Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abba ya mayar da Sheikh Daurawa kan shugabancin Hisba ta Kano

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Abin da ya sa ake tuhumar gwamnatocin baya kan ‘kuɗin Abacha’

  2. Mutum shida sun mutu a hari kan makarantar yara a China

    'Yan sanda a China sun ce an kashe mutum shida a wani harin wuka da aka kai kan makarantar yara da ke yankin Guangdong a kudu maso gabashin ƙasar.

    Ƴan sanda sun ce an jikkata mutum guda sannan sun kama wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Wu a garin Lianjiang.

    Kakakin shugaban yankin da ke birnin Lianjiang (Jianjiang), ya shaida wa ƴan jarida cewa mutum uku cikin waɗanda aka kashe kananan yara ne.

    Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa wani jami'i a yankin ya ce sauran waɗanda abin ya rutsa da su sun haɗa da malami da kuma iyaye biyu.

    Harin ya faru ne a ranar Litinin a daidai lokacin da iyaye suka kai ‘ya’yansu makaranta.

    • An yi rana mafi tsananin zafi a tsawon shekara 60 a China
    • Yadda ake cin zarafi da kashe ƴan Ghana a jiragen ruwan China
  3. Ali Bongo zai nemi tazarce a karo na uku a Gabon

    Shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo ya ce zai sake tsayawa takara a zaben da za a yi a watan Agusta, a wani mataki na ci gaba da mulki na tsawon shekaru 56 da iyalan gidansu suka yi a ƙasar.

    "Saboda babu abin da ya fi nasara, a yau ina sanar da ku cewa zan tsaya takara,” in ji Bongo lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa.

    A ranar 26 ga watan Agusta za a yi zaben shugaban ƙasa a Gabon.

    Bongo mai shekaru 64, ya kasance shugaban ƙasar ta Gabon mai arzikin man fetur tsawon wa’adin mulki na shekaru bakwai har sau biyu.

    Ya gaji mahaifinsa, Omar Bongo wanda ya rasu a shekara ta 2009, kuma mahaifin na sa ya jagoranci ƙasar tun daga shekarar 1967 har zuwa rasuwarsa.

    Kundin tsarin mulkin Gabon bai iyakance wa’adin mulkin shugaban ƙasa ba.

    A zabuƙa biyu da Ali Bongo ya samu nasara, ya fuskanci ƙalubale daga wajen ‘yan adawa inda suka yi zargin an tafka magudi.

    A shekara ta 2016, lokacin da ya lashe zaben shugaban ƙasa, sai da aka yi zanga-zanga a ƙasar har aka ƙona ginin majalisar dokoki.

    Sanarwar Ali Bongo ta neman tazarce ta jefa shakku a zukatan al‘ummar ƙasar ganin cewa yayi fama da bugun jini a watan Oktoban 2018 har sai da aka kai shi Moroko neman magani.

    Ya shafe watanni uku yana jinya a ƙasar waje, amma sai ya koma gida ba zato ba tsammani a lokacin da aka yi yunkurin kifar da gwamnatinsa.

  4. Shugaba Biden zai gana da Sunak da Sarki Charles a kan Yaƙin Ukraine

    Shugaba Biden da ke rangadin gajeren lokaci a London a hanyarsa ta zuwa taron kungiyar tsaro ta NATO - zai gana da Firaminista Rishi Sunak da sarki Charles na uku.

    Wakilin BBC ya ce ganawar da Biden zai yi a fadar gwamnati na Downing Street, zai duba yaƙin Ukraine da kuma batun sauyin yanayi.

    Birtaniya da sauran mambobin NATO sun nuna matukar damuwa kan matakin gwamnatin Amurka na baya-bayan nan na bai wa Ukraine shu'umin bam mai 'ya'ya.

    Ukraine ta ce ba za ta yi amfani da irin wannan bam din ba a Rasha ko kuma yankuna masu al'umma.

    Sai dai Ofishin jakadancin Rasha a Washington na ikirarin cewa wannan mataki na Amurka ba shi da maraba da laifukan yaki.

    • Yadda ziyarar shugaban Ukraine ta kasance a Amurka
    • Abin da ya sa ziyarar Biden a Gabas ta Tsakiya ta jawo ce-ce-ku-ce
  5. Gwamnatin Filato ta saka dokar takaita zirga-zirga ta sa’a 24 a karamar hukumar Mangu

    Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya sanya dokar takaita zirga-zirga ta sa’a 24 a karamar hukumar Mangu na jihar sakamakon hare-hare da suka janyo asarar rayuka da ma dukiyoyi a yankin.

    Rikicin tsakanin wasu kabilu a yankin ya kuma raba mutane da dama yawa da muhallansu da kuma haifar da zaman dar-dar tskakanin kabilun fulani da kuma ta magafu.

    Shugaban matasan Fulani ta Miyetti Allah a yankin na Mangu, Saidu Jauro ya fada wa BBC cewa al'ummar magafu sun kai hari a gidajen fulani tare da kona wasu, inda ya ce an kashe mutane 18 a garin Amsan.

    Wani daga ɓangaren kabilar ta magafu da ake zargi da kai harin ya ce 'a iya sanina ban san wani ɗan kabilar magafu da ya far wa fulani ba".

  6. Mutum 28 sun mutu sakamakon ruwan saman mai karfi a Indiya

    Ruwan sama mai karfin gaske na ci-gaba da ɗaiɗaita yankunan arewacin Indiya, ta hanyar haifar da zabtarerwar ƙasa da ambaliyar ruwa.

    Akalla mutum 28 kawo yanzu aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da gadoji da gine-gine ke rushewa.

    An sake fitar da gargaɗi kan yanayi mai muni a jihohi irinsu Himachal Pradesh da Uttara-khand da Ladakh, sannan ana aikin kwashe mutane a yankunan da suka fi fuskantar barazana irinsu Punjab.

    A Delhi da kewayen birnin, an rufe dukkanin makarantu a yau Litinin saboda fargabar ambaliya daga kogin Yamuna da ka iya ɓallewa.

    Wannan shine ruwan sama mafi karfi da ake ganin a birnin ƙasar cikin shekaru 40.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi na Kai-tseye barkanmu da war haka.

    Aisha Babangida ke fatan kasancewa da ku a wannan rana ta Litinin domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya lekawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.