Rufewa
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye.
Sai kuma gobe Lahadi - idan Allah ya kai mu za mu dawo da sabbin labarai.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye.
Sai kuma gobe Lahadi - idan Allah ya kai mu za mu dawo da sabbin labarai.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Belarus ta sanar da cewar mambobin kungiyar sojojin haya na Rasha Wagner sun fara horar da dakarunta.
Wannan dai shi ne karon farko da Belarusa ta tabbatar da komawar wasu dakarun Wagner ƙasar a hukumance.
Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin shugaban ƙasar Belarus Alexander Lukashenko da Vladmir Putin.
Sai dai Ukraine ta bayyana cewa za ta ci gaba da sanya ido duk da cewar ba ta fuskanci wani ƙalubale ba.
Sakataren tsaron Birtaniya Ben Wallace, ya ce zai yi murabus a wani garambawul na majalisar ƙasar da za a yi nan gaba.
Ya shaida wa jaridar Sunday Times cewa ba zai tsaya takara ba a babban zaɓe mai zuwa.
Mista Wallace ya yi aiki a matsayin sakataren tsaro a karkashin wasu firaministocin ƙasar guda uku kuma ya taka rawar gani sosai a martanin da Birtaniya ta mayar kan yakin Ukraine.
Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa suna sa ran za a sake yin garambawul ɗin a watan Satumba.
Mista Wallace ya ce zai yi murabus ne saboda yadda aikin ya takura iyalansa.
Sanarwar ta zo ne bayan shafe kwanaki ana raɗe-raɗen cewa zai bar gwamnati bayan shafe shekaru huɗu a kan mukamin.
Wakilan ɓangarori da ke faɗa da juna a Sudan da suka kunshi sojojin ƙasar da kuma dakarun RSF, sun dawo tattaunawa a birnin Jeddah na Saudiyya domin laluɓo hanyar warware rikicin wanda ya shiga wata na haɗu.
Wata majiya daga ɓangaren gwamnati ce ta sanar da dawowa tattaunawar.
Sai dai dakarun RSF ba su komai ba kan batun dawowa tattaunawar a Jeddah.
Saudiyya da Amurka ba su kai ga tabbatar da dawowa don ci gaba da tataunawa ba tsakanin ɓangarorin da ke faɗa da juna a Sudan.
Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ɗaukacin shugabannin Afrika da su mutunta ƴancin dimokuraɗiyya da doka-da-oda da kuma wanzuwar siyasa.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a taron tsakiyar shekara na gamayyar Kungiyoyin Haɗin Kan Afirka da na rassan ƙungiyoyin tattalin arzikin ƙasashen yankin Afirka da ke gudana a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya.
Tinubu ya buƙaci mahukuntan ƙasashen na Afrika da su tabbatar sun mutunta batun sake sabunta mulkin dimokuraɗiyya.
Shugaban Najeriyar wanda kasance sabon shugaban kungiyar Ecowas, ya ce ya kamata a yi watsi da batun juyin mulki a faɗin nahiyar, musamman ma wannan lokaci da ake fama da rashin tsaro da sauyin yanayi da kuma annobar korona.
Ya ce abin takaici ne ganin cewa duk da kasancewar Yammacin Afrika sahun gaba wajen ɗaɓɓaka dimokuraɗiyya da kuma kyakkyawar shugabanci, ita ke gaba a yankin wajen amfani da hanyoyi da suka saɓa wa kundin tsarin mulki don sauya gwamnati.
Ya kuma yi gargaɗin cewa yawaitar kifar da gwamnatoci da ake samu a Afrika, na barazanar kawo rashin zaman lafiya da tsaro, da janyo talauci da ɗaiɗaita mutane wajen raba su da muhallansu.
''Tsakanin 2020 zuwa yanzu, Afria ta fuskanci juyin mulki guda shiga da kuma guda uku wanda ba a samu nasara ba. Hakan na janyo tarnaki ga tsarin dimokuraɗiyyar mu a Afrika.
"Don haka, na ke kira ga ɗaukacin shugabannin Afrika da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun mutunta ƴancin dimokuraɗiyya da kuma doka-da-oda don tabbatar da ɗorewar siyasa a nahiyar," in ji Tinubu.
Mutum goma goma ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota a kan babbar hanyar Jebba-Bode a jihar Kwara.
Lamarin ya rutsa da mutum 17 waɗanda suka haɗa da maza 12 da mata guda biyu da kuma wasu yara guda uku.
Mutanen da suka mutu sun kunshi maza guda bakwai da mace guda ɗaya da kuma yara biyu.
