Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Tinubu zai bai wa kowacce jiha naira biliyan biyar don rage raɗaɗi

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye

Rahoto kai-tsaye

Badamasi Abdulkadir Mukhtar, Muhammad Annur Muhammad, Aliyu Tanko, A'isha Babangida, Abdullahi Bello Diginza and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Dakaru 25 aka kashe a jihar Neja - Hedikwatar tsaro

    Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce sojoji 25 ne aka kashe a jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar ƙasar.

    Kafafen yada labarai a Najeriya sun ambato kakakin hedikwatar tsaron, Manjo-Janar Edward Buba, yana tabbatar da hakan, lokacin da yake bayani kan kwanton-ɓaunar da aka yi wa dakarun sojin Najeriya a jihar, ranar 14 ga watan Agustan 2023.

    Manjo-Janar Buba ya ce har yanzu ana gudanar da bincike kan abin da ya janyo hatsarin jirgin saman rundunar sojin Najeriya a jihar Nejan, ya kuma buƙaci jama'ar gari su kiyaye farfagandar da ƴan bindiga ke yaɗawa a kan batun.

    Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindiga sun yiwa dakarun sojin Najeriya kwanton-ɓauna inda wasu dakarun suka mutu.

    Jirgin rundunar sojin saman Najeriya mai saukar Ungulu, ƙirar MI-171 ya faɗi ne yayin da ya ke kan hanyarsa ta kai ɗaukin gaggawa, a ƙaramar hukuma Shiroro ta jihar Neja.

  2. Majalisar dokoki ta janye mulkin soji a gabashin DR Congo

    Majalisar dokokin jamhuriyar dimokuraɗiyyar Congo ta goyi bayan janye mulkin soji a yankunan da ke gabashin ƙasar mai fama da rashin tsaro.

    A ƙuri'ar da suka kaɗa wajen taron kwana uku da suka yi, mafi yawan ƴan majalisar sun amince da dakatar da dokar mulkin sojin da ke aiki a gabashin ƙasar.

    A watan Mayun shekarar 2021 gwamnatin ƙasar ta ƙaƙaba dokar da ta kafa gwamnatin mulkin soja a yankin, tare da kawar da ta farar hula don yaƙi da ƙungiyoyin mayaƙa a yankin Ituku da kuma arewacin Kivu.

    Sai dai a cikin wani rahoto sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce lamarin ya ƙara lalacewa a yankin, inda mutane aƙalla miliyan huɗu suka rasa muhallinsu.

    Kakakin gwamnatin, Patrick Muyaya ya ce yanzu dai ana jira ne a ga matakin da shugaba Félix Tshisekedi zai ɗauka a kan batun.

  3. Tinubu zai rantsar da sabbin ministoci a ranar Litinin

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai rantsar da sabbin ministocinsa a ranar Litinin 21 ga wannan wata na Agusta.

    Za a rantsar da ministocin ne a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 10 na safe.

    A ranar Laraba ne fadar shugaban ƙasar ta sanar da ma'aikatun da sabobbin ministocin za su riƙe.

    Tinubu ya fara miƙa sunan mutum 28 ne ga majalisa don tantance su, a ranar 27 ga watan Yuli, sannan ya ƙara tura mata ƙarin sunayen a cikin watan Agusta.

    Majalisar dattawan Najeriyan ta amince da 45 daga cikin mutum 48 da shugaba Tinubu ya aike mata yayin da ta ƙi tabbatar da uku a ciki, da suka haɗa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Elrufai da Stella Okotete daga jihar Delta da kuma Danladi Abubakar daga jihar Taraba.

    • Majalisa ta amince da naɗin mutum 45 a matsayin ministocin Tinubu
    • Majalisa ba ta tabbatar da El-Rufai a matsayin minista ba
  4. Kotu ta ɗage zaman shari'ar Emefiele

    Da safiyar yau ne hukumomi suka gurfanar da gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele a kotu bisa tuhume-tuhumen da suka haɗar da na badaƙalar kuɗi naira biliyan 6.9.

    Sai dai alƙalin kotun, mai shari'a Hamza Muazu ya ɗage zaman zuwa ranar 23 ga watan Agustan 2023 saboda rashin bayyanar Sa'adatu Yaro, wata jami'a da ake zargin sun aikata laifin tare da Emiefele.

    Ga hotunan yadda Emiefele ya bayyana a kotu ranar Alhamis.

  5. Saudiyya da Iran na tattaunawar ɗinke ɓaraka

    A wani mataki na ƙara inganta dangantaka da ɗinke ɓaraka tsakanin ƙasashen Saudiyya da Iran, ministan harkokin wajen Iran, zai kai ziyara zuwa birnin Riyadh.

    A yau Alhamis ne, ake sa ran Hossein Amirab-dullahian zai yi bulaguron, watanni biyu bayan takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya kai irin wannan ziyara birnin Tehran.

