Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Buhari ya jajanta wa iyalan sojojin da aka kashe a Neja

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu binmu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshe labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Abdullahi Dello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. An yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu tayar da ƙayar-baya a Somaliya

    An yi arangama tsakanin jami'an 'yan sanda da wasu masu tayar da ƙayar baya a Mogadishu babban birnin Somaliya

    Rikicin ya ɓalle ne a ranar Juma`a bayan yan sanda suka yi yunƙurin kama wasu 'yan bindiga da aka zarga da kai hare-hare da sace kayan mutane.

    An kwashe sama da sa`o`i goma ana harbe-harben bindiga, kakakin yan sanda ya bayyana cewar sun yi nasarar kama shugaban masu ta da kayar bayan tare da 10 daga cikin mayaƙansa.

    Shugaban ƙasar Hassan Sheikh Mohamud ya marci jami`an tsaro su jajirce wajen inganta tsaro a babban birnin ƙasar

  3. Hari da ake zargin Falasdinawa da kai wa ya kashe mutum biyu

    Wani Uba da dansa sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da ake zargin Falasdinawa sun kaddamar a gabar yammacin kogin Jordan.Rahotanni sun kara da cewar, dan bindiga ya harbi fararen hular a wurin wankin motoci dake garin Huwara a kudancin Nablus.Kungiyoyin Hamas da IS sun yaba da harin da aka kai, jim kadan bayan sojojin Isra`ila sun sanya shinge a hanyoyin da suke kusa da inda al`amarin ya faru.A watan Fabrairun bana wani mummunan hari ya sanya mazauna Isra`ila sun banka wa yankunan Falasdinawa wuta, lamarin da ya haifar da mutuwar wani Bafalasdine daya bayan an kone gidaje da motoci da dama

  4. Tawagar Ecowas ta gana da Bazoum

    Tawagar Ecowas ta musamman da ta ziyarci Nijar ta samu ganawa da shugabannin mulkin sojin ƙasar a wani yunƙuri na maido da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan karagar mulkin ƙasar.

    Tawagar masu shiga tsakanin - ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya janar Abdulsalamu Abubakar mai ritaya da mai Alfarma sarkin Musulmin Najeriya Muhammad sa'adu Abubakar lll - ta samu ganawa da shugaban mulkin sojin kasar Janar Abdourahamane Tchiani.

    Tawagar ta Ecowas ta kuma samu ganawa da hamɓararren shugaban ƙasar mohamed Bazoum.

    Ziyarar masu shiga tsakanin na zuwa ne kwana guda bayan da manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas suka ce sun saka ranar afka wa Nijar da yaƙi, matsawar sojojin ba su mayar da bazoum kan mulki ba.

    Sojojin mulkin sun tattauna da tawagar Ecowas ɗin a birnin Yamai, to sai dai ba su yi bayani abubuwan da suka tattauna ba.

    Tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ɗaukar dubban 'yan sa kai domin kare ƙasar daga farmakin Ecowas.

  5. Brighton ta ci kwallo takwas a wasa biyu a Premier ta bana

  6. An fara ɗaukar masu aikin sa-kai a Nijar

    Daruruwan matasa ne suka taru a birnin Yamai domin ɗaukarsu aikin sa-kai a Nijar, a wani yunƙuri na kare ƙasar daga farmakin Ecowas.

    Rahotonni na cewa an shirya ɗaukar matasan aikin ne domin mayar da martani idan ƙungiyar Ecowas ta kai wa ƙasar farmaki.

    Ana gudanar da aikin ne a wani ɓoyayyen wuri a Yamai babban birnin ƙasar, to sai dai an hana 'yan jarida zuwa inda ake aikin ɗaukar 'yan sa kan.

    Ba a dai sani ba ko sojojin da suka yi juyin mulkin na sane da aikin ɗaukar 'yan sa-kan.

    Rahotonni da ke fitowa daga ƙasar sun ce, ana sa ran ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar-baya a ƙasar za su tallafa wa sojojin da magunguna da kayan aiki sauran dabaru idan Ecowas ta ƙaddamar da yaƙi a ƙasar.