Hatsarin ya afku a ranar yammacin ranar Alhamis, inda wasu motoci guda uku suka garu, abin da kuma aka danganta faruwarsa da gudu fiye da kima da kuma kokarin wucewa da direbobin motocin suka yi.
Babban kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta jihar, Fredrick Ade Ogidan ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin ba su kulawar gaggawa, yayin da aka kai waɗanda suka mutu kuma ɗakin ajiyar gawawwaki na asibitin koyarwa na Jami'ar jihar da ke Ilorin.
Rahotanni na bayyana cewa an garzaya da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zuwa asibiti domin duba lafiyarsa.
Tun da farko, Mista Netanyahu ya bayyana cewa yana fama da ciwo a kirjinsa kafin daga bisani a kai shi asibitin Sheba da ke garin Hashomer.
Amma an ce yana ci gaba da samun kulawar da ta kamata.
Netanyahu, mai shekara 73, ya kasance shugaba mafi daɗewa a ƙasar isra'ila.
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLE ta ce tana bincike game da wani rikici da ya kai ga harbe-harbe a lokacin da jami’anta suka kai samame kan wata dabar masu sayar da miyagun ƙwayoyi a unguwar Okpanam da ke Asaba a jihar Delta.
Lamarin da ya sa harsashi ya samu wani matashi, abin da kuma ya yi sanadiyyar mutuwarsa a asibiti a lokacin da ake yi masa maganai.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Asabar, shugaban hukumar Burgejiya Janar Buba Marwa mai ritaya ya ce ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi daga shalkwatar hukumar da ke Abuja tare da tura shi zuwa jihar Delta don gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin gaskiyar abin da ya faru.
Rahoton binciken farko ya nuna cewa ‘’A ranar Alhamis 13 ga watan Yuli, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma Jami’an hukumar NDLEA suka ƙaddamar da wani samame bayan samun bayanan sirri kan wata dabar manyan dilolin ƙwaya da ke unguwar Okpanam na jihar Delta, inda a yayin samamen aka samu yamutsi tsakanin jami’anmu da gungun masu laifin wadanda ke cikin wata mota ƙirar Toyota Camry, inda suka harbi ɗaya daga cikin jami’anmu wanda yanzu haka ke cikin mawuyacin hali a asibiti’’
‘’A ƙoƙarin hana motar guduwa ne wani jami’inmu ya yi yunƙurin harbin tayar motar’’.
Sanarwar ta ce a yayin da aka ɗauki jami’in hukumar zuwa asibiti, sai jami’an suka samu labarin cewa harsashin da jami’in nasu ya harbi tayar motar ya samu wani matashi, inda jami’an hukumar suka yi gaggawar gano mahaifinsa, tare da bin sa zuwa asibiti domin taimaka masa, sai dai matashin ya mutu a lokacin da ake yi masa magani.
“Muna tattaunawa da iyalansa domin ba su duk taimakon da suke bukata. Yayin da muke gudanar da bincike, muna masu tabbatar wa iyalan matashin da sauran al’ummar gari cewa za mu yi ƙoƙarin gano ainihin abin da ya faru domin ɗaukar matakin da ya dace’’, in ji sanarwar.
Shirin Lafiya Zinariya na wannan makon, wanda Habiba Adamu ta gabatar, ya duba matsalat hawan jini, da abubuwan da ke haddasa cutar, da yadda za a magance ta.
An gargaɗi mazauna birane 16 a fadin Italiya game da tsananin zafin da ke ci gaba da shafar kudancin Turai.
Gargaɗin, wanda ke nuna irin illar da zafin ranar zai iya yi wa lafiyar mutane, ya shafi biranen Rome da Florence da Bologna waɗanda masu yawon buɗe idanu suka fi ziyarta.
Zafin ranar ya zarta yadda aka saba gani a wasu yankunan Turai a 'yan kwanakin nan.
Ana fargabar samun ƙaruwar zafin ranar cikin mako mai zuwa.
Gwamnatin Italiya ta shawaraci mutanen da ke yankin da gargaɗin ya shafa da su kauce wa shiga ranar tsakanin ƙarfe 11:00 na safe zuwa 6:00 na yamma, sannan a bai wa tsofaffi da gajiyayyu kulawa ta musamman.
Zafi wani lokaci ne da ke zuwa a wani yanayin shekara, to sai dai a baya-bayan nan duniya na fuskanta ƙaruwar zafin rana da ake alaƙantawa da batun ɗumamar yanayi.
