Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tinubu ya sanar da Majalisar Dokoki aniyar tura dakaru zuwa Nijar
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Badamasi Abdulkadir Mukhtar, Umar Mikail and Rabiatu Kabir Runka
Donald Trump ya musanta tuhumar murɗe zabe
Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya musanta zargin da ake masa na neman murɗe sakamakon zaɓen 2020 da ya sha kayi.
Da ya bayyana a kotun birnin Washington, Mr Trump ya yi bayanin cikin sanyin murya, inda ya jaddada cewa bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.
Ya shaidawa manema labarai cewa an gurfanar da shi ne saboda dalilan siyasa.
Wannan ne karo na uku da tsohon shugaban ƙasar ya bayyana a gaba kotu kan zargin aikata manyan laifuka. .
An ga Mr Trump yana dunƙule tafin hannunsa yayin da yake zaune a cikin kotun, ya kuma riƙa girgiza kai lokacin da ake karanto tuhumar.
Cutar mashaƙo ta kashe ƙananan yara 122 a Najeriya - Unicef
Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (Unicef) ya ce cutar mashaƙo ta kashe yara 122 a Najeriya ya zuwa watan Yuli.
Jami'ar yaɗa labaran asusun a Najeriya, Ms Safiya Akau, ta ce UNICEF yana ƙara ƙokarin hana yaɗuwar cutar wadda ta shafi ƙananan yara a jiha 27.
Mashaƙo cuta ce mai sarƙe numfashi kuma mai kisa.
Ms Akau ta ce daga cikin gwaji 3,850 da aka yi cikin watan Yuli, an tabbatar cewa mutum 1,387 na ɗauke da cutar.
Ta ce kashi 98 na masu cutar sun fito ne daga jihohin Kano da Yobe da Katsina da Legas da Sokoto da Zamfara da kuma Birnin Tarayya, Abuja.
Ta kuma yi nuni da cewa kashi 71.5 na masu ɗauke da cutar ƙananan yara ne ƴan shekara biyu zuwa 14.
Gwamnan Adamawa Fintiri ya naɗa mataimaka 47 a fannin yaɗa labarai
Gwamnan jihar Adamawa da ke arewacin Najeriya, Ahmadu Umaru Finitiri, ya naɗa mutum 47 a matsayin masu taimaka masa a fannin yaɗa labarai 47.
Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta bayyana tawagar mutanen a matsayin "mai ƙunshe da mabambantan mutane da al'adu kuma masu ƙwazo".
Ma'abota shafukan sada zumunta a Najeriya na ci gaba da sukar gwamnan game da yawan mataimakan, waɗanda dukkansu za su yi aiki a fannin yaɗa labarai kawai.
Ga jerin sunayen hadiman nasa:
1. Dr. John Ngamsa
2. Babayola Tongo
3. George Kushi
4. Ijafiya Domiya
5. Sherif Alhassan
6. Muhammed Tukur
7. Nurudeen Kama
8. Pius Iliya
9. Awal Hamza
10. Thomas Terry
11. Barrister Sunday Wugirah
12. Victor Dogo
13. Mohammed Faisal
14. Miracle Musa
15. Abubakar Idris
16. Nafiu Abubakar
17. Prince Solomon Yakubu Tumba
18. Abdullahi Damare
19. Vandi Yusuf
20. Emmanuel Tumba
21. Jonathan Jude
22. Auwal Hamza
23. Jamila Tanko
24. Mohammed Rayan Yunuda
25. Paul Barnabas
26. Suleiman Garga
27. Zailani Abba Kawu
28. Elijah Sambo
29. Benan Wyclif
30. Nasir Kasim
31. Wali Ibrahim Facebook
32. Mamse Adamu
33. Muhammed Girei
34. Sani Garta
35. Emmanuel Lakami
36. Ibrahim Assad
37. Musa Elson
38. Hierarchy Harold
39. Micah Simon Tihze
40. Jameel Kolere
41. Joan Daniel
42. Jibril Musa
43. Halima Bala
44. Nacha Waziri
45. Ahmadu Hamidu
46. Ijabani Ijahu
47. Hamanbello Idris
Habasha na shirin kafa dokar ta-ɓaci a yankin Amhara
Majalisar zartarwar Habasha ta amince da kafa dokar ta-ɓaci a yankin Amhara bayan shafe kwanaki ana faɗa tsakanin sojin ƙasar da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
Matakin na zuwa ne kwana ɗaya bayan shugaban yankin, Yilkal Kefale, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta ɗauki mataki, yana mai cewa ''hukumomin tsaro sun kasa tabbatar da doka a yankin''.
Rahotanni sun ce ƙungiyar mayaƙa ta Fano ta ƙwace iko da ƙauyuka da dama da kuma wasu manyan birane.
An katse layin waya, an kuma taƙaita sufurin jiragen sama a wasu biranen yankin.
Sanarwar da ofishin firaministan ƙasar ya fitar ta ce akwai buƙatar saka dokar ta-ɓaci domin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Dole sai majalisar dokokin ƙasar ta amince kafin a ɗauki matakin kafa dokar ta-ɓacin.
Sojojin mulkin Nijar sun gargaɗi kasashen Ecowas
Sabuwar gwamnatin sojin Nijar ta ce za ta mayar da martani ba tare da bata lokaci ba ga duk wata takala ko yunkurin takala daga kasashen Afirka ta Yamma.
Gargadin ya zo ne kwana uku kafin karewar wa'adin da kungiyar Ecowas ta ba wa Nijar din na a dawo da kasar kan turbar tsarin mulki.
Sojojin sun ce sun soke wasu yarjejeniyoyin soji da aka kulla tsakanin Shugaba Bazoum da Faransa bayan sun karbe ikon kasar.
Jakadan Nijar a Amurka, Kiari Liman Tinguiri wanda sojojin suka kora, ya ce ''idan Nijar ta durkushe to baki dayan yankin Sahel abin ya shafa, sannan yankin zai fuskanci babbar matsala, idan kuwa har aka samu matsala a yankin to kare kasashen ma zai yi matukar wuya''.
Cikin mukalar da ya rubuta a jaridar Washington Post, Shugaba Bazoum ya ce an yi garkuwa da shi inda ya yi kira ga Amurka da ma sauran kasashen Yamma a kan su taimaka a dawo da kasar kan turbar tsarin mulki.
Ya kuma yi gargadin cewa muddin aka bari juyin mulkin kasar ya yi tasiri to hakan zai haifar da mummunan sakamako.
Assalamu alaikum
Ma'abota BBC Hausa barkan mu da safiyar Juma'a.
Badamasi Abdulkadir Mukhtar ne ke farin cikin kasancewa da ku a wannan lokaci.
Ku ci gaba da bibiyar mu domin kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.
Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta don tafka muhawara a kan labaran da muka wallafa.