Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Labarin tura 'yan NYSC zuwa Nijar ba gaskiya ba ne'
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Babu abin da ya fi dacewa da ƙasarmu fiye da mulkin dimokraɗiyya - Sojojin Najeriya
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya ce babban abin da ya fi dacewa da ƙasar a wannan zamani shi ne mulkin dimokradiyya.
Babban hafsan sojin ya bayyana haka ne a lokacin bikin yayen manyan sojoji da aka gudanar da makarantar yaye manyan hafsoshi ta Jaji da ke Kaduna, kamar yadda wata sanarwa da kakakin rundunar Burgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar.
Laftanar Janar Lagbaja ya ce dole ne a tunasar da sojojin ƙasar cewa taimakonsu wajen tabbatuwa da ɗorewar mulki shi ne babbar hanyar nuna ƙwarewa a aikin soji.
Ya kuma ce babban burin kowanne ɗan Najeriya a yanzu shi ne ɗorewar mulkin dimokradiyya, wanda zai tabbatar da haɗin kan ƙasa da kuma kare muradun 'yan Najeriya, ba tare da la'akari da bambanci addini ko na ƙabila ba.
''A don haka ina kira ga duka sojojin Najeriya su bayar da gudunmowarsu wajen tabbatar da ɗorewar mulkin dimokraɗiyya, sannan su kauce wa shiga lamuran siyasa a lokacin gudanar da ayyukansu'', in babban hafsan sojojin.
Ya kuma jaddada burin rundunar sojin ƙasar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ƙasar.
Laftanar Janar Lagbaja ya ce sojojin ƙasar tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaron ƙasar na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da kare martabar ƙasar.
Babban hafsan sojin na wannan jawabi ne a daidai lokacin da ƙasashen ƙungiyar Ecowas suka bai wa sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum a Nijar wa'adin mako guda na su mayar da shi kan mulki su fuskanci tarin takunkumai, ciki har da na matakin soji.
- Sama da janar-janar 100 ne suka yi ritaya a rundunar sojin Najeriya
- Nawa ne alabashin ɗan sandan Najeriya? Abubuwan da ya kamata ku sani
Majalisar dokokin Senegal ta wanke wasu manyan 'yan adawar ƙasar biyu
Majalisar dokokin Senegal ta wanke wasu manyan 'yan adawar ƙasar biyu, inda ta ce a yanzu suna da damar tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar mai zuwa.
Majalisar ta kaɗa ƙuri'ar yafe wa mutanen biyu da a baya aka yanke wa hukuncin haramta tsayawa takara.
A yanzu dai majalisar ta amince Khalifa Sall, da kuma Karim Wadd - wanda aka haramta wa tsayawa takara a 2019 - za su iya tsayawa takara.
Jagoran 'yan adawan ƙasar Ousmane Sanko na fuskantar tuhuma kan aikata wasu laifuka da za su hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa.
An buƙaci alƙali ya taƙaita bayanan Donald Trump
Masu gabatar da ƙara a Amurka sun buƙaci wani alƙali ya taƙaita bayanan da Donald Trump zai riƙa bayyana wa jama'a, kan zargin da ake yi masa na yunƙurin sauya sakamakon zaɓen shugaban Amurka na 2020.
A yau Lahadi ne lauyan Mista Trump zai yi nazari a kan duk wata shaida da gwamnatin ke da ita a kan zargin da take yi wa tsohon shugaban na Amurka.
Masu gabatar da ƙarar sun ce idan har Mista Trump ya bayyana wasu daga cikin waɗannan shaidun, to tabbas hakan zai iya yin illa ga wasu daga cikin shaidun.
Sun bayar da misalin wani saƙo da toshon shugaban ƙasar ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ranar Juma'a, inda a ciki ya ce ''Idan kuka ce min kule, zan ce muku cas''.
To amma masu yaƙin neman zaɓen Trump, sun ce abin da tsohon shugaban ƙasar ya wallafa na nufin waɗanda suke sukarsa ne a cikin jam'iyyarsa ta Republican.
- Yadda zargin aikata lalata ke neman ɗaure Donald Trump
- Me zai faru bayan gurfanar da Trump?
Assalamu alaikum
Masu bin mu a wannan shafi barkan mu da hutun ƙarshen mako
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman Najeriya da Nijar.
Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.