Babbar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta gargaɗi Ƙungiyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (Ecowas) kan amfani da ƙarfin soji a Nijar don mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi, mai ɗauke da sa hannun shugabanta na ƙasa, Comrade Joe Ajaero, ta ce rashin amfanin da ke tattare da yunƙurin ya zarta amfaninsa.
A cikin makon da ya gabata ne ƙungiyar Ecowas ta gudanar da wani taron gaggawa a Abuja babban birnin Najeriya, inda ta umarci dakarunta su shiga cikin shirin ko-ta-kwana, a yunƙurin da ƙungiyar ke yi na maido da shugaba Bazoum kan karagar mulki.
A taro, shugaban ƙungiyar Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban Najeriya, ya ce za a yi amfani da duk matakan da suka dace, ciki har da na soji , idan ta kama domin mayar da shugaba Bazoum.
To sai dai NLC ta ce hakan ba abin da zai haifar, sai jefa rayuwar hamɓararren shugabna ƙasar da na iyalansa cikin hatsari, tare da haifar wa ilarihin yankin yammacin Afirka faɗawa cikin mummunar matsala, ciki har da arewacin Najeriya.
Kungiyar ta kuma ce hakan ka iya haifar da asarar rayuka masu yawa ga al'ummar yankin yammacin Afirka.
A ranar Asabar ne dai tawagar malaman addinin Musulunci ta Najeriya ta gana da shugabannin juyin mulkin na Nijar.
Inda malaman suka ce sojojin sun amince su tattauna da ƙungiyar Ecowas domin daidaita al'amura.
A ranar 26 ga watan Yuli ne sojojin Nijar suka kifar da gwamnatin fara hula ta shugaban Bazoum a Nijar tare da ci gaba da tsare shi, tare da shi da iyalansa, da kuma ɗansa mai shekara 20 a fadar shugaban ƙasar.