Haram dai ta shafe shekaru masu yawa tana kai hare-hare a ƙasashen yankin tafkin Chadi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, tare da raba miliyoyi da muhallansu.
Jam'iyyar adawa ta yi watsi da sakamakon zaɓen Zimbabwe
Babban ɗan takarar jam'iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasar Zimbabwe ya yi watsi da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar, inda ya bayyana zaɓen da cewa 'tsantsar maguɗi' ne.
Cikin wani saƙo da Nelson Chamisa ya aike wa magoya bayansa a shafinsa na sada zumunta, ya ce an yi musu fashin muryoyi da ƙuri'unsu.
A ranar Asabar ne hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana shugaban ƙasar Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe zaɓe da kusan kashi 53 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.
An zargi Jam'iyyarsa ta ZANU PF - wadda ke jan ragamar ƙasar tun lokacin da ta samu 'yancin kai a shekarar 1980 - da yin amfani da 'yan sanda da kotuna wajen rage wa 'yan adawa ƙarfi a lokacin yaƙin neman zaɓe.
An kuma zargi Jam'iyyar da kwashe shekaru tana amfani da dabaru, ciki har da tashin hankali domin taimaka wa Robert Mugabe ci gaba da kankanewa kan mulki, har ma zuwa lokacin da 'yan ƙasar suka buƙaci ya sauka daga mulki.
Masu sanya idanu na ƙasashen waje a zaɓen sun yi ta sukar yadda aka gudanar da zaɓen.
Abin jira a gani shi ne ko jam'iyyar adawar na da ƙwarararn hujjojin tafka maguɗi a zaɓen.
Amsoshin Takardunku
Shugaban Amurka ya buƙaci ganawa da Tinubu
Shugaban Amurka Joe Biden ya aike da gayyata ga shugaban Najeriya Bola Tinubu domin gudanar da wata tattaunawa tsakaninsu.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale, ya fitar ya ce jakadan shugaban Amurka na musamman, kuma mataimakin sakataren harkokin wajen ƙasar, Ambasada Molly Phee, ne ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci shugaba Tinubu a fadarsa.
Mista Phee ya shaida wa Tinubu cewa shugaban Amurka Joe Biden na buƙatar ganawa ta musamman da shi, a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a birnin New York cikin watan Satumba.
Jakadan na Amurka ya ce Tinubu ne kaɗai shugaban Afirka da shugaban Amurka ya karrama da gayyatar ganawa da shi.
Ya ƙara da cewa “Mun san akwai hanyoyin da za mu bi domin ƙarfafa zuba jarin Amurka a Najeriya, kuma muna son yin aiki kafaɗa-da-ƙafaɗa da kai domin cimma hakan, a wani ɓangare na inganta tattalin arzikin Najeriya da ma na Afirka".
“Muna yabawa da irin ƙoƙarin da kake yi wajen samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari. Kan haka ne shugaba Joe Biden ke buƙatar ganawa da kai a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, kuma kai kaɗai ne shugaban da ya buƙaci ganawa da kai daga Afirka. Wannan kuma alama ce da ke nuna cewa ya yarda da nagartar shugabancinka," in ji jakandan na Amurka.
Labarai da dumi-dumi, 'Gwajin ƙwayar halitta ya tabbatar da mutuwar Prigozhin'
Jami'an Rasha sun ce an tabbatar da mutuwar shugaban kamfanin sojojin hayar Rasha na Wagner, Yevgeny Prigozhin bayan da aka yi wa gawarwakin mutanen da ke cikin jirgin gwajin ƙwayoyin halitta
Tawagar masu binciken sun ce gwajin da suka yi wa gawarwaki 10 da ke cikin jirgin, ya yi dai dai da na sunayen fasinjojin ke cikin jirgin.
A ranar 25 ga watan Agusta ne jirgin Prigozhin ya faɗi a arewa maso yammacin birnin Moscow, tare da kashe duka mutanen da ke cikinsa.
Gwamnatin Rasha ta musanta raɗe-raɗe radin da ake yaɗawa cewa tana da hannu a faɗuwar jirgin.
Cikin watan Yuni ne Mista Prigozhin ya jagoranci wani boren soji da bai yi nasara ba, ga gwamnatin shugaba Putin na Rasha
- Putin ya miƙa ta'aziyya kan mutuwar shugaban Wagner
- Shin juyin mulki Wagner ke yunƙurin yi wa Putin?
Najeriya na asarar gangar mai 400,000 a kowacce rana - Ribadu
Babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya ce ƙasar na asarar gangar danyen mai 400,000 a kowacce rana sakamakon ayyukan ɓarayin man na ciki da wajen ƙasar, duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kawar da matsalar ɓarayin man.
Ribadu ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar da shugaban ƙasa ya aike zuwa duba wasu wurare na man fetur da iskar gas a jihar Rivers mai arzikin man fetur.
Ya ce ayyukan masu satar ɗanyen mai da ke fasa bututan mai na kawo wa ƙasar babban naƙasu ta fuskar tatalin arziki, lamarin da ya ce shi ke haifar da tsadar rayuwa a ƙasar.
“Abin takaici ne yadda wasu tsirarun mutane ke sace albarkatun ƙasarmu domin amfanar da kawunansu, abin da kuma ke haifar da asara mai yawa ga ƙasarmu da mutanen yankin".
Ya ƙara da cewa “Najeriya na da arzikin man da za ta iya haƙo gangar mai miliyan biyu a kowacce rana, amma yanzu ƙasa da ganga miliyan 1.6 kawai muke iya haƙowa, sakamakon ayyukan ɓarayin mai da masu fasa bututan man".
“Kenan kusan gangar mai 400,000 wasu ɓata-gari da masu yi wa tattalin arzikinmu zagon-ƙasa ke sacewa a kowacce rana domin amfanar da kansu", in ji Ribadu.
Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkar taro ya ce darajar gangar mai 400,000 a yanzu ta kai dala miliya hudu, "kenan waɗannan kuɗaɗe muke asara a kowacce rana sakamakon ayyukan waɗannan ɓata-garin".
"Idan ka lissafa dala miliyan huɗu sau kwanakin shekara 365, za ka ga cewa maƙudan biliyoyin daloli muke asara a ƙowacce shekara"".
Kuɗin da ya ce sun isa ƙasar inganta tattalin arzikinta ta hanyar farfaɗo da darajar ƙudin ƙasar, da rage tsadar rayuwa da sauran fannoni.
Ribadu ya ƙara da cewa gwamnatin shugaban Tinubu na damuwa da wannan mummunar ɗabi'a, ya kuma ce gwamnatin ta fara ɗaukar matakai don kawo ƙarshen wannan matsala.
Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu
Shirin Taɓa Karatu Taɓa Karatu tare da Haruna Tangaza da Umayma Sani Abdulmumin