Abba ya mayar da Sheikh Daurawa kan shugabancin Hisba ta Kano

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Ahmad Tijjani Bawage

  1. An kama jirgin ruwa makare da danyen man fetur na sata daga Najeriya

    NNPCL

    Asalin hoton, OTHER

    Kamfanin mai na Najeriya NNPCL, ya kama wani jirgin dakon man da ke hanyarsa ta zuwa Kamaru dauke da gurbataccen man da aka hako daga jihar Ondo lita dubu 800.

    Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Litinin, ya ce jirgin mallakin wani kamfanin Najeriya mai suna MT-TURA II, ya kai shekaru 12 ya na dakon irin wannan man a boye, kuma a yanzu za a lalata jirgin don ya zame wa masu irin wannan sana'a darasi.

    Bangaren man fetur na Najeriya na fama da rashawa tsawon gwammam shekaru, inda ake satar danyen mai da kuma kafa haramtattun matatun mai a yankin Neja-Delta. A 2022 gwamnatin kasar ta ce tana asarar sama da gangar danyen mai 470,000 a kowace rana sanadiyyar wadannan ayyuka.

    A watan Agustan 2022 danyen man fetur da Najeriya ke fitarwa ya ragu zuwa kasa da ganga miliyan guda a kowace rana - mafi karanci a cikin shekaru 30.

  2. Zulum ya dakatar da ayyukan ƴan Jari-bola a Borno

    Gwamnan jihar Bornon, Babagana Umara Zulum

    Asalin hoton, Borno State Government

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum

    Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zullum, ya dakatar da ayyukan 'yan jari bola a sassan jihohi 27 na jihar.

    Gwamnan ya dauki matakin ne da nufin kare irin wadannan masu sana'a da ci gaba da kashensu da 'yan Boko Haram ke yi a wajen garuruwan kananan hukumomin jihar.

    Ba a san adadin matasan da ke irin wannan sana'a da ke tafiye tafiye zuwa garuruwa don sana'arsu da aka kashe ba.

    Da yake sanar da matakin, gwamna Zullum, ya ce," A cikin shekaru biyar da suka wuce, an kashe mutane da dama a sakamakon yawan jari bola da suke abin da ya janyo gwamnatin jihar ta fara bincike a kai ke nan."

    Ya kara da cewa, " Kuna ganin wannan wajen, duk waje ne mallakin gwamnati, sannan daga baya kuma waje ne mallakin kamfanonin sadarwa. A don haka irin wadannan sana'oi zagon kasa ne da ake yi wa gwamnatin tarayya, a don haka na bayar da umarnin dakatar da wannan sana'a."

    Zullum, ya ce yawancin masu irin wannan sana'a kuma na lalata kayayyakin gwamnati da ma na kamfanoni masu zaman kansu a don haka ba za a amince da irin wadannan mutane ba.

    Gwamnatin jihar ta ce zata yi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro don tabbatar da an kama duk wanda ya nuna kunnen kashi ko ya karya doka.

    ...

    Asalin hoton, Borno State Government

  3. An kori ƴan sandan da suka sumar da wani farar hula

    An dakatar da dukkan 'yan sanda takwas da ke da hannu wajen sumar da wani farar hula a wani yanki na birnin Johannesburg daga aiki.

    An dauki bidiyon 'yan sandan wadanda ke rakiyar mataimakin shugaban kasa Paul Mashatile suna janyo wasu jami'in soja da ke samun horo wanda kuma ke sanye da kayan da bana soja ba daga motar da su ke ciki inda suka lakada masu duka a wannan watan.

    Sun bar daya daga cikin wadanda suka lakawa dukan a sume bayan sun dake shi a ka.

    Ba a san dalilin da ya sa suka lakada musu dukan ba.

    Bidiyon dai ya janyo suka a kasar inda aka rinka tambayar me yasa ake ba wa 'yan siyasa kariya?

    Shi dai mataimakin shugana kasar Mashatile wanda ya ce ba ya wajen a lokacin da lamarin da ya afku, ya soki lamarin inda ya bayyana shi cewa an yi amfani da karfin tuwo wajen cin zarafin farar hula.

  4. Dole gwamnatoci su kare masu fallasa rashawa a Afirka - Amnesty

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar kare hakkin bil'adam ta Amnesty International, ta ce dole ne kasashe yammaci da tsakiyar Afirka su ddaina cin zarafin masu bankaɗo ayyukan rashawa, a maimakon hakan sai a dauki matakan kare su.

    Yau ne aka cika shekara 20 da cimma yarjejeniya kasashen Afirka ta kiyayewa da kuma yaki da rashawa.