    A ƙarshen taron hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas da aka gudanar da Ghana ne aka amince da saka ranar far wa Nijar da yaƙi.

    To sai dai ƙungiyar ba ta bayyana takammiyar rana ba, amma ta ce dakarunta a shirye suke domin fara kai farmaki.

    • Ecowas ta ce hafsoshin sojinta sun sa ranar shiga Nijar
    • Ƙasashen da Ecowas ta yi nasarar mai da mulkin dimokraɗiyya
  7. Lafiya Zinariya

  8. Zulum ya bai wa sojojin da suka jikkata a Borno naira miliyan 10

    Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayar da tallafin naira miliyan 10 ga sojojin da suka jikkata sakamakon yaƙi da Boko Haram da suke yi a jihar.

    Cikin wani saƙo da gwamnan ya wallafa shafinsa na X da a baya aka fi sani da Twitter, ya ce tallafin na daga cikin alƙawarin da ya ɗauka, wata biyu da suka gabata a lokacin da babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya kai ziyara jihar.

    Babban hafsan sojin ƙasan dai ya je jihar ne domin gudanar da bukukuwan babbar sallar tare da dakarun ƙasar da ke fagen daga a jihar ta Bornon.

    Kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida Farfesa Usman A Tar tare da babban sakataren gidan gwamnatin jihar Barrister Mustapha Ali Busuguma ne suka miƙa kuɗin ga babban kwamandan runduna ta bakwai da ke Maiduguri, Manjo Janar Peter Malla ranar Asabar.

    Sojojin Najeriya da dama ne suka mutu a rikicin Boko Haram da aka ƙwashe fiye da shekara 10 ana yi a yankin arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihohin Borno da Yobe da wasu yankunan jihar Adamawa.

    Lamarin da yayin sanadiyyar mutuwar dubban fararen hula da raba miliyoyi da muhallansu.

  9. Gane Mini Hanya: Kan makon shayar da jariri nonon uwa

    Masana na cewa babban abin da ke taimaka wa jariri daga haihuwa har zuwa kasancewarsa cikakken mutum shi ne wadataccen nonon uwa.

    A kan samu yanayin da likitoci kan alaanta cutuka da ke shiga jikin mutum sakamakon rashin garkuwa mai kyau wadda kuma ke samo asali saboda karancin nonon uwa a jikin yaro.

    Hukumar Lafiya ta Duniya dai ta sanya watan nan na Agusta domin ya zamo lokacin nuna muhimmancin nonon uwa ga jariri.

    Kuma a kan haka ne Aisha Salisu Babangida ta tattauna da Dr Mariya Mukhtar Yola, kwararriyar likitar yara a babban asibitin Abuja.

  10. Buhari ya jajanta wa iyalan sojojin Najeriya da aka kashe a Neja

    Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa kan mutuwar sojojin ƙasar da aka kashe a wani ƙwanton-ɓauna da 'yan bindiga suka yi musu tare da faɗuwar wani jirgin helikofta na soji a jihar Neja.

    Cikin wani saƙon Twitter da tsohon shugaban ƙasar ya wallafa ya ce ya kaɗu da hatsarin jirgin helikoftan, bayan da kuma aka yi wa waso sojojin ƙaar kwanton-ɓauna.

    “Ina miƙa soƙon jaje ga iyalan mamatan. ina kuma yi wa waɗanda suka jikkata addaua'r fatan samun lafiya''.

    Buhari ya kuma aike da saƙon ta'aziyyarsa ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da rundunar sojin ƙasar.

    A ranar Alhamis ne shalkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojojinta 36 a wani ƙwanton-ɓauna da aka yi musu a yankin Zungeru na jihar Neja, da faɗuwar jirgin helikofta da ya ƙwaso gawarwakin sojojin da marasa lafiyar ranar Litinin da ta gabata.

