Tinubu zai bai wa kowacce jiha naira biliyan biyar don rage raɗaɗi
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye
Rahoto kai-tsaye
Badamasi Abdulkadir Mukhtar, Muhammad Annur Muhammad, Aliyu Tanko, A'isha Babangida, Abdullahi Bello Diginza and Mukhtar Adamu Bawa
Rufewa
Masu bin mu a wannan shafi, ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kenan.
Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta don ci gaba da tafka muhawara a kan labaran da muka wallafa.
Aisha Babangida ke fatan mu kwana lafiya
Faransa ta kama mutum hudu da take zargi da hannu a nutsewar kwale-kwale
Asalin hoton, bbc
Bayanan hoto, ...
Hukumomin Faransa sun ce sun kama wasu mutum hudu bisa zargin hannu a kifewar wani kwale-kwale da 'yan ci-rani ranar Asabar.
Lamarin da ya yi sanadaiyyar mutuwar mutum shida da ke cikin jirgin da ya samu matsala a kusa da Calai.
Jami'an tsaron tekun Faransa da na Birtaniya sun ceto wasu mutum fiye da 50.
Rahotanni sun ce alkalan Faransa na nazarin tuhume-tuhume da za ayi wa mutanen 'yan asalin Iraqi da Sudan da aka kama kuma ake zargi da kisan kai ba da gangan ba.
Kafafen yaɗa labaran Faransa sun ce ana kyautata zaton akalla biyu daga cikin mutanen na da alaka da hanyoyin safarar mutane.
Rahotonni sun ce mutanen da ke cikin jirgin ‘yan kasar Afganistan ne, yayin da wasu kuma ‘yan kasar Sudan ne.
Sweden ta ce tana fuskantar barazanar ta'addanci
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, ...
Kasar Sweden ta ce tana ƙara fuskantar barazanar ta`addancin a daidai lokacin da ake cigaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasashen duniya sakamakon ƙona ƙur`anin da aka yi.
A watan Yunin da ya wuce ne wani mai zanga-zanga ya yayyaga wasu shafukan alkur`ani, kana ya kona su a wajen babban masalcin Stockholm.
Firaiminista, Ulf Kristersson, ya shaida wa manema labarai cewa Sweden ta wargaza shirin kai mata hari daban-daban, amma bai yi cikakken bayani a kan lamarin ba.
Shugaban `yan sandan kasar ya ce barazanar da kasar ke fuskanta ta mataki na biyu a ma`aunin barazanar ta`addanci.
Saudiyya ta gayyaci shugaban Iran
Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Saudiyya ta gayyaci shugabanƙasar Iran da ta dade tana adawa da shi domin ya ziyarci ƙasar.
Ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da ya yi da takwaransa na Iran Hossein Amir-Abdollahi a birnin Riyadh.
Kasashen biyu sun goyi bayan bangarorin da ke adawa da juna a rikice-rikicen gabas ta tsakiya, amma sun amince da daidaita dangantakarsu a watan Maris.
Akwai gagarumin bambancin ra'ayi tsakanin ƙasashen biyu,sai dai sun yanke shawarar daidaitawa da juna bayan da suka fahimci suna tafka asarar biliyoyin kuɗaɗe a yaƙin Yamen da sauran sassan gabas ta tsakiya.
Saudiyya ta yanke hulda da Iran a cikin shekara ta 2016, bayan da masu zanga-zanga suka mamaye ofishin jakadancinta da ke Tehran.
Hatsarin jirgin sama ya kashe mutane 10 a Malaysia
Asalin hoton, EPA/EFE/REX/SHUTTERSTOCK
Bayanan hoto, ...
Akalla mutane 10 sun mutu a lokacin da wani jirgin sama mallakin wani mutum ya yi karo da wata mota da babur a kan wata babbar hanya a lokacin da yake yunkurin sauka, in ji 'yan sandan Malaysia.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Malaysia ta ce fasinjoji shida da ma'aikatan jirgin biyu na cikin jirgin Beechcraft.
