Najeriya ta sayi allura 50,000 don yi wa dabbobi riga-kafin cutar Anthrax a jihar Naija
Gwamnatin Najeriya ta aike da allurar riga-kafin cutar Anthrax 50,000 zuwa jihar Naija da ke tsakiyar kasar.
Cikin wani sakon Twitter da gidan talbijin na ƙasar NTA ya wallafa ya ce za a yi wa dabbobi riga-kafin cutar ne a yankin ƙaramar hukumar Suleja da ke jihar.
Haka kuma ita ma gwamnatin jihar Naijan ta sayi allurar riga-kafin cutar kusan 40,000 domin gudanar da aikin yi wa dabbobin riga-kafi.
Dabbobi na gida da na daji na kamuwa da cutar ne idan suka shaƙe ta daga ƙasa wadda ke ƙunshe da ƙwayoyin cutar ko kuma suka ci ciyawa ko shan ruwan da ke ɗauke da ita.
Dabbobin da suka fi kamuwa da cutar sun haɗa da shanu da tumaki da awaki da kuma barewa.
Haka kuma likitoci sun ce mutane na kamuwa da cutar a lokacin da suka yi cuɗanya da dabbobin da ke ɗauke da cutar ko kuma suka taɓa wani abu da ya fito daga jikin dabbobin.
A baya-bayan nan dai hukumomin Najeriya sun bayyana ɓuallar cutar a jihar ta Naija, lamarin da ya sa hukumomin lafiyar ƙasar yin gargaɗi game da cin naman dabbobin da ba su da lafiya.
Tuni hukumomi a wasu ƙasashe maƙwabtan Najeriya suka ayyana ɓarkewar cutar, kamar Ghana.
- Mece ce cutar Anthrax kuma ta yaya ake kamuwa da ita?
- Gwamnatin Ghana ta hana cin nama tsawon wata ɗaya a wani yanki