Jagoran 'yan adawar Kenya Raila Odinga ya ce "mura mai tsanani" ce ta hana shi shiga zanga-zangar da aka shafe kwanaki uku ana yi kan tituna da ake yi akan tsadar rayuwa da ƙarin haraji.
"Ba lallai ba ne ganin shugabannin 'yan adawa a kan tituna," Mr Odinga ya shaida wa wani gidan talabijin na Kenya game da zanga-zangar da za a kawo karshen shi a yau.
Gogaggen dan siyasar, wanda ya sha kaye a zaben shugaban kasa da aka yi ta ce-ce-ku-ce a bara, ya ce zanga-zangar neman canji ta al'umma ce ba tasa ba shi kadai.
Ya musanta rade-radin rashinsa wata dabara ce ta kulla yarjejeniya da shugaba William Ruto, inda ya kara da cewa ba ya neman shiga wani bangare na gwamnati.
"Ba mu yi ba, kuma ba za mu nemi 'tsarin musafaha' ba," in ji jagoran 'yan adawar yayin da yake magana kan sunan yarjejeniyar da ya kulla da tsohon shugaban kasar, Uhuru Kenyatta.
A nasa bangaren shugaba Ruto ya dage kan cewa ba zai shiga tattaunawa da Mr Odinga domin warware rikicin da ke faruwa a yanzu ba.
A ranar Alhamis din da ta gabata, ya yaba da martanin da ‘yan sandan suka yi – Shugaban ‘yan sandan ya ce zanga-zangar barazana ce ga tsaron kasa tare da tura jami’an kwantar da tarzoma a fadin kasar.
Sai dai wasu da dama sun soki yadda jami'an tsaro ke fuskantar masu zanga-zangar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Mutane kalilan ne suka shiga zanga-zangar adawa da gwamnati a wannan makon idan aka kwatanta da zanga-zangar da aka yi a baya. Mutane da yawa sun zauna a gida a ranakun Laraba da Alhamis, saboda fargabar tashin hankali.
Amma da alama abubuwa sun dawo daidai ranar Juma'a tare da sake buɗe makarantu da kasuwanci.
Manyan tashoshin mota a babban birnin kasar, Nairobi, da sauran garuruwa na ci gaba da aiki a hankali.