    Babbar sakatariya a kungiyar ta Amnesty, Agnes Callamard, ta ce "Irin halin da masu fallasa rashawa ke shiga a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka abin babu dadi, wadannan mutanen fa mutane ne da ke taka muhimmiyar rawa da sadaukarwa wajen yaki da cin hanci da rashawa, to amma sai kaga daga karshe su ake kai wa hari ko wulakanta su saboda kawai sun bayyana gaskiya."

    Ta ci gaba da cewa," Dole ne gwamnatoci su tashi tsaye wajen kare hakkin dan'adam da girmama masu kwarmata irin waɗannan bayanai da ma biya musu dukkan bukatunsu saboda rawar da suke takawa wajen bayyana marassa gaskiya."

  5. An zaƙulo gawar yara uku a gidan fasto mai fatawar azumin mutuwa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Kenya ta fara zakulo gawar mutanen da suka mutu a dajin nan da ke da alaka da kungiyar asiri.

    Daga cikin an zakulo gawar yara uku da aka samu a gidan fasfon nan mai fatarwa azumin mutuwa, sannan gawa tara a wurare daban daban.

    Ministan tsaron kasar Kithure Kindiki ya ce 'yan sanda sun kuma gano karin wasu kaburbura wanda aka yi amanna cewa an binne gawawwaki da dama a ciki.

    A bangare guda kuma, wani babban jami'i a ma'aikatar kula da filaye ta kasar ya ce mutumin da ake zargi shi ne shugaban kungiyar asirin Paul Mackenzie Nthenge, ba wai ya sayi dajin ko ya dauki hayar dajin mai nisan kadada 800 inda aka yi amanna cewa mutane sun mutu saboda azumin mutuwa an kuma binne su a wajen.

    Ma mallakin dajin mai suna Chakama Ranch ya ce Mackenzie da magoya bayansa suna zama ne kawai a gonarsu ba wai sun saya ba.

    A cewar hukumomi, an bayar da rahoton bacewar mutane 613, kuma Mackenzie da wasu mutum 27 da ake zargi za su bayyana gaban kotu a ranar 2 ga watan Augusta mai zuwa.

  6. An dauki matakin hana yara mata bara a Hadejia

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jama’a a wasu jihohin arewacin Najeriya na ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu ‘yan mata matasa ke yin bara a kan tituna da tashoshin mota.

    Matsalar barace-barace da yaran da suka isa zuwa makaranta ke yi ba sabon abu ba ce a yankin sai dai galibi maza ne ke yi.

    Game da wannan matsala hukumomi a Hadejia da ke jihar Jigawa suka dauki matakin hana barace-baracen, bayan da aka samu wasu mata mabarata an yi musu ciki tare da mayar da su garuruwan su na asali.

    Bayanan da BBC ta samu na cewa mabaratan maza da mata suna kwarara ne cikin garin Hadejia daga ciki da wajen jihar Jigawa, don yin bara inda suke bi tashoshin mota da kasuwanni.

    A baya-baya matsalar ta yi kamari inda mazauna yankin suka ce al'amarin ya kai ga ana cin zarafin wasu daga cikinsu.

    Game da wannan matsala dai karamar hukumar Hadejia ta samar da wani kwamiti wanda ya bincika batun sannan ya bayar da shawararin abin da ya kamata a yi.

    Akasarin matan da aka kama din ba su da takamaiman wurin kwana sai dai watangaririya da suke yi.

    Mahukunta a Hadejan sun ce yaran da suke gararamba ‘yan asalin karamar hukumar Hadejan musamman marasa galihu, za a yi musu tsari don tsugunar da su tare da sanya su a makaranta.

  7. Ghana za ta gina tashoshin cajin motoci masu amfani da lantarki

    Hukumomi a Ghana na shirin gina tashoshin cajin motocin lantarki guda 1,000 a fadin kasar nan da shekaru biyar masu zuwa, domin cimma burin gwamnati na rage dogaro da amfani da makamashi mai gurɓata muhalli.

    A cewar Dr Mohammed Amin Adam, karamin minista a ma'aikatar kudi, matakin wani bangare ne na shirin gwamnati na gaggauta sauya tsarin sufuri a kasar.

    Karamin ministan kudin ya ce za a fara gina tashoshin a hankali sannan za a zuba jarin kusan dala miliyan 600 daga yanzu zuwa shekara ta 2070 domin samun hanyar komawa kan amfani da makamashi mai dorewa.

    Dr Mohammed Amin Adam, ya ce yanzu akwai motoci sama da dubu da ke amfani da lantarki a kasar Ghana.

    Tuni dai wasu kamfanoni da ke kera motoci masu amfani da lantarki suka isa Ghana, abin da ake ganin samar da tashoshin cajin motocin zai ba su damar kera irin wadannan motoci.