Jirgin dai ya taso ne daga Langkawi zuwa Selangor, zuwa yammacin babban birnin Kuala Lumpur.
Shugaban ‘yan sandan Selangor ya ce jirgin ya rasa hanyar sadarwa da masu kula da zirga-zirgar jiragen.
Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa yana aiki a wurin a matsayin injiniya lokacin da ya ji karar fashewar wani abu,ya je inda hatsarin ya faru, a nan ya ga mutane da suka jikkata.
Mohamad Syahmie Mohamad Hashim - wanda tsohon mamba ne a rundunar sojin saman Malaysia - ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa ya ga jirgin yana tashi ta hanyar da ba ta dace ba.
Cire tallafin mai: Majalisar tattalin arziƙi za ta yi aiki da ƙungiyar ƙwadago
Asalin hoton, Kaduna Governor/Twitter
Bayanan hoto, Majalisar Tattalin Arzikin - wadda mataimakin shugaban ƙasa ke jagoranta - ta ƙunshi gwamnonin jihohin ƙasar 36
Majalisar kula da Tattalin Arzikin Najeriya ta ce ta ɗauki wani mataki na tunkarar matsalar cire tallafin man fetur a kasar, inda ta kafa wani kwamitin wucin gadi.
Babban manufar kafa kwamitin ita ce fara tattaunawa da shugabannin kungiyoyin kwadago na jihohi daban-daban don samun mafita.
A yayin taron majalisar karo na 135 a Abuja ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Sanata. Kashim Shettima ne aka yanke shawarar kafa kwamitin.
Kwamitin ya kunshi shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq da Gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo da Shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Hope Uzodinma na jihar Imo da Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed na jihar Bauchi, da gwamnan jihar Abia, Alex Otti.
Asalin hoton, Kaduna Governor
Mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa aikin kwamitin shi ne hada kai da shugabannin kungiyar kwadago a fadin Najeriya domin samar da mafita mai amfani ga ƙasar bayan cire tallafin man fetur.
Bugu da kari, majalisar ta NEC ta samu bayanai kan yadda ake ci gaba da raba muhimman kayayyaki a fadin ƙasar baki daya kamar shinkafa da hatsi da takin zamani ga jihohi.
An kuma amince da matakin ba da tallafin kuɗi naira biliyan biyar daga gwamnatin tarayya, tare da jinjina wa babban bankin Najeriya (CBN) da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) bisa gudunmawar suke takawa game da wadannan tsare-tsare.
Hukumar ta kuma amince da kokarin da gwamnatocin jihohi ke yi a nasu aikin, tare da kara musu ƙwarin gwiwar fadada rabon kayan agaji domin rage wahalhalun da ‘yan kasa ke ciki musamman talakawa masu karamin karfi.
Majalisar ta kuma miƙa ta'aziyya ga rundunar sojojin Najeriya da iyalansu kan kisan da aka yi wa wasu dakarunta a jihar Neja tare da yin shiru na minti daya don karrama mamatan.
Barcelona ta naɗa Deco a matsayin daraktan wasanni
Amurka ta tura sabuwar jakadiya zuwa Nijar
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, ...
Ana sa ran nan ba da jimawa ba sabuwar jakadiyar Amurka a Nijar za ta fara aikinta a Yamai babban birnin kasar.
An dora wa Kathleen Fitzgibbon jagorancin tawagar Amurka a Nijar lokacin da mataimakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Vedant Patel ya bayyana lokaci da cewa mai matukar muhimmanci.
Ana kuma sa ran jakadan za su hada kai da kokarin gwamnatin Amurka wajen magance juyin mulkin da kuma tallafa wa Amurkawa da suka makale a Nijar.
Mista Patel bai fayyace lokacin da sabon wakiliyar za ta je Nijar ba.
Sai dai ya shaida wa manema labarai a ranar Larabar da ta gabata cewa tafiyarta zuwa Nijar ba zai nuna wani sauyi kan yadda gwamnatin Amurka ke ganin juyin mulki da sojoji suka yi ba.
