Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Tinubu ya sanar da Majalisar Dokoki aniyar tura dakaru zuwa Nijar

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Badamasi Abdulkadir Mukhtar, Umar Mikail and Rabiatu Kabir Runka

  1. Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin samun ƙaruwar hare-haren Yahudawa

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin samun ƙaruwar hare-haren Yahudawa ƴan kama wuri-zauna a kan Falasɗinawa a yankin Gabar-Yamma, da Isra'ila ta mamaye.

    Majalisar ta ce zuwa yanzu an kai irin waɗannan hare-hare har dari shida kusan ƙarin kashi 40 cikin dari, idan aka kwatanta da bara.

    Rahoton Majalisar ya ce, an kori Falasɗinawa da dama daga muhallinsu, kuma suna fuskantar barazanar rushe gidajensu daga hukumomin Isra'ila.

  2. Ecowas ta amince da tsarin ɗaukar matakin soji kan Nijar

    Ƙasashen Yammacin Afrika sun amince da wani tsari na ɗaukar matakin soji kan Nijar, idan har sojojin da suka yi juyin mulki suka ƙi amincewa da sharaɗin dawo da hamɓarren shugaba, Mohamed Bazoum bisa karagar mulkin.

    Tun da farko ECOWAS ta bai wa sojojin na jamhuriyar Nijar wa'adin ranar Lahadi su mayar da mulki ga farar hula.

    Alamu na nuna cewa sojojin Ecowas sun ƙagu da su ƙaddamar da yaƙi a Nijar idan har hakan ya zama dole.

    Yanzu haka dai, Najeriya ta rufe iyakokin ƙasar da Nijar, ta kuma yanke wutar da take bai wa Nijar din duk a lokaci guda, matakan sun haddasa tashin farashin kayan masarufi a ƙasar, hakan na nuna yadda matakan Ecowas ɗin za su haddasa wahalhalu ga ƴan ƙasar.

    A ranar Alhamis wata tawaga ta kungiyar ta je Nijar, domin shiga tsakani sai dai ba ta samu damar ganawa da shugaban mulkin sojin ba, da ma hamɓararren shugaban na farar hula.

    Masu aiko da rahotanni sun ce, ɗaukar matakin soji kan lamarin zai iya zama mai wahala sosai, saboda kayan aiki, da kuma hadari, domin zai iya kara dagula al'amura a yankin, wanda masu ikirarin jihadi ke yi wa ta'annati.

  3. Sudan: Dakarun RSF sun ƙwace Dafur

    Ƙungiyar dakarun kar-ta-kwana, Rapid Support Forces ko RSF, wadda ke yaƙi da rundunar sojin Sudan ta ce ta ƙwace iko da jihar Darfur.

    An yi ta gwabza faɗa a babban birnin jihar, Zalingei, sai dai BBC ba ta iya tabbatar da cewa kungiyar ta yi galaba a kan sojojin ba.

    Darfur da ke yammacin ƙasar ta Sudan ta yi fama da mummunan faɗa, bayan babban birnin ƙasar, Khartoum, tun da yaƙi ya ɓarke a tsakiyar watan Afrilu.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yaƙin na Sudan ya raba sama da mutum miliyan uku da muhallinsu, a fadin kasar.

  4. Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan cire Maryam Shetty daga jerin ministoci

  5. Habasha ta ayyana dokar-ta-ɓaci a yankin Amhara

    Gwamnatin Habasha ta ayyana dokar-ta-ɓaci a yankin Amhara bayan kwanakin da aka kwashhe ana mummunan faɗa tsakanin sojoji da mayaƙan sa-kai.

    Ofishin Firaminitan ƙasar ya ce yanayin zama na tsarin mulki na fuskantar barazana a Amhara a don haka ya wajaba a dauki matakin.

    Wakilin BBC ya ce "Tun da farko Shugaban yankin, na Ahamara Yilkal Kefale, ya nuna cewa yanayin tsaro ya tabarbare, a don haka ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka."

    Faɗan ya karkata zuwa birane biyu kuma an katse layukan sadarwa, abin da ya sa yake da wuya a iya sanin ainahin abin da ke wakana a yakin.

  6. Faransa ta yi watsi da matakin Nijar na katse hulɗar soji

    Faransa ta yi watsi da matakin da gwamnatin Nijar ta ɗauka na soke yarjejeniyoyin soji da aka ƙulla tsakanin shugabannin ƙasashen biyu.

    Faransa ta ce waɗanda suka yi juyin mulki ba su da ƴancin soke yarjeniyoyin.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce "Tsarin doka na yarjejeniyar tsaro da Faransa ta kulla da Nijar ya dogara ne kan yarjejeniyoyin da aka rattaba wa hannu da halastattun hukumomin Nijar."

    Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Nijar ta sanar a ranar Juma'a cewar ta soke yarjejeniyar soji da diflomasiyya da Faransa, da Togo, da Najeriya da kuma Amurka.

  7. Rasha ta yi gargaɗi ga ƙasashen Yamma kan juyin mulkin Nijar

    Fadar Kremlin ta ce duk wani yunƙurin shiga batun juyin mulkin Nijar daga ƙasashen da ba na Ecowas ba zai ƙara lalata lamarin.

    Kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov ne ya faɗi hakan sa'ilin da yake tsokaci kan kiran da hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya yi, na neman Amurka da sauran ƙasashen duniya su ɗauki matakin dawo da mulkin farar hula a ƙasar.

    Ya ce "Babu wata alama cewa shigar ƙasashen da ba na Afrika ba za su iya kawo mafita kan halin da ake ciki,"

    Ya ƙara da cewa "Muna sanya ido kan abubuwan da ke faruwa, kuma mun damu da halin tsoron da ake ciki a Nijar, muna kuma goyon bayan duk wani mataki na samar da zaman lafiya da tsaron jama'a a ƙasar,"

  8. Shugaban Kwastam ya isa Katsina don tabbatar da rufe bodar Najeriya da Nijar

    Muƙaddashin shugaban hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya, Bashir Adewale, ya isa jihar Katsina domin tabbatar da umurnin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu na rufe iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

    Shugaban hukumar Bashir Adewale ya ce ya zo jihar ne domin cika duk wani umurnin da shugaban ƙasar ya bayar kasancewar sa shugaban ECOWAS.

    Ya ce "Da zarar abubuwa suka tafi yadda ake so yana da tabbacin za a sake buɗe iyakokin."

  9. Matawalle ya sha yabo wajen sanatoci lokacin tantancewa

    Sanatoci ba su yi tambayoyi ga Bello Matawalle ba a wajen tantance shi a matsayin minista daga jihar Zamfara.

    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Barau Jibril ya ce Matawalle mutum ne mai ƙima saboda haka ya bayar da shawarar ya yi gaisuwa ya wuce.

    A lokacin da Matawalle ya kammala bayani kan rayuwarsa, Sanata Abdula'aziz Yari ya yaba tare da buƙatar majalisa ta amince da tsohon gwamnan na Zamfara ba tare da yi masa wasu tambayoyi ba.

    Sauran waɗanda suka yaba wa Matawalle sun haɗa da Kawu Sumaila, da Abdula-Azeez Ƴar'adua da kuma Sanata Ali Ndume.

    Matawalle tsohon gwamnan jihar Zamfara ne da ya sha kaye wajen jam'iyar adawa ta PDP.

    Baya ga Matawalle, Majalisar Dattawar ta kuma tantance wanda shugaba Tinubu ya sanya sunansa daga jihar Kebbi, wato Tanko Sununu.

    Shi ma Sununu, wanda ɗan majalisar wakilai ne na tarayya bai fuskanci wasu tambayoyi daga ƴan majalisar ba.

  10. Bagudu bai fuskanci tambayoyi a majalisa ba

    Majalisar dattawan Najeriya ta tantance tsohon gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu a matsayin minista daga jihar Kebbi.

    Bagudu bai fuskanci tambayoyi a majalisa a lokacin da ake tantance shi ba, la'akari da cewa tsohon mdan majalisar dattawan ƙasar, kamar yadda sanatocin ska bayyana.

    Tsohon gwamnan jihar Kebbin ya yi gaisuwa ne kawai ya wuce kamar yadda shugaban majalisar dattawa ya ba shi dama.

  11. Tasirin yarjejeniyar tsaro da Nijar ta soke da Faransa

  12. Tinubu ya sanar da Majalisar Dokoki aniyar tura dakaru zuwa Nijar

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa majalisar dokokin Najeriya matsayar da ƙungiyar Ecowas ta cimma kan ɗaukar matakin soji a kan Nijar da kuma sauran takunkuman da aka ɗauka na ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki.

    Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya sanar da saƙon shugaban ƙasar inda ya karanto kai tsaye daga wasikar shugaba Tinubun.

    Wasikar na cewa “Bayan abin takaicin da ya faru a Nijar inda aka hamɓarar da shugaban ƙasa, Ecowas a ƙarƙashin jagorancina ta yi Allah-wadai da juyin mulkin kuma ta amince da ɗaukar matakan dawo da Nijar kan turbar dimokuraɗiyya. A wani mataki na dawo da zaman lafiya a ƙasar Ecowas ta fitar da matsaya.