    A watan Mayun bana ne, ƙasashen biyu suka mayar da hulɗar diflomasiyya tsakaninsu, shekara bakwai bayan Saudiyya ta katse duk wata alaƙa da Iran.

    Ƙasar China ce dai ta shige gaba wajen ganin sun dawo da alaƙar, a wani mataki da ake ganin Chinar na kara samun wurin zama da ƙarfin faɗa-a-ji a yankin Gabas ta Tsakiya.

  6. Emefiele ya bayyana a gaban kuliya kan tuhume-tuhume 20

    Gwamnan babban bankin Najeriya -CBN da aka dakatar, Godwin Emefiele ya bayyana a gaban kotu a yau Alhamis domin amsa zargi kan tuhume-tuhume 20 da ake masa da suka shafi rashawa.

    Lauyoyin gwamnati ne suka shigar da sabobbin zarge-zarge a kansa da suke da nasaba da 'amfani da ofishinsa wajen bayar da kwangila ba bisa ka'ida ba',

    Ana zargin Emefiele da hada baki da wata ma'aikaciyar babban bankin kasar da kuma wani kamfani wajen siyo motoci masu sulke 98 ba tare da sun bi ka'idojin bayar da kwangila ba.

    Rahotanni sun ce matar da ake zarginsu tare darekta ce a bankin na CBN kuma kawo yanzu ba su mayar da martani ba kan wadannan zarge-zargen.

    A watan Yuni ne Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele kuma hukumomi suka gabatar da shi gaban kuliya a Lagos bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba ko da yake ya musanta zargin.

  7. An sanya ranar fara shari'ar Trump

    An sanya ranar da za a fara sauraren ƙarar da ake tuhumar tsohon shugaban Amurka Donald Trump da aikata laifukan da suka shafi ƙoƙarin murɗa zaɓen shugaban ƙasa a jihar Georgia da shara ƙarya a matsayin sa na babban jami'in gwamnati.

    Masu shigar da ƙara sun ce za a fara zaman kotun a farkon watan Satumba da ke tafe.

    Jagoran alƙalan ta buƙaci Trump ya fara gabatar da kansa a farkon watan Satumba, kafin zaman shari'ar a watan Mayun baɗi, kwanaki 4 gabannin zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na zaɓe mai zuwa da wasu jihohin Amurka za su yi.

  8. Ana fargabar 'yan ci-rani fiye da 60 sun mutu a teku

    Ƴan ci-rani fiye da 60 ne ake fargabar sun mutu bayan an gano wani jirgin ruwa yana walagigi a cikin teku kusan nisan kilomita 300 daga gaɓar Cape Verde a Afirka ta Yamma.

    An yi imani cewa jirgin kwale-kwalen kamun kifin ya shafe tsawon wata ɗaya a cikin teku.

    An kuɓutar da mutum 38.

    Waɗanda suka kuɓutan sun haɗar da ƙananan yara ƴan tsakanin shekara 12 zuwa 16, a cewar Hukumar kula da Ƙaura ta Duniya.

    Rahotanni sun nuna cewa jirgin ruwan ya bar gaɓar ruwan Senegal a watan Yuli ɗauke da 'yan ci-rani sama da 100. Kuma kusan waɗanda ke cikin kwale-kwalen ƴan ƙasar Senegal ne.

    Ana jin cewa jirgin ya nufi tsibiran Canary na ƙasar Sifaniya.

    Wani jirgin masunta daga ƙasar Sifaniya ne ya gano kwale-kwalen, inda ya sanar da hukumomin Cape Verde.

    Hukumomin agaji sun gano gawawwakin mutum bakwai.

  9. Malamai za su fara ladabtar da ɗalibai a Koriya ta kudu

    Ma'aikatar Ilimi a Koriya ta Kudu ta amince da wata sabuwar doka da za ta bai wa malaman makaranta damar horas da duk ɗalibin da ya aikata ba daidai ba, bayan zanga-zangar da su ka yi kan cin zarafin da ɗalibai da iyayensu ke yi musu.

    Daga watan Satumba, malaman su na da ikon korar ɗalibai masu surutu dagaa aji a lokacin darasi, da kuma korar waɗanda aka kama da wayar salula a aji tare da ƙwace ta.

    Dokar dai, ba ta ba su damar dukan dalibi ko ba shi horo mai tsanani ba, amma Malaman sun samu ƴancin ficewa daga ɗakin tattaunawa tsakanin iyayen ɗalibai da malaman idan suka fara furta kalaman ɓatanci ko zagi ko cin zarafi a gare su.

    Wannan na zuwa ne bayan wata malama ta kashe kanta a watan Yuli, sanadin cin zarafin da iyayen wasu ɗalibai suka yi mata har da kokawa lokacin da take tsaka da koyarwa.

  10. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Alhamis.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye tare da ni Badamasi Abdulkadir Mukhtar.

    Ku biyo mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.