Ya ce Amurka ta jajirce wajen inganta tsaro, kwanciyar hankali, da dimokuradiyya a yankin Sahel.
"muna ci gaba da bayar da shawarwarin samar da mafita ta hanyar diflomasiyya da ke mutunta tsarin mulkin Nijar, da kuma gaggauta sakin shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa," in ji Mista Patel.
Ms FitzGibbon jami'ar diflomasiyya ce da ke da kwarewa sosai wajen yin aiki a Afirka.
Majalisar dattawan Amurka ta tabbatar da ita a matsayin jakadiyar Nijar a ranar 27 ga watan Yuli, kwana daya bayan juyin mulkin Nijar.
Nijar ta kasance ba tare da jakadan Amurka ba tun watan Disambar 2021.
Zargin cin hanci ya yi wa kotun zaɓen Kano dabaibayi
Gwamnatin Najeriya za ta bai wa kowacce jiha naira biliyan biyar don rage raɗaɗi
Asalin hoton, Twitter/DOlusegun
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da bai wa kowacce jihar naira biliyan biyar domin sayen kayan abinci don raba wa talakawa a jihohin a matsayin kayan rage raɗaɗi..
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim - kaɗan bayan kammala taron majalisar tattalin arziki da aka gudanar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.
Matakin na zuwa ne mako guda bayan tashin gwauron zabi da farashin kayan abinci suka yi a ƙasar da kusan kashi fiye da 20 cikin 100 cikin shekara 18.
Lamarin da masana ke dangantawa da cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.
Gwamnan na jihar Borno ya ce gwamnatin tarayya ta bai wa kowane gwamna tirela biyar na shinkafa domin rabawa a jiharsa.
Zulum ya ce gwamnonin za su sayi buhun shinkafa 100,000 da na masara 40,000 da kuma takin zamani domin raba wa al'umominsu do taimaka musu wajen rage raɗaɗin tsadar rayuwa da suke fuskanta.
Tun da farko sakataren gwamnatin tarayya George Akume ya ce an bai wa jihohin ƙasar 36 tirela 100 na taki da tirela 100 ma hatsi a matsayin tallafin rage raɗaɗin.
Mista Akume ya bayyana hakan ne a lokacin bikin ƙaddamar da littafin tarihin Edwin Clark.
Barcelona ta naɗa Deco daraktan wasanni
Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta saɗa tsohon ɗan wasan tsakiyarta Deco a matsayin sabon daraktan wasannin ƙungiyar
Dan kasar Portugal, haifaffen Brazil, mai shekara 45, ya sanya hannu kan kwantiragin shekara uku a Nou Camp.
A shekarar 2004 ne Deco ya fara komawa Barcelona daga Porto, kuma ya lashe gasar La Liga sau biyu a kakar wasanni huɗu, da kuma gasar Zakarun Turai a shekarar 2006.
Barca ta ce Deco zai jagoranci sabuwar aƙidar wasansu kuma zai yi aiki tare da kociyan ƙungiyar Xavi da sauran masu taimaka masa.
Ƙungiyar ta ce tana shirin yi wa bangaren gudarwarta garambawul, inda ba da cikakkun bayanai nan da makonni masu zuwa.
Tsohon daraktan wasanni Jordi Cruyff ya bar kungiyar a watan Mayu.
Deco ya kuma buga kakar wasa biyu a Chelsea bayan zamansa a Sifaniya kafin ya koma Brazil inda ya yi ritaya a kungiyar Fluminense da ke Rio de Janeiro.
Manchester United na tattaunawa mai zurfi kan Greenwood
DSS ta bankaɗo shirin kai wa jirgin ƙasa hari
Asalin hoton, NIGERIAN RAILWAY
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya, ta fitar da wata sanarwa da ke gargadin hukumar da ke kula da sufurin jirgin kasa ta Najeriya cewa ƴan bindiga na kitsa kai hari daga kowane lokaci a layin dogo da ya hada
Kaduna zuwa Abuja.
