Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kotu ta bayar da umarnin sakin tsohon kwamishinan Ganduje

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mayaƙan Wagner na horas da sojojin Belarus

    Cikin wata sanarwa da Belarus ta fitar, ta ce sojojin hayar Wagner sun fara horar da dakarunta

    Sanarwar ita ce tabbaci na farko a hukumance cewa wasu mayakan Wagner sun koma Belarus, makonni bayan tutsun da suka yi a Rasha.

    Wani bidiyon ma'aikatar tsaron ƙasar ya nuna wasu mutane sanye da takunkumi na horar da wasu sojoji.

    Bidiyon bai yi ƙarin bayani game da adadin mayaƙan na Wegner da ke Belarus ba.

    Dama shugaba Alexender Lukashenko ne ya miƙa tayin karbarsu, a wani ɓangare na yarjejeniyar kawo ƙashen boren da suka yi wa Moscow.

    Ukraine ta ce tana sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Belarus, sai dai ba ta hango wata barazana ba zuwa yanzu.

    • Shin juyin mulki Wagner ke yunƙurin yi wa Putin?
    • Dole mu gurfanar da mayaƙan Wagner a gaban kuliya - Putin
  2. Marabanku

    Masu bin mu a wannan shafi barkan mu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muhawara

    Ku biyo mu...