Babbar kotun tarayyar da ke Kano ta ba da umarnin a saki wani tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Idris Wada Saleh wanda ake zargi da almundahanar naira biliyan ɗaya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a baya-bayan nan ne babbar kotun Majistaren jihar ta umarci tsare shi a hannun hukumar karɓar ƙorafe- ƙorafe hana cin hanci ta jihar Kano (KPCACC).
An zargi tsohon kwamishinan da yaudara da kuma yin karya a takardun wasu ayyuka zamanin gwamnatin da ta wuce.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta yi zargin cewa a 2023, tsohon kwamishinan ya bai wa kamfanin Arafat construction da 'Multi resources' kudi nairan biliyan ɗaya domin gyaran tituna 30 a cikin birnin jihar.
To sai dai in ji hukumar, babu ko ɗaya cikin ayyukan da aka yi. A baya-bayan nan dai hukumar KPCACC ta ce ta aike da takardar gayyata ga tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje a kan 'bidiyon dala'.
To amma babbar kotun tarayya a jihar ta dakatar da hukumar a kan wannan batu, har zuwa lokacin da za ta kammala sauraron ƙorafin da Ganduje ya shigar gabanta yana neman ta hana hukumar binciken sa.
Akalla mutum 20 ne suka mutu, sannna aka kwashe wasu dubbai, bayan da wata mummunar ambaliya ruwa ta afka wa Koriya ta Kudu sakamakon mamakon ruwan sama a yankunan tsakiyar ƙasar.
Ruwan sama mai ƙarfi da aka kwashe tsawon kwana uku ana tafkawa a ƙasar ya haifar da zaizayewar laka tare da cikar babbar madatsar ruwa da ke lardin arewacin Chungcheong, lamarin da ya sa ta batse.
Mamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske ya haddasa karyewar titunan mota, da na hanyoyin jiragen ƙasa, inda ya rika tafiya da ƙananna motoci.
Jami'ai sun ce an tilasta wa dubban mutane barin gidajensu, yayin da mutum 14 suka ɓata.
Lardin Arewacin Gyeongsang mai tsaunuka ne lamarin ya fi ƙamari, inda zaizayewar laka ta haddasa lalacewar gidaje masu yawan gaske.
Firaministan ƙasar Han Duck-soo ya buƙaci sosjojin kasar su taimaka wa aikin ceto.
Hukumomi sun ce ƙananan motoci 19 ne ruwan ya tafi da su a lardin Chungcheong da ke tsakiyar ƙasar, lamarin da ke haddasa fargabar ƙaruwar adadin waɗanda suka mutu.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto Dakta Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce babu wani muƙami da a yanzu yake nema a rayuwara.
A hirarsa da BBC Bafarawa ya ce a yanzu duk wani mai mulki da ai kai wa ziyara, zai je ne tsakaninsa da Allah ba don wani abu da zai samu ba na muƙami.
''Babu abin da na ke so a yanzu, bayan gamawa lafiya''.
Hirar na zuwa ne bayan ziyarar da ƙungiyar tsoffin gwamnonin 1999 wadda Bafarawa ke cikinta, da suka yi zamani da shugaban ƙasar Bola Tinubu, lokacin da yake gwamnan jihar Legas na cikin waɗanda suka ziyarce shi a `yan kwanakin nan.
A filin mu na gane mani hanya wannan makon, Ibrahim Isa ya tattauna da tsohon gwamnan na jihar Sokoto, kan ziyarar tasu da wasu batutuwa da suka shafi siyasar Najeriya da ta jihar Sokoto
Khalifa Yakubu Shu'aibu wani matashi ne daga Arewacin Najeriya wanda ya karanci harkar ƙere-ƙere, ya mayar da ɗakinsa 'Smart room', inda yake kunna hasken lantarki da kunna ruwan famfo da kuma fanka da ma wasu abubuwan da dama ta hanyar ba su umarni da bakinsa kawai.
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya ta kama wani mutum bisa zarginsa da sayar da 'ya'yansa guda uku.
Yayin da 'yan sanda ke holen mutumin a ofishinsu da ke unguwar tsohuwar GRA a jihar, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Grace Iringe-Koko, ta ce sun kama mutane masu yawa da ke harkar sayar da ƙanana yara a fadin jihar.
Mutumin mai suna Michael Charles, ya amince cewa ya sayar da 'ya'yansa, yana mai cewa talauci da rashin halin ɗaukar nauyin 'ya'yan nasa ne ya sanya shi ɗaukar matakin.
Sauran mutanen da ke da hannu wajen sayar da yaran sun hadar da wani likita da kuma wani tsohon kansila.