Babban daraktan hukumar ta DSS reshen birnin Abuja, R.N. Adepemu, cikin wata wasiƙa ya ce an yi wannan gargaɗin ne domin ɗaukar ƙwaƙƙwaran matakan tsaro a kan wannan hanya, kana ta bayar da shawarwarin da suka dace a ɗauka.
Wasikar ta ci gaba da cewa, bayanan sirri
da aka samu sun tabbatar da wannan shirin na kai mummunan harin daga kowane lokaci
a yanzu.
Ya ce maharan na shirin amfani da irin salon da suka taɓa bi a baya wajen kai harin, inda suke shirin kai hari tare da sace fasinjoji domin neman kudin
fansa.
Daga cikin matakan da hukumar ta nemi a ɗauka sun haɗa da amfani da jiragen
sama domin shawagi a wuraren domin lura da abubuwan da ka je su zo, wanda ya
haɗa da gudanar da sintirin a kan hanyar da kewayenta.
Haka kuma hukumura ta DSS ta nemi a samar da ƙarin jami‘an soji da yan
sanda don gudanar da binciken jama‘a da ababen hawa da baza jami’an tsaro a
dazukan Byazhin da Jibi da dazukan Ja, haɗi da samar da na’urorin sadarwa
ga jami’an sintiri na ƴan sanda da kuma samar da wata tawagar ƴan sandan ko-ta-kwana waɗanda aikinsu shi ne kai ɗaukin gaggawa a lokocin buƙatar hakan,
tare da samar da tsarin tattauna bayanan sirri da suka shafi tsaro a tsakaninsu.
Wasikar ta ci gaba da cewa, duk da ya ke wannan bayanin da aka yi hasashen
aukuwar sa, bai fito sarari ba, amma zai iya jefa fargaba sakamakon neman samar
da tsaron dukiya da rayukan jama’a da ke zirga-zirga akan wannan hanyar, inda
hukumar ta nemi kada a ruruta labarin har ya zarce yadda aka bayyana
shi.
Kazalika hukumar ta DSS ta ce yin wanan gargaɗi a kan lokaci na da manufar
kaucewa maimaita abinda ya taba faruwa da farko ne, inda aka samu mummunan
harin da ya kai ga wasu fasinjoji sun rasa rayuwarsu kana wasu su ka jikkata, baya
ga yin garkuwa da wasu, da ƴan bindigar suka yi na tsawon watanni kafin
su kai ga samun ƴanci, bayan biyan kuɗin fansa.
'Talge muka riƙa sha da azumin bara a hannun maharan jirgin ƙasan Kaduna'
Maharan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna sun sake sakin mutum huɗu
Olise ya tsawaita kwantiragi duk da Chelsea na zawarcinsa
Guardiola ya lashe kofin UEFA Super Cup karo na uku
An yi zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin a Syria
Asalin hoton, Reuters
Ɗaruruwan masu zanga-zanga a Syria sun rufe tituna tare da ƙona tayoyi suna masu rera waƙoƙin ƙin jinin gwamnati.
Masu zanga-zangar sun riƙa ɗaga alamomin da ke nuna adawa da gwamnatin ƙasar sakamakon ƙara farashin mai da kuma matsin tattalin arziƙi da ƙasar ke fuskanta.
Sun kuma riƙa kiraye-kirayen a hamɓarar da gwamnatin shugaba Bashir Al Assad.
Janye tallafin man fetur da gwamnatin Syria ta yi ya janyo gagarumin tashin farashin mai da kuma sauran kayyayaki a ƙasar.
Gwamnatin Syria ta bayar da damar kai agaji yankin 'yan tawaye
An garzaya da Ousmane Sonko sashen kula da masu ciwo mai tsanani
Asalin hoton, AFP
Makusantan jagoran adawar Senegal, Ousmane Sonko - wanda ke yajin cin abinci - sun ce an garzaya da shi sashen kula da masu tsananin ciwo don kula da lafiyar sa.
