Gwamnatin sojin Nijar na yawon neman goyon bayan ƙasashe

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawo wa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. NLC ta gargaɗi Ecowas kan afka wa Nijar da yaƙi

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta gargaɗi Ƙungiyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (Ecowas) kan amfani da ƙarfin soji a Nijar don mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi, mai ɗauke da sa hannun shugabanta na ƙasa, Comrade Joe Ajaero, ta ce rashin amfanin da ke tattare da yunƙurin ya zarta amfaninsa.

    A cikin makon da ya gabata ne ƙungiyar Ecowas ta gudanar da wani taron gaggawa a Abuja babban birnin Najeriya, inda ta umarci dakarunta su shiga cikin shirin ko-ta-kwana, a yunƙurin da ƙungiyar ke yi na maido da shugaba Bazoum kan karagar mulki.

    A taro, shugaban ƙungiyar Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban Najeriya, ya ce za a yi amfani da duk matakan da suka dace, ciki har da na soji , idan ta kama domin mayar da shugaba Bazoum.

    To sai dai NLC ta ce hakan ba abin da zai haifar, sai jefa rayuwar hamɓararren shugabna ƙasar da na iyalansa cikin hatsari, tare da haifar wa ilarihin yankin yammacin Afirka faɗawa cikin mummunar matsala, ciki har da arewacin Najeriya.

    Kungiyar ta kuma ce hakan ka iya haifar da asarar rayuka masu yawa ga al'ummar yankin yammacin Afirka.

    A ranar Asabar ne dai tawagar malaman addinin Musulunci ta Najeriya ta gana da shugabannin juyin mulkin na Nijar.

    Inda malaman suka ce sojojin sun amince su tattauna da ƙungiyar Ecowas domin daidaita al'amura.

    A ranar 26 ga watan Yuli ne sojojin Nijar suka kifar da gwamnatin fara hula ta shugaban Bazoum a Nijar tare da ci gaba da tsare shi, tare da shi da iyalansa, da kuma ɗansa mai shekara 20 a fadar shugaban ƙasar.

  3. Karyewar farashi na haddasa fargaba a china

  4. Mutum huɗu sun mutu a harin da aka kai masallaci a Iran

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A shekarar da ta gabata ma an kashe mutum 13 a wani hari da aka kai masallacin

    Akalla mutum huɗu ne suka mutu a wani hari da aka kai wa masallacin Cheragh da ke Shiraz a ƙasar Iran.

    Kafofin yaɗa labaran kasar sun ce mutum biyu cikin waɗanda suka mutun, hadiman masallacin ne, wanda ke zama masallaci na uku mafi daraja a Iran.

    Rahotonni sun ce wasu mutum biyu ne ɗauke da makamai suka ƙaddamar da harin.

    'Yan sanda sun samu nasarar kama guda daga cikinsu, yayin da ɗayan ya tsare. Sai dai 'yan sandan sun ce suna farautarsa.

    A watan Octoban shekarar da ta gabata ma wani hari da ƙungiyar ISIS ta yi kirarin kai wa masallacin ya kashe mutum 13.

    A watan da ya gabata ne hukumomin Iran suka zartar da hukuncin kisa kan mutum biyu da aka samu da laifin taimaka wa maharan.

  5. Faɗa ya sake ɓarkewa a wasu biranen Sudan

    e

    Asalin hoton, Reuters

    Faɗa ya ɓarke a birnin Nyala da ke yammacin Sudan da sauran wurare a kudancin yankin Darfur, kamar yadda wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Ana fargaɓar faɗan zai iya yaɗuwa zuwa ilahirin yankin na Darfur da ke yammacin ƙasar.

    Rikicin da ake yi a birnin Khartoum ya haifar da hare-haren ƙabilanci a yammacin Darfur, tare da raba sama da mutum miliyan huɗu da muhallansu zuwa makwabtan ƙasashen Chadi da Masar da Sudan ta Kudu da sauran ƙasashe.

    A baya birnin Nyala - birni na biyu mafi girma a ƙasar - ya fuskanci faɗan da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF.

    Faɗan na baya-bayan na ya lalata ababen more rayuwa kamar lantarki da ruwan sha da kuma hanyoyin sadarwa a birnin na Nyala, kamar yadda Reuters ya ruwaito.

    Kungiyar lauyoyin Darfur, mai sa ido kan hakkin bil-adama ta ce aƙalla mutum takwas ne suka mutu sakamakon faɗan na baya-bayan nan.