  8. Abba ya mayar da Sheikh Daurawa kan shugabancin Hisba ta Kano

    Malam Daurawa

    Asalin hoton, OTHER

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya mayar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kan muƙamin shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano.

    A lokacin da yake tabbatar da komawa kan muƙamin ga BBC, Sheikh Daurawa ya ce: "Lallai a yau na je ofishin SSG na kaɓo takardar kama aiki."

    A watan Mayun 2019 ne Sheikh Daurawa, tare da wasu jami'an hukumar ta Hisba a wancan lokaci suka ajiye muƙamansu.

    Duk da dai babu cikakken bayani kan dalilin ajiye aikin nasa a wancan lokaci, an yi amannar cewa hakan ya faru ne sanadiyyar rashin jituwa tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

    A tattaunawar tasa da BBC, Sheikh Daurawa ya ce ya sake karɓar muƙamin ne kasancewar gwamnatin ta yanzu "Sun nuna min cewa da gaske suke yi, sun nuna min cewa da gaske za su yi aiki."

    Ya ƙara da cewa: "Dalilin da ya sa na ajiye aikin a baya shi ne saboda aikin yaƙi yiwuwa daga ƙarshe-ƙarshe."

    'Abin da zan mayar da hankali a kai'

    A tattaunawar tasa da BBC, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce babban abin da zai mayar da hakali a kai shi ne batun auren zawarawa, kamar yadda gwamnan jihar ya alƙawurta.

    Ya ce "Gwamnan a cikin kamfe ɗinsa ya ce zai aurar da zawarawa da ƴanmata da kuma taimaka wa harkar iyali da marayu da kuma iyayen marayu, waɗanda aka mutu aka bar su da yara. Shi ne abu na farko da za mu sa a gaba."

    Ya kuma ce zai ɗora a kan abubuwa masu kyau da aka yi a Hisbah tare kuma da duba inda za a yi gyara.

  9. Dusar ƙanƙara ta sauka a Johannesburg karon farko a cikin shekara goma

    Zubar dusar kankara
    Bayanan hoto, Zubar dusar kankara

    A karon farko bayan shekaru sama da goma, dusar kankara ta sauka a Johannesburg.

    Rabon dusar kankara ta sauka a birnin tun shekarar 2012, kuma dusar ta sauka a yanzu ne saboda tsananin sanyi da ake fama da shi a kasar.

    Mahukunta sun shawarci mazauna birnin da dauki matakan kare kansu daga sanyi sannan manoma d amasu kiwon dabbobi kuma su samarwa da dabbobinsu wajen da za su ajiye su.

    Hukumar hasashen yanayi ta Afirka ta Kudu ta ce an kuma samu zubar dusar kankara a gabashin Cape da kuma Mpumalanga.

    Ana kyautata tsammanin ci gaba da fuskantar wannan yanayi na zubar dusar kankara a birnin har nan da mako guda.

  10. Ba mu da alƙaluman mutanen da aka kashe a Mangu - Gwamnatin Filato

  11. Kotu ta dakatar da gurfanar da kwamshinan zaben Adamawa da aka dakatar

    Hudu Yunusa- Ari,

    Asalin hoton, OTHER

    Bayanan hoto, Hudu Yunusa- Ari

    Wata babbar kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta dakatar da Hukumar Zabe ta Kasar INEC, daga gurfanar da kwamshinan zaben Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa- Ari, a kan ayyana Aisha Dahiru, ta jam'iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

    Mai shari'a Donatus Okorowo, ne ya bayar da umarnin bayan da lauyan da ke kare Mrs Dahiru Mr Michael Aondoaka, SAN, ya gabatar da bukatar hakan.

    A cikin bukatar da suka gabatar, 'yar takarar gwamnan ta APC, ta shigar da INEC da babban mai shari'a na kasa kara.

    Yayin da ya ke gabatar da bukatar a ranar Litinin, Aondoaka ya ce kamata ya yi har sai kotu ta tabbatar da matsayin wadda ya ke karewa kamar yadda sashe na 149 na kundin zaben 2022 ya tanadar, kafin a gurfanar da Yunusa-Ari.

    Ya ce sun rubutawa kotu don nuna mata cewa karar da suka kai mai karfi ce.

    Ya ce a cikin takardar da suka rubuta sun ce sun amince cewa za su amince da duk wani hukunci kotu idan aka tabbatar da cewa karar ba mai karfi ba ce.

  12. Masu amfani da Thread sun kai miliyan 100 a kwana biyar

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, ...

    Mutane sama da million ɗari ne suka yi rajista da Threads, sabon manhajar sada zumunta da aka kaddamar kwanaki biyar da suka wuce.