Wani ɗan jami'iyyar Pastef ta Ousmane Sonko, Ousseynou Ly ya ce "Mista Sonko ya fara rashin lafiya a daren ranar Laraba".
Jam'iyyar Pastef ta ce hukumomin Senegal ne ke da laifi kan duk abin da ya faru da Sanko.
Hukumomin Senegal ba su fitar da wata sanarwa kan halin da Ousmane Sonko ke ciki ba.
Ya dai yi shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaben ƙasar da za a yi cikin watan Fabrairun baɗi, amma ya shiga dambarwar siyasa da hukumomi tun daga shekarar 2021, lokacin da aka ƙaddamar da bincike kan zargin rashawa da gwamnati ke masa.
A cikin watan Yuni aka yanke wa Sanko hukuncin zaman wata biyu a gidan yari, a shari'ar da ya yi iƙirarin cewa bita-da-ƙullin siyasa ne.
Lamarin ya janyo bore daga magoya bayansa, kuma ya kai ga mutuwar mutum 24, kamar yadda ƙungiyar Amnesty International ta tabbatar.
Bayan wata ɗaya ne aka kama shi, aka kuma gurfanar da shi a mako mai zuwa a bisa zargin tunzura tashin hankali.
Me 'yan Najeriya ke cewa kan ma'aikatun ministocin Tinubu?
Hotunan taron manyan hafsoshin sojin Ecowas a Ghana
Manyan hafsoshin sojin ƙungiyar Ecowas sun fara taro a birnin Accra na Ghana don tattaunawa kan Nijar.
Bayanan hoto, Lokacin da hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa ya isa zauren taron.
Bayanan hoto, Yadda hafsoshin sojin ke shiga zauren taron a birnin Accra na Ghana.
Bayanan hoto, Taron na ranar Alhamis zai mayar da hankali ne ga tsara matakin da ya dace Ecowas ta ɗauka kan sojin da suka ƙwace mulki a Nijar.
Bayanan hoto, A baya ma dai sojojin Ecowas sun yi makamancin wannan taro a birnin Abuja na Najeriya.
Bayanan hoto, Shugabannin Ecowas sun umarci sojojinsu su zamo cikin shirin ko-ta-kwana don ƙwato mulkin daga hannun sojin Nijar idan tattaunawar sulhu ta gagara.
Bayanan hoto, Zauren taron da manyan hafsoshin Ecowas ke tattauna matakin da za su ɗauka kan Nijar.
Bayanan hoto, Ana sa ran hafsoshin su sanar da matsayar da suka cimmawa game da Nijar ɗin a ƙarshen taron na ranar Alhamis.
Gungun mutane sun ƙona coci-coci bisa zargin wulakanta addini a Pakistan
Asalin hoton, Reuters
Ƴan sanda a Pakistan sun ce dubban Musulmai sun ƙona cocI-coci guda huɗu, sun kuma fasa wasu gidaje bayan wulaƙanta Alƙur'ani mai girma da wasu Kiristoci guda biyu suka yi.
Mazuna birnin Jaranwala da ke Gabashin Punjab sun ce wasu gomman gine-gine da ke kusa da coci-cocin su ma sun ƙone.
Ƴan sanda suna tsare da wasu masu zanga-zanga fiye da 100, sun kuma ƙaddamar da bincike a kan rikicin.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar, amma sun bayar da tabbacin cewa ba a kashe kowa ba.
Jami'an tsaron sun kuma shigar wani Kirista mazaunin yankin ƙara, bayan sun zarge shi da cin mutuncin addini, laifin da dokar ƙasar ta yi wa tanadin hukuncin kisa.
Duk da cewa Pakistan ba ta taɓa zartar da hukuncin kisa ga masu aikata laifin wulakanta addini ba, irin wannan laifi yana saurin kawo zanga-zanga da tashin hakankali, har ma da kisan waɗanda ake zargi da laifin.