  11. Yadda direbobin motocin kaya suka yi sansani a iyakar Benin da Nijar cikin hotunan Afirka

  12. Sabuwar jakadiyar Amurka ta isa Nijar

    Sabuwar jakadar Amurka a Nijar, Kathleen Fitzgibbons, ta isa birnin Yamai a yau Asabar amma ba za ta gabatar da takardun aikinta ba "saboda halin siysar da ake ciki," a cewar Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.

    Zuwan Fitzgibbons "bai sauya matsayarmu ba, ya zama dole ne kawai saboda a samu babban jami'i a ofishin jakadancinmu a wannan lokaci mai sarƙaƙiya," kamar yadda kakakin ma'ikatar Matthew Miller ya bayyana cikin wata sanarwa.

    Amurka na ci gaba da neman hanyoyin difilomasiyya don sasanta rikicin siyasar da ya ɓarke tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli kuma suka tsare shi.

    Sanarwar ta ƙara da cewa: "Abin da Fitzgibbons za ta mayar da hankali a kai shi ne lalubo hanyoyin sasanta rikicin ta hanyar lumana da kuma sakin Bazoum da iyalansa nan take, da kuma waɗanda aka tsare ba bisa doka ba."

  13. Tawagar Ecowas ta gana da Bazoum da Tchiani

  14. Labarai da dumi-dumi, Tawagar Ecowas ta sauka a Yamai

    Tawagar da Ecowas ta tura don sasanta rikicin siyasar Nijar ta isa Yamai, babban birnin ƙasar a yau Asabar.

    Tawagar ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Abdulsalami Abubakar, ta samu tarba daga Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, wanda sojoji suka naɗa.

    Ana sa ran za su tattauna da jagoran mulkin sojan, Janar Abdourahmane Tchiani, game da yadda za a mayar da mulki ga farar hula.

    Ecowas na son sojojin su mayar da Mohamed Bazoum kan mulki, wanda suke tsare da shi tun 25 ga watan Yuli.

  15. Za mu nemi ƙasar da za mu kai dakarunmu idan muka fice daga Nijar - Amurka

    Kwamandan dakarun Amurka a Turai da Afirka ya ce sun fara shirin ɗaukar matakai idan aka nemi su fice daga Nijar ciki har da neman ƙasar da za su mayar da su a yammacin Afirka, kamar yadda kafofin labaran Amurka suka ruwaito.

    "Za mu kasance cikin shiri idan wani abu ya faru," a cewar Janar James Hecker yayin tattaunawarsa da manema labarai ta intanet a ranar Juma'a.

    "Akwai matakai da za mu iya ɗauka da yawa idan za mu fice [daga Nijar]. Dole ne dai mu zama a shirye don ɗaukar dukkan matakan...amma muna fatan ba za ta kai ga haka ba.

    "Dole za mu duba wasu ƙasashen da za mu yi ƙawance da su a [yammacin] Afirka da za mu mayar da kayan aikinmu can."

    Amurka na da dakaru aƙalla 1,000 a Nijar da ke aikin yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel, kuma har yanzu ba ta ayyana kifar da gwamnatin Bazoum a matsayin juyin mulki ba.

    Da zarar Amurka ta ayyana lamarin a matsayin juyin mulki, hakan zai shafi alaƙarta da Nijar kai-tsaye, abin da ka iya kawo ƙarshen tallafin da take bai wa ƙasar da kuma zaman dakarun nata a can.

  16. 'Yan Nijar mazauna Kano sun yi zanga-zangar goyon bayan Ecowas

  17. Al-Qaeda ta yi iƙirarin kashe sojojin Nijar 17

    Reshen yankin Sahel na ƙungiyar al-Qaeda ya yi iƙirarin ɗaukar alhakin kashe sojojin Nijar 17 cikin wani hari da 'yan bindigar masu iƙirarin jihadi suka kai a yankin Tillaberi.

    Ƙungiyar Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) ta ɗauki alhakin cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Telegram ranar 17 ga watan Agusta.

    Ta ce maharan sun yi wa sojojin kwanton-ɓauna tsakanin garuruwan Boni da Torodi da ke kusa da iyakar Nijar da Burkina Faso a ranar Talata da ta wuce.