  6. An raba maki tsakanin Chelsea da Liverpool a Premier

  7. An kashe jaririya 'yar mako uku da iyayenta a wani hari da Rasha ta kai Ukraine

    UKRAINE GOVERNMENT

    Asalin hoton, UKRAINE GOVERNMENT

    Wani hari ta sama da Rasha ta ƙaddamar a kudancin Ukraine ranar Lahadi ya yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai ciki har da wani jariri ɗan mako uku tare da iyayensa.

    Ministan harkokin cikin gida na Ukraine, Igor Klymenko, ya ce harin ya faɗa kan gidan iyalan huɗu da ke ƙauyen Shyroka Balka a yankin Kherson.

    Haka kuma wasu ƙarin mutum uku sun mutu a ƙauyen Stanislav, da ke makwabtaka.

    Ministan ya yaɗa hotunan ɓarnar da harin ya haddasa a ƙauyen Shyroka Balka, inda suka nuna baƙin hayaƙi na tashi daga gine-ginen, ter da hotunan gawarwakin mutanen.

    Kherson na daga cikin yankunanUkraine huɗu da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi iƙirarin ƙwacewa a shekarar da ta gabata.

    A watan Nuwamban bara ne dakarun Ukraine suka ƙwace wani ɓangare na yammacin yankin, to sai dai sojojin Rasha sun ci gaba da harba makamai daga kogin Dnipro.

  8. Shin kun san tsamiya na maganin cutattukan da suka shafi fata?

    Akan samu bishiyar tsamiya a ƙasashen Afirka da na yankin Asiya.

    Dakta Halima Abdulƙadir Idris malama a Jami'ar Bayero da ke Kano ta ce ana amfani da tsamiya wajen yin magungunan da suka shafi fata, da lemon tsamiya.

    Tsamiya na ƙunshe da sinadarin vitamin C, da Vitamin D da E da ke taimakawa wajen gina jikin ɗan adam, kamar yadda malamar jami'ar ta bayyana.

    Ta ƙara da cewa ana amfani da tsamiya wajen maganin cututtukan da suka shafi fata da haɗa abincin yara.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  9. Mancini ya yi ritaya daga horas da Italiya

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Roberto Mancini ya yi ritaya daga aikin kociyan tawagar Italiya, bayan shekara biyar yana kan aikin.

    Dan kasara Italiya ya fara aiki tun bayan da kasar ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya ta 2018.

    Ya dauki kofin nahiyar Turai Euro 2020 a Wembley, bayan nasara a kan Ingila a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

    Daga nan tawagar ta kafa tarihin wasa 37 a jere ba tare da an doke ta ba, amma ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya a 2022, wanda Argentina ta lashe.

    Ana sa ran tawagar hukumar kwallon kafar Italiya za ta sanar da sabon wanda zai maye gurbin tsohon kociyan Manchester City.

    Italiya tana ta uku a rukunin neman shiga gasar nahiyar Turai ta 2024 da za a yi a Jamus, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Ingila a cikin watan Maris.

    Za ta buga wasan gaba da Arewacin Macedonia ranar 9 ga watan Satumba da kuma fuskantar Ukraine ranar 12 ga watan Satumba.

    Mancini tsohon dan kwallon tawagar Italiya da Sampdoria ya horar da Manchester City da lashe Premier League a 2012.

    A karkashin jagorancinsa Italiya ta kare a mataki na uku a Nations League a watan Yuni.

    Kociyan ya yi fama da fuskantar matsi tun bayan da Italiya ta kasa samun gurbin zuwa Qatar buga gasar kofin duniya a watan Maris, bayan rashin nasara a hannun Arewacin Macedoni.

  10. Watakila Mbappe ya ci gaba da zama a PSG

  11. Gwamnatin sojin Nijar na yawon neman goyon bayan ƙasashe

    Sojojin Nijar

    Asalin hoton, Reuters

    Sojojin da ke mulkin Nijar na ci gaba da neman goyon bayan ƙasashen Afirka ta Yamma, waɗanda su ma ke ƙarƙashin mulkin soja.

    Rahotanni sun bayyana cewa wata tawaga da sojojin suka tura ta isa Guinea a ranar Asabar.

    Kafin haka, sabon ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Mody, ya isa Mali a ranar Juma'a cikin wata gajeriyar ziyara.

    Ƙasashen Mali da Burkina Faso da Gueinea da ke Afirka ta Yamma, dukkansu na ƙarƙashin mulkin soja kuma sun sanar da goya wa Nijar baya idan dakarun Ecowas ko na wata ƙasar waje suka kai wa sojojin hari.

    Har yanzu ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma (Ecowas) na ci gaba da yunƙurin difilomasiyya don sasanta rikicin siyasar, duk da barazanar amfani da ƙarfin soja don taka wa sojojin ƙarƙashin Janar Abdourahmane Tchiani birki.

    A gefe guda kuma, fitattun mutane da ƙungiyoyi a Najeriya na ci gaba da nuna adawa da yin amfani da ƙarfin yayin da Shugaba Bola Tinubu, a matsayinsa na shugaban Ecowas, yake jagorantar yunƙurin.

  12. Baturen da ya ƙware a Hausa ta BBC da litattafan soyayya

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu:

    Shirin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu na wannan makon ya tattauna da wani Baturen Italiya da ya koyi harshen Hausa ta hanyar sauraron BBC da kuma karatun litattafan soyayya na Hausa.

  13. 'Yan bindiga sun kashe sojojin Mali shida

    Mali

    Asalin hoton, Reuters

    Wani harin 'yan bindiga ya kashe sojojin Mali shida a arewacin ƙasar, kamar yadda rundunar sojan ta bayyana.

    Kamfanin labarai na AFP ya ruwaito cewa tun a ranar Asabar rundunar sojan ta ba da rahoton kashe sojanta ɗaya da kuma raunata wasu huɗu a harin da aka kai a Ber ranar Juma'a.

    Yanzu adadin ya kai shida, a cewar sanarwar, yayin da "aka kashe 'yan ta'addan 24".

    Haka nan, sun gudu sun bar bindigogi ƙirar AK-47 da babura, in ji sojin.

    Ta ƙara da cewa fafatawar da aka yi a yankin Timbuktu ta faru ne "bayan wani gungun 'yan ta'adda ya yi yunƙurin kutsawa sansanin sojin Mali".

    Tun farko an tsara kai sojojin Ber ne domin su maye gurbin dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da ake kira MINUSMA yayin da suke shirin barin Mali.

    Sojojin da ke mulkin Mali tun 2020 sun kori dakarun kiyaye zaman lafiyar ne a watan Yuni, inda suka ba su wa'adin kafin ƙarshen shekara.

  14. Ma'anar unguwar 'Tudunwada' da yadda ta samo asali

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Shirin Amsoshin Takardunku

    Filin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambayoyi biyu da suka shafi tarihi da kuma likitanci.

    Mece ce ma'anar kalmar Tudunwada? wato shahararrun unguwanni da ake da su a faɗin ƙasar Hausa.

    Sannan likita ya amsa tambaye game da yadda ake samun lalurar cin ruwa yatsu.

    Shirin na zuwa ne ta rediyo duk ranar Asabar da dare, a kuma maimaita shi ranar Lahadi.

  15. Haɗurran mota a Najeriya sun kashe mutum 4,387 a rabin 2023

    Bisi Kazeem

    Asalin hoton, FRSC

    Jimillar mutum 4,387 ne suka mutu sakamakon haɗurran ababen hawa cikin wata shidan farko na 2023 a Najeriya, a cewar hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa.

    Jami'in faɗakarwa na hukumar Federal Road Safety Corps (FRSC), Bisi Kazeem, ya faɗa wa kamfanin labarai na Najeriya NAN cewa daga watan Janairu zuwa Yunin 2023 an samu mutum 14,108 da suka ji raunuka.

    A lissafi na tsakatsaki, alƙaluman na nufin mutum 731 ne ke mutuwa duk wata, ko kuma 24 a kowace rana, a cewar rahoton na NAN.

    "Waɗannan haɗurra na faruwa ne saboda tafiya cikin dare, da gajiya, da karya dokar hanya, da wucewar ganganci, da amfani da tayoyin da suka gama aiki, da kuma tsananin gudu," in ji Mista Kazeem.

    "Ka san kuma jami'anmu ba su aiki cikin dare, saboda haka ne direbobi ke amfani da wannan damar wajen karya dokokin tuƙi."

  16. Katsinawa na zanga-zangar goyon bayan Ecowas kan juyin mulkin Nijar

    Katsina

    Asalin hoton, Bishir Dauda

    Bayanan hoto, Gomman masu zanga-zangar lumana sun fito kan titunan birnin Katsina da ke arewacin Najeriya don yin tir da da juyin mulkin sojoji suka yi a Jahuriyar Nijar tare da nuna goyon baya ga ƙungiyar Ecowas.
    Katsina

    Asalin hoton, Bishir Dauda

    Bayanan hoto, Masu macin ɗauke da kwalaye masu saƙonni iri-iri sun zagaya titunan birnin a safiyar yau Lahadi, a jihar da ke maƙwabtaka da Nijar.
    Katsina

    Asalin hoton, Bishir Dauda

    Bayanan hoto, "A saki Bazoum," kamar yadda ɗaya daga cikin kwalayen ke cewa. Wani kuma ya ce "muna tare da Ecowas".
    Katsina

    Asalin hoton, Bishir Dauda

    Bayanan hoto, Ƙungiyar Coalition of Pro-Democracy Activists wadda ta shirya zanga-zangar, ta yi "kira da babbar murya ga sojojin mulki da su buɗe ƙofar tattaunawa da Ecowas don shawo kan matsalar".
  17. Kalli ɓarnar da wutar daji ta yi wa garin Lahaina a Amurka

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

    Muutm 89 aka tabbatar da mutuwarsu zuwa yanzu sakamakon wutar dajin da ta ƙone garin Lahaina da ke jihar Hawaii a Amurka.

    Gwamnan jihar, Josh Green, ya yi gargaɗin cewa "adadin zai iya ƙaruwa sosai", yayin da ake ci gaba da aikin neman waɗanda ba a gani ba.

    Akwai ɗaruruwan mutanen da ba a san inda suke ba.

  18. NEMA ta fara raba wa iyalai 22,000 kayan tallafi a Kano

    Tallafi

    Asalin hoton, NEMA

    Bayanan hoto, Mataimakin Gwamnan Kano Aminu Abdulsalam-Gwarzo ne ya jagoranci raba kayayyakin

    Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya National Emergency Management Agency (NEMA) ta ƙaddamar da rarraba kayan tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a 2022 da kuma mabuƙata a jihar Kano da ke arewacin ƙasar.

    Shugaban hukumar, Mustapha Ahmed-Habib, ya ce suna sa ran raba kayan ga iyalai 660,000 a faɗin Najeriya.

    Mataimakin Gwamnan Kano Aminu Abdulsalam-Gwarzo, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a rabon kayan ranar Asabar, ya ce iyalai 979 ne za su amfana daga ƙananan hukumomi 20 na Kano, yayin da aka ware wa ƙananan hukumomin Municipal da Tarauni 1,520 kowacce.

    Cikin kayan abinci da aka raba akwai shinkafa, da wake, da dawa, da kayan miya, da gishiri, da kuma sinadaran ɗanɗano.

    Kazalika, an raba kayayyakin noma da na inganta rayuwa kamar gidan sauro, da ledoji, da barguna, da katifu, da botikai na roba, da risho, da tukunyar girki.

    Aminu Abdulsalam ya nemi waɗanda suka amfana da tallafin da kada su sayar da su, yana mai cewa an ba su ne don su inganta rayuwarsu.

    Tallafi

    Asalin hoton, NEMA

  19. Wutar daji ta kashe mutum 89 a Hawaii zuwa yanzu

    Lahaina

    Asalin hoton, Reuters

    Wutar dajin tsibirin Maui(Mawe) da ke Hawaii ta zamo babbar musibar da ta afkawa Amurka a cikin sama da shekaru 100.

    Zuwa yanzu akalla mutum 89 ne aka tabbatar sun rasa ransu sakamakon wutar.

    Gwamnan Hawaii, Josh Green, ya yi gargadin cewa za a iya samun karuwar adadin wadanda suka mutu.

    Ya shaida wa manema labarai cewa kudin da aka kashe wajen shawo kan wutar ya kai kusan dala biliyan shida kawo yanzu.

    Wutar ta cinye baki dayan garin Lahaina.

    Gwamnatin Amurka na kara tura kayan kai dauki don taimaka wa ma'aikatan da ke aikin kashe wutar da ma neman mutane a garin.

  20. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a wannan shafi da zai kawo rahotanni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Ku biyo ni Umar Mikail a wannan hantsi don sanin halin da duniyar ke ciki cikin harshenku mai albarka - Hausa ba dabo ba.