Yayin da take magana a madadin mahaifiyar yaran wadda ita kurma ce, kakar yaran ta ce surukin nata ya daɗe yana sayar da 'ya'yan da 'yar tata ke haifa, tare da yi mata ƙaryar cewa yaran mutuwa suke yi a lokacin haihuwarsu a asibiti.
Sanarwar da 'yan sanda suka fitar, na cewa bayanan da suka samu sakamakon kama wasu da ake zargi da safarar ƙananan yara ne ya kai su ga gano waɗannan mutane, tare da mutanen da ke sayen jariran.
Bayan da ka kama su ne suka shaida wa 'yan sanda yadda suka yi cinikin yaran.
''Daya daga cikin wadda ta sayi jariran mai suna Favour Amaewhule ta ce ta sayi jaririn a kan kuɗi naira 700,000, inda aka bai wa mahaifin jaririn naira 350,000, sauran 350,000 ɗinn kuwa aka bayar da su ga tsohon kansilan tare da abokan hulɗarsa'', kamar yadda sanarwar 'yan sandan ta bayyana.
A halin da ake ciki dai rundunar 'yan sandan ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano ƙarin mutanen da ke wannan mummunar sana'a, domin daukar mataki a kan su.
Daruruwan masu zanga-zanga ne suka fantsama kan titunan Bangui babban birnin Jamhuriyar Airka ta Tsakiya a ranar Juma'a domin nuna adawa da shirin gwamnatin ƙasar na yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima, domin bai wa shugaban ƙasar Faustin-Archange Touadera damar sake tsayawa takara a wa'adin mulki na uku.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, shugabanin adawar ƙasar ne suka jagoranci masu zanga-zangar su aƙalla 500 a birin na Bangui, tare da rakiyar jami'an tsaron kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
Tun da farko gwamnatin ƙasar ta haramta zanga-zangar, to amma shugabanin adawar suka buƙaci jami'an kiyayen zaman lfiyar na MDD su ba su kariya a lokacin gudanar da ita.
A ranar 30 ga watan Yuli ne za a kaɗa ƙuri'ar amincewa da yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyara.
A watan Mayun da ya gabata ne, shugaba Touadéra ya bayyana cewa za a yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul.
Idan har matakin ya yi nasara to za a cire batun taƙaita wa'adin mulki a kundin tsarin mulkin ƙasar, lamarin da zai bai wa shugabana ƙasar damar sake tsayawa takara a wa'adin mulki na uku, kamar yadda magoya bayansa ke fata.
A shekarar 2020 ne shugabar kotun tsarin mulkin Farfesa Danièle Darlan ta ce shirin yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima, ya saɓa wa doka, musamman batun ƙara wa'adin mulkin shugaban kasa.
Kalaman da suka sanya aka sauke ta daga muƙamin tare da maye gurbinta da Jean-Pierre Waboé, wanda ake ganin makusanci ne ga shugaban kasar.
Tsohon firaministan ƙasar, kuma ɗan majalisar jam'iyyar adawa Martin Ziguele ya ce, ''Touadera na son zama mai mulkin kama-karya, shi ya sa muke adawa da gyaran dokar, wadda ba komai ba ce, face zambar siyasa''
A shekarar 2016 ne aka fara zaɓen Touadera a matsayin shugaban ƙasa da taimakon Faransa da Majalisar Dinkin Duniya, haka kuma an sake zaɓensa a 2020 a zaɓen da ya sha suka kan rashin fitowar masu kaɗa ƙuri'a, musamman a yankunan da 'yan tawate ke riƙe da su.
Kungiyar agaji ta Medicine San Frontiers ta bayyana cewa halin da ake ciki na jin kai a yankin Darfur na Sudan na ara tabarbarewa.
Ta ce sama da mutum 300 aka kashe a El Fasher tun bayan ɓarkewar rikici tsakanin sojoji da dakarun RSF masu sanye da kayan sarki cikin watan Afrilu.
Wani ɗan ƙaramin asibitin haihuwa ne ake amfani da shi a matsayin babban asibitin yankin baki daya.
Babban jami'in da ke sanya ido kan asibitin Mohammed Alfa-geeh, ya ce har yanzu ana kulawa ne da marasa lafiya a kan dakali wasu kuma a ƙasa, domin babu wurin kwantar da marasa lafiya a asibitin.
Wawaso da ƙwace da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke yi, ya haifar da ƙarancin abinci, da man fetur da magunguna, lamarin da ya sa farashinsu ya tashi.