    Ƙungiyar ta wallafa hotuna huɗu na motoci da makamai da suka sace bayan harin.

    Rundunar sojin Nijar ta ce sojojin 17 aka kashe tare da raunata wasu 20, tana mai cewa ta kashe 100 daga cikin maharan yayin da suke ƙoƙarin guduwa.

    Sanarwar ta JNIM na zuwa ne yayin da ƙungiyar Ecowas ke cewa tana shirin tura dakarun soja Nijar ɗin don tilasta wa sojojin mulkin ƙasar dawo da mulkin farar hula bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yuli.

    • An kashe sojojin Nijar 45 a hare-haren 'yan bindiga tun bayan juyin mulki
  18. Mali da Burkina Faso sun aika wa Nijar jiragen yaƙi - Sojin Nijar

    Ƙasashen Mali da Burkina Faso sun aika wa Nijar jiragen yaƙi ɗai-ɗai don nuna goyon bayansu ga sojojin mulkin ƙasar da suka yi juyin mulki a watan Yuli.

    Wani rahoto da kafar talabijin ɗin RTN ta gwamnatin ƙasar ta yaɗa ranar Juma'a ya ce ƙasashen biyu sun fara cika alƙawarin da suka ɗauka na taimaka wa Nijar kare kanta daga harin da Ecowas ke shirin kai mata don dawo da mulkin farar hula.

    "Mali da Burkina Faso sun fara ɗaukar matakan cika alƙawari ta hanyar aiko da jirage don kare duk wani hari a kan Nijar," in ji rahoton.

    An bayyana cewa jiragen na kai hari ne ƙirar Super Tucano.

    A jiya Juma'a hafsoshin tsaro na ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma wato Ecowas suka ce sun saka ranar da za su afka wa Nijar don mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.

    Sai dai sun ce ba za su faɗi ranar ba, kuma za a ci gaba da yunƙurin shawo kan lamarin ta hanyar difilomasiyya.

    • Ecowas ta ce hafsoshin sojinta sun sa ranar shiga Nijar
    • Abin da ake nufi da matakin amfani da ƙarfin sojan Ecowas
  19. Amurka za ta ƙarfafa ayyukan soji da ƙasashen Koriya da Japan

    Shugaban Amurka Joe Biden da shugabannin kasashen Koriya ta Kudu da Japan sun amince da ƙarfafa harkokin soji da kuma hada kai don bunkasa tattalin arzikinsu.

    Sun cimma hakan ne a wajen taron da aka yi a Camp David da ke wajen Amurka ranar Juma'a.

    An yi taron da nufin shawo kan ƙaruwar karfin China da kuma barazanar makaman nukiliya daga Koriya ta Arewa.

    A taron za a taɓo batun samar da hanyoyi uku ƙwarara da za a yi amfani da su wajen shawo kan waɗannan matsaloli.

    Cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kasashen uku sun zargi China da aikata wasu abubuwa marasa kyau a tekun kudancin ƙasarta.

    Taron mai matukar tarihi, an yi shi ne da zimmar haɗa kan Koriya ta Kudu da Japan wadanda dangantakarsu ta yi tsami tsawon shekaru.

  20. Mun harbo jirage 15 na hare-haren Rasha, in ji sojin Ukraine

    Rundunar sojin Ukraine ta ce ta harbo 15 cikin jirage 17 marasa matua da Rasha ta harba mata a daren da ya gabata, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana a Facebook.

    "A daren nan, Rasha ta kawo mana hari ta hanyar amfani da jiragen Shahed-136/131 da Iran ke ƙerawa," a cewar sanarwar.

    Ta ƙara da cewa "muna ci gaba da bincike kan ɓarnar da suka yi".

    Rasha ta hari yankin Kursk, inda jiniya ta dinga ƙara a yankunan tsakiya da yammacin Ukraine.

    A cewar rundunar sojin Ukraine, Rasha ta harba makamai masu linzami uku da kuma kai hare-hare ta sama 41 a kan ƙasarsu cikin kwana ɗaya.