    Wanna yana nufin Threads, wanda kamfanin Meta ya ƙaddamar, ya buge tarihin da aka kafa manhajar AI's ChatGPT ya kafa a baya.

    An sabuwar manhajar akan dandalin manhajojin Apple da Android a cikin ƙasashe 100 a ranar Larabar da ta gabata.

    Amma har yanzu manhajar ba ta kai Turai ba saboda rashin tabbas kan dokar sirrin bayanan EU.

    Mark Zuckerberg, shugaban kamfanin Meta, wanda kuma ya mallaki Facebook, ya ce manhajar ta samu rijistar mutane miliyan 10 a cikin sa'o'i bakwai da kaddamar da ita kuma sama da miliyan 30 a safiyar Alhamis.

    Sa'o'i 24 bayan haka, adadin mutane da suka yi rajistar amfani da manhajar ya ninka fiye da sau biyu.

    A mabiya miliyan 100, a alkaluma da dandalin bayanai na Quiver Quantitative ya fitar, Threads ya kasance yan kasa da kashi ɗaya cikin uku na yawan mutane da ke amfani da Twitter.

    Wasu masu amfani da shafin Twitter sun nuna rashin jin daɗi tun lokacin da Elon Musk ya karɓi kamfanin.

    An kori ma'aikata da dama tun bayan da Musk ya sayi shafin, inda kuma ya sanar da sauye-sauye don taimakawa wajen samar da kuɗaɗen shiga a Twitter.

  13. Firaiministan Netherlands zai bar siyasa

    Netherlands

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, ...

    Firaiministan Netherlands da yafi dadewa kan mulki, Mark Rutte ya sanar da cewa zai yi murabus daga siyasa.

    Shugaban mai fuskantar kuri'ar rashin amincewa daga majalisar kasar ya ce zai yi murabus bayan zaben watan Nuwamba.

    Mr Rutte ya jagoranci gwamnatin hadaka 4 tun daga shekarar 2010, kuma yanzu haka yana jan ragamar gwamnatin rikon-kwarya bayan rushewar hadakar gwamnatinsa.

    "Jiya da safe na sanar da matakin da na dauka cewa ba zan sake tsayawa takara a jam'iyyar VVD ba, zan yi murabus daga siyasa da zarar an kafa sabuwar majalisa", in ji Rutte.

    Dukkan ministocinsa sun yi murabus ranar Juma'a, bayan kasa cimma matsaya a kan tsare-tsaren shigar baki kasar.

  14. Putin ya gana da shugaban sojojin haya na Wagner

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gana da shugaban sojojin hayar Rasha na Wagner, Yevgeny Prigozhin bayan gazawar kungiyar a watan da ya gabata, in ji fadar Kremlin.

    Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya kara da cewa Prigozhin wanda ke jagorantar kungiyar sojojin haya na Wagner na daga cikin mutane 35 da aka gayyata zuwa taron da aka yi a birnin Moscow.

    Ya ce shugaba Putin ya yi bayani kan yadda yaƙin Ukraine ke gudana da kuma boren sojojin haya.

    Tawayen da suka kaddamar a ranar 23 ga watan Yuni ya ɗauki tsawon sa'o'i 24.

    A karkashin yarjejeniyar, an yi watsi da tuhumar Prigozhin kuma an yi masa tayin koma wa Belarus.

    An yi ta ce-ce-ku-ce tsakanin jama'a tsakanin Wagner da ma'aikatar tsaron Rasha game da gudanar da yakin. Prigozhin dai ya sha zargin ma'aikatar da gazawa.

    Sai dai a ranar Litinin, Mista Peskov ya ce shugaban Wagner na cikin kwamandojin da aka gayyata zuwa Kremlin kwanaki biyar bayan rugujewar rikicin.

    Kamfanin dillancin labaran Interfax ya ambato Mista Peskov yana cewa "Shugaban ya yi bayani akan abubuwan da kamfanin yayi a fagen daga.

    A cewar kakakin, ya ce Prigozhin ya shaida wa Mista Putin cewa Wagner ta goyi bayansa ba tare da wani sharaɗi ba. Ba a dai san inda shugaban na Wagner yake ba.

    A ranar Alhamis ɗin da ta gabata, shugaban Belarus Alexander Lukashenko - wanda ya kulla yarjejeniya ta kawo karshen tashin hankali - ya ce Prigozhin yana ƙasar Rasha.

    • Shin me juyin mulki Wagner ke yunƙurin yi wa Putin?
    • Dole mu gurfanar da mayaƙan Wagner a gaban kuliya - Putin
  15. Hotunan yadda Biden ya gana da Sarki Charles II

    Biden
    Bayanan hoto, Lokacin da shugaba Joe Biden ya isa kusurwa huