Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Buhari ya jajanta wa iyalan sojojin da aka kashe a Neja

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Wutar daji: Hukumomi a Kanada sun umarci mazauna Kelwona su gudu

    A yayin da Kanada ke ci gaba da fuskantar wutar daji mafi muni a duniya, an ƙaddamar da dokar ta-ɓaci a birnin Kelwona da ke kudancin British Colombia.

    Birnin mai mutum 150,000 na fuskantar barazanar gobara daga ɓangaren yammaci mai makwabtaka, wanda ke cikin barazanar wutar tun kwana biyu da suka wuce.

    Wakilin BBC ya ce mahukunta sun umarci kowa ya bar inda yake saboda irin haɗarin da wutar ke da shi wadda ake gani za ta iya kai wa ga birnin cikin sa'oi.

    Iska mai karfi da ke kadawa na ƙara rura wutar.

    Wani jami'in kashe gobara ya ce yadda suke kashe wutar kamar suna kashe wutar da ta yi shekara 100 tana ci.

  2. Assalamu Alaikum

    Ma'abota BBC Hausa barkanmu da hantsin Asabar, sannu da shigowa shafin labarai kai-tsaye.

    Umar Mikail ne zai kasance da ku don kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Ku biyo mu.