    “Za a rufe duk iyakokin Nijar da ƙasashenmu da kuma sanya ido don tabbatar da cewa an yi biyayya ga matakin.

    “Yanke wutar lantarkin da ake kaiwa Nijar da neman goyon bayan ƙasashen duniya wajen aiwatar da matsayar ƙungiyar Ecowas da kuma datse sufurin jirgin sama daga cikin Nijar da ma wanda zai shiga ƙasar.

    “Rufe hanyoyin shigar da kaya Nijar daga Legas da kuma wayar da kan ƴan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta game da shirin ɗaukar matakin soji a kan sojojin Nijar ɗin.''

  13. Jirgin Ukraine ya kai wa jirgin ruwan Rasha hari a Bahar Aswad

  14. Nijar ta katse hulɗa da Najeriya

    Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yanke hulɗa da Najeriya da Togo da Amurka da kuma wadda ta raine ta, Faransa bayan tawagar da Ecowas ta tura don tattaunawa da sojojin da suka hamɓarar da shugaba Bazoum ta gaza samun matsaya da sojojin.

    A wani jawabi da ya yi ta kafar yaɗa labaran ƙasar ta Nijar, jagoran juyin mulkin, Kanar Amadou Abdramane ne ya sanar da matakin da ma wasu matakan da suka ɗauka.

    Ya ce “Mun kawo ƙarshen duk wata hulɗar jakadanci da Najeriya da Faransa da Togo da kuma Amurka. Duk wata matsaya da aka cimma a baya ta rushe.”

    Tawagar da Ecowas ta tura don tattaunawa da sojojin Nijar ɗin a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar ta gana da wasu daga cikin sojojin a ranar Alhamis amma ba a cimma wata matsaya ba.

    Manyan hafsoshin sojin ƙasashen Ecowas sun kammala wani taro a birnin Abuja, inda suka tattauna yiyuwar ɗaukar matakin soji a kan Nijar idan sasanci ya gagara.

  15. Chelsea ta sayi Disasi daga Monaco

  16. Brighton ba ta da niyyar sayar da Caicedo a wannan bazarar

  17. Ministocin Tinubu: Majalisa ta tantance ƙarin mutum uku

    Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance ƙarin mutum uku daga cikin waɗanda Shugaba Tinubu ya nemi amincewarta don naɗa su ministoci.

    Mutanen da aka tantance sun haɗa da Sanata Ibrahim Geidam, tsohon Gwamnan Yobe, da Sanata Aliyu Sabi Abdullahi daga jihar Neja da kuma Sanata Heineken Lokpobori daga jihar Bayelsa.

    Majalisar ta nemi su yi gaisuwa ne kawai su fita bayan sun gabatar da taƙaitaccen tarihinsu, kasancewar sun taɓa zama ƴan majalisa kuma kundin aikin Majalisar Dattawa ya amince da hakan.

    Suna cikin ƙarin mutum 19 da Tinubu ya aika wa Majalisar ranar Laraba.

  18. Majalisa ta tantance Adegboyega Oyetola

    Majalisar dattawan Najeriya ta ci gaba da zaman tantance mutanen da shugaba Bola Tinubu ya aike mata don neman amincewa ya naɗa su ministoci.

    A zaman na ranar Juma'a, majalisar ta fara ne da tantance tsohon gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola.

    Wannan ne zaman majalisar na huɗu a kan wannan aiki na tantance ministoci.

  19. Kotun ƙolin India ta hana zartar da hukunci kan Rahul Gandhi

    Kotun ƙolin India ta hana aiwatar da hukunci kan jagoran adawa, Rahul Gandhi wanda a baya aka samu da laifin cin mutumcin firaminista Nerandra Modi.

    Kotu ta yanke mashi hukuncin shekara biyu a gidan yari a cikin watan Maris kan kalaman da ya furta game da sunan mahaifin firaministan ƙasar, lokacin da yake jawabi wajen ganganmin neman zaɓe a 2019.

    Bayan hukuncin kotun ne aka dakatar da Mr Gandhi daga majalisar.

    Hukuncin da kotun ƙolin ta bayar ranar juma'a zai bashi damar komawa majalisa da kuma tsayawa takara a zaɓen shekara mai zuwa.

    Kotun ƙolin ta yi nuni da cewa dalilan da alƙalin da ya yanke wa Mr Gandhi hukuncin shekara biyu ya bayar basu da ƙwari.

    Kotun ta kuma ja hankalin Gandhi a kan kiyaye kalaman da yake furtawa.

  20. Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty a jerin ministocinsa