Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tinubu ya ba da umarni a sake nazari kan shirin tallafin N8,000
Wannan shafi ne da yake kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Ahmad Tijjani Bawage and Rabiatu Kabir Runka
Ronaldo ba zai sake komawa taka leda a nahiyar Turai ba
Gwamnan Taraba ya kafa kwamiti domin ƙwato kadarorin gwamnati
Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya kafa kwamiti da zai yi duba da kuma ƙwato kadaron jihar a faɗin Najeriya.
An ɗora wa kwamitin alhakin bincikowa da kuma gano kadarori a jihar Kaduna da ofishin jihar ta Taraba da ke Legas da kuma Abuja, babban birnin ƙasar.
A cewar sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar Gebon Kataps ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an ɗora kwamitin nauyin nema da kuma gano inda kowane irin nau'in kadarorin gwamnatin suke a faɗin ƙasar.
Ya ce kwamitin zai kuma ƙimar kuɗin kowace kadara da kuma bai wa gwamnatin jihar shawarwari.
Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa cikin makonni huɗu.
Dakarun RSF sun karɓe iko da wani gari a kudancin Darfur
Dakarun RSF da ke faɗa da sojojin Sudan, sun kwace iko da wani gari a kudancin yankin Darfur.
An kuma ruwaito cewa suna aikata laifukan take hakkin ɗan adam a garin.
Artabu tsakanin dakarun na RSF da sojoji ya tilasta wa dubban iyalai tserewa garin Kas.
Akwai rahotanni da ke cewa mayakan RSF na satar kayan abinci a kasuwanni da kuma lalata gine-ginen gwamnati.
Dakarun RSF na far wa al'ummomi da ba Larabawa a faɗin Darfur tun bayan ɓarkewar faɗa a tsakiyar watan Afrilu.
Ana ci gaba da gwaɓza faɗa a Khartoum, babban birnin Sudan da kuma wasu yakunana da dama yayin da ake ƙasashen duniya ke ƙoƙari wajen shiga tsakani domin kawo karshen rikicin.
An taɓa samun irin wannan rikici a ƙasar shekaru 20 da suka gabata, lokacin da aka tura wasu mayaƙa don murkushe ƴan tawaye. Yaƙin ya yi sanadiyyar rayukan mutane kusn 300,000.
Ba mu janye wa tsofaffin gwamnoni masu ba su tsaro ba - Rundunar Ƴan Sanda
Hukumar ƴan sandan Najeriya ta musanta labarin da ke cewa ta janye jami'anta waɗanda ke aikin kare wasu tsofaffin jami'an gwamnati.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce mutane su yi watsi da sanarwar saboda karya ce tsawgwaronta.
Ta ce a sanarwar da aka fitar, an nuna sanya hannun mataimakin kwamishinan yan sanda mai muƙamin DCP, wanda shi kaɗai zai nuna cewa karya ce saboda irin wannan, mataimakin kwamishinan ƴan sanda mai muƙamin ACP ne ya kamata ya sanya hannu.
Muƙaddashin Sifeton Ƴan Sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun, ya ce za su gudanar da bincike domin gano waɗanda suka fitar da sanarwar domin su fuskanci hukunci.
Dole ne mu dakatar da kai agaji Haiti saboda raguwar tallafin kuɗi - WFP
Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce dole ne ya dakatar da taimakon gaggawa da ya ke a Haiti saboda raguwar tallafin kudin da ya ke samu.
Dakatarwar za ta shafi dubban mutane a watan nan, a cewar shirin.
Mai magana da yawun shirin, Jean Martin Bauer, ya bayyana dakatarwar a matsayin abin da bai ji daɗinta ba.
Ya kuma bukaci kungiyoyin agaji na duniya da su yunkuro don ceton rayuwar mutane da dama.
Ya ce kusan rabin al'ummar Haiti sun dogara ne a kan abincin da ake bayar wa na tallafi a kullum don tsira da rayuwarsu.
Ƙasar dai na fama da matsaloli da dama abin da ake gani kashe shugaban ƙasar Jovenel Moise shekaru 2 da suka wuce ne ya haddasa.
Ana ci gaba da fuskantar tsananin zafi a kudancin Turai
Ana ci gaba da fuskantar tsananin zafi a kudancin Turai, a yayin da ake kyautata tsammanin yanayin da ake ciki a tsakiyar Mediterranean zai karu daga yau.
Masu hasashen yanayi sun ce yanayin da ake ciki a tsibirin Sardinia na ƙasar Italiya ya kai digiri 46 a ma’aunin Celsius.
Ana ta gargaɗi a kan cewa za a ci gaba da fuskantar tsananin zafi a Italiya har nan da kwanaki 10 masu zuwa.
Ana kuma tsammanin fuskantar tsananin zafin a wasu sassan Sifaniya.
Akwai rahotanni ɗaukewar wutar lantarki a wasu yankuna saboda karuwar bukatar na’urar sanyaya ɗaki wato AC.
Rasha ta sake buɗe gadar da ta haɗe ƙasar da yankin Crimea
Gwamnatin Rasha ta ce ta ɗan sake buɗe gadar da ta haɗe ƙasar da kuma yankin Crimea da ta mamaye, kwana guda bayan wani hari da aka kai ya lalata.
Mataimakin Faraiministan ƙasar Marat Khusnullin, ya ce an bar motoci na farko sun wuce ta titi guda da ke gadar inda suka tsallaka zuwa yankin Kerch.
Ya ce "yana fata za a buɗe sauran titunan da ke kan gadar zuwa nan da tsakiyar watan Satumba.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa za su mayar da harin ramuwar gayya a kan abin da ya kira harin ta'addancin da aka kai kan gadar.
Buɗewa
Ma'abota BBC Hausa barkan mu da safiyar Talata.
Ahmad Tijjani Bawage da Rabiatu Kabir Runka ke farin cikin kasancewa da ku a wannan shafi na kai-tsaye.
Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da kuma sauran sassan duniya.