Mu kwana lafiya
Nan muka zo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi.
Za mu zo muku da wasu ƙayatattu da suka shafi rayuwarku gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu zama lafiya daga Umar Mikail.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Nan muka zo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi.
Za mu zo muku da wasu ƙayatattu da suka shafi rayuwarku gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu zama lafiya daga Umar Mikail.
Wasu gine-gine da aka yi ba bisa kaida ba sun rushe a Tehran babban birnin Iran, inda mutum uku suka mutu.
'Yan sanda biyu na cikin waɗanda suka mutu, wasu 11 kuma suka jikkata.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce an ruguza wasu gine-gine da ke kusa da su.
Sanarwar 'yan sanda ta ce gine-ginen ba su bi ka'idojin tsaro ba.
Wani jami'i a Tehran ya ce sama da gine-gine 46,000 ne aka rushe a babban birnin kasar cikin shekara biyu da suka gabata.

Asalin hoton, Science Photo Library
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Nigerian Association of Resident Doctors (NARD) ta sanar da aniyar gudanar da zanga-zangar lumana kullum daga ranar Laraba.
Kazalika, ta ce mambobinta za su dinga yin cincirundo a bakin ma'aikatar lafiya, da ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, da kuma sakatariyar manyan ma'aikatun lafiya na jihohi.
Da take ba da sanarwar a ranar Asabar, NARD ta ce ta ɗauki matakin ne saboda ta matsa wa mahukunta duba buƙatun nata da ta ce an yi watsi da su.
A ranar 25 ga watan Yuli ƙungiyar ta fara yajin aikin sai baba ta gani a faɗin Najeriya. Daga cikin buƙatun nasu akwai neman biyan alawus-alawus da suka ce suna bin bashi.
A ranar 1 ga watan Agusta kuma gwamnatin tarayya ta ayyana tsarin "ba aiki ba albashi" a kan likitocin, abin da ke nufin duk likitan da ya ƙaurace wa aiki ba zai samu albashinsa a ƙarshen kowane wata ba.
Masana harkokin lafiyar abinci sun bayyana irin amfanin da ganyen zogale yake da shi a jikin ɗan Adam saboda sinadaran da yake ƙunshe da su.
Zainab Ujudud Sharif ta bayyana cewa bincike ya tabbatar zogale itace mai albarka matuƙa.
Itacen zogale kan fito har a wurin da babu ruwa, hakan ya sa ta ce ganyensa da sassaƙensa duka suna da amfani a jikin mutum.
"Yana da sinadaran A,B, C,D har da E ma. Kuma yana ɗauke da Calcium, Potassium," in ji ta.
Ta ƙara da cewa man zogale yana cikin mayukan da suka fi tsada a duniya.
Dubban 'yan Nijar ne suka taru a filin wasa na Général Seyni Kountche da ke birnin Yamai don nuna goyon bayansu ga sojojin da suka yi juyin mulki a ranar Lahadi.
Tun washegarin da sojoji suka yi juyin mulkin wasu suka fara zanga-zangar goyon baya da kuma ta adawa da su.
Lamarin na zuwa ne yayin da wa'adin da ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma ta bai wa sojojin ya cika - kan ko dai su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed kan mulki ko kuma su fuskanci ƙarfin soja.
Tuni mambobin ƙungiyar suka rufe iyakokinsu tare da yanke duk wata hulɗa da Nijar ɗin, yayin da ƙasashen Mali da Burkina Faso da Guinea suka ayyana goyon bayansu ga sojojin na Nijar ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani.
Najeriya, babbar ƙawar Nijar, ita ce ke jagaorantar yunƙurin tilasta wa sojojin.

Asalin hoton, Reuters
Arsenal ta kara wa fatanta na doke Manchester City a gasar Premier League kwarin gwiwa bayan ta lashe Community Shield a wasan da ta doke kungiyar ta Pep Guardiola 4-1 a bugun fenariti.
An tashi wasan 1-1 ba tare da buga ƙarin zagaye biyu na ƙarin lokaci ba.
Matashin dan wasan Mancherster City Cole Palmer ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal a minti na 70, kafin Leandro Trossard ya farke ta a minti na 101 bayan ƙara minti 8.
A haka wasan ya kai zuwa bugun Fenariti, inda Kevin de Bruyne da Rodri suka zubar ma City, sannan Fabio Vieira ya jefa wa Arsenal bugun karshe da ya tabbatar da nasarar tata.
Yanzu kungoyin biyu za su saurari fara gasar Premier ta bana a mako mai zuwa, inda Man City za ta kara da Burnley ranar Juma'a, ita kuma Arsenal ta karbi bakuncin Nottingham Forest ranar Asabar.

Asalin hoton, NYSC
Hukumar yi wa ƙasa hidima a Najeriya, National Youth Service Corps (NYSC), ta ce babu wani shiri da take yi na tura matasan masu hidimar ƙasa zuwa Jamhuriyar Nijar don yaƙar sojojin da suka yi juyin mulki.
Kakakin NYSC, Mista Eddy Megwa, ya ce sun musanta batun ne sakamakon wani bidiyo da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta, kamar yadda kamfanin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.
"Babu ƙanshin gaskiya a labarin da wani mai shirya barkwanci ya ƙirƙira," in ji shi. "Ya kamata masu yi wa ƙasa hidima da iyaye su yi watsi da batun, wanda aka shirya shi da zimmar tayar da zaune tsaye."
Ya ƙara da cewa jami'an tsaro za su kama wanda ya ƙirƙiri bidiyon.
A ranar Juma'a ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi goyon bayan majalisar ƙasar don tura sojoji ƙarƙashin ƙungiyar Ecowas zuwa Nijar don su tilasta wa sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum komawa kan tsarin mulki.
Sai dai majalisar ba ta goyi bayan ƙudirin ba, tana mai ba da shawarar a ci gaba da yunƙurin tattaunawa ta hanyar difilomasiyya.

Asalin hoton, NDLEA
Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA sun kama wasu mutum biyu, da suka yi ƙaryar cewa ma'auta ne da ke da niyyar zuwa Indiya domin rashin lafiya da hodar-ibilis.
Mutanen biyu Mista Ilonzeh Kingsley Onyebuchi da Misis Ilonzeh Roseline Nonyelum, an kama su ne da ƙulli 184 na hodar-ibilis da nauyinta ya kai kiligiram 3.322, an kuma gano wata ƙwayar mai nauyin giram 100 ɓoye a ɗan kamfan matar.
Jami'an NDLEA sun kama mutanen biyu a wurin binciken kayayyaki na farko a filin jirgin sama na Legas, a lokacin da suke ƙoƙarin shigar jirgi zuwa Indiya.
Duk da cewa sunayen da ke jikin takardun tafiyarsu ya nuna cewa ma'aurata ne, hukumar NDLEA ta buƙaci dauki hoton jikinsu.
Hoton da ya tabbatar da cewa akwai hodar-ibilis ɗin a hjikin nasu, a don haka ne jami'an hukumar suka kai wa wani ɗakin gaji domin tilasta musu fito da abin da suka ɓoye a jikin nasu.
Yayin da sunayen da ke jikin takardun tafiyarsu ya nuna suna iri daya, watao Ilonzeh Kingsley Onyebuchi ga manijin, da matar Ilonzeh Roseline Nonyelum, binciken farko da hukumar ta gudanar ya gano cewa mutanen ba ma'aurata ba ne.
Binciken ya nuna cewa sun yi amfani da suna ɗaya domin kawar da hankalin jami'an tsaro a wajen bincike.
Sunan matar na gaskiya shi ne Ngogbike Nkechi kamar yadda bincken ya bayyana.
Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Moroko ya yi sanadin mutuwar mutum 24, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito.
Lamarin ya faru a yankin Azilal mai nisan kilomita 310 daga babban birnin ƙasar Rabat.

Asalin hoton, Facebook/Ganduje/Shetty
Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce wasu 'yan ba-ni-na-iya ne suka bayar da sunan Maryam Shetty don naɗa ta minista daga Kano, ba tare da saninsa ba.
Sai dai, ya ce shugaban ƙasa yana da damar naɗa mutanen da yake son tafiya da su a muƙaman ministoci daga jihohin ƙasar bisa la'akari da tsare-tsarensa da ƙwarewar mutanen da kuma sauran buƙatu.
A wata hira da ya yi da wasu kafofin yaɗa labarai ciki har da Freedom Radio ranar Asabar, tsohon gwamnan, wanda shi ne jagoran jam'iyyar a Kano, ya ce ba shi da cikakkiyar masaniya a kan Maryam Shetty, hasali ma ba su santa ba a matsayinsu na jagororin APC daga Kano.
Don haka ''ka ga ba mu da wani ma'auni da za mu ce za ta iya, ko ba za ta iya wannan aiki ba idan aka nemi shawararmu''.
Ganduje ya ce martanin da mutane suka yi ta bayyanawa a shafukan sada zumunta, shi ma ya taka rawa wajen ɗaukar matakin sauya sunan Dakta Maryam Shetty, bayan wasu sun riƙa nuna cewa ba za ta iya riƙe muƙamin minista a Najeriya ba kasancewar ba ta taɓa riƙe wani muƙamin gwamnati ba.
Shugaban na APC ya ce da haka ne labari ya je har wajen shugaban ƙasa, wanda ya kira Ganduje don jin shawararsa.
''Ya ce min ga fa abin da ke faruwa, shin kai ka bayar da sunanta? Sai na ce masa a'a sam sam, ba ni ba ne, ban ma sani ba, daga nan ya ce to ya ka gani? akwai buƙatar a canja?, sai na ce masa ƙwarai da gaske kuwa'', in ji tsohon gwamnan na Kano.
Ganduje ya ce muƙamin minista, matsayi ne da ke buƙatar dattaku da sani (ƙwarewa), sannan yana buƙatar taka muhimmiyar rawa wajen kafa gwamnati a siyasance.
''To idan ka auna waɗannan abubuwa kuwa, ai mu ya kamata a tambaya, in dai ana so a bayar da wakilci daga jihar Kano'', in ji shi.
Ya ce ko da wani can ya bayar da wata shawara, to ya kamata a tuntuɓe su , idan ya dace sai su ba da goyon baya.
Cire sunan Maryam Shetty daga jerin ministocin Shugaba Tinubu, kamar bayyana sunanta a cikin waɗanda za a naɗa tun farko, ya yi matuƙar janyo muhawara musamman a tsakanin matasa da matan ƙasar.
Da yawa suna cewa abin da aka yi ya nuna rashin dacewa da kuma hangen nesa.

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar matan Netherlands ta samu nasarar tsallakawa zuwa wasan dab da kusa da ƙarshe a gasar Kofin Duniya ta Mata, bayan da ta doke Afirka ta Kudu da ci 2-0.
Matan na Netherlands su ne suka zo na biyu a wasan cikin rukuni a gaban Amurka wadda ke riƙe da kofin.
A yanzu tawagar ta matan Netherlands za ta kara da Sifaniya wadda ta doke Switzerland 5-1 a ranar Asabar.

Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla fasinjoji 15 ne suka mutu yayin da wasu 50 suka jikkata bayan da wani jirgin ƙasa ya sauka daga kan hanyarsa a kudancin Pakistan.
Tuni a ka kai mutanen da suka jikkata asibiti domin ba su kulawar gaggawa.
Wani jami'in jirgin ƙasan ya ce jirgin na kan hanyarsa ne daga birnin Karachi zuwa Abbottabad a lokacin da hatsarin ya auku.
Tawagar jami'an ceto ta hallara a wajen domin kuɓutar da fasinjojin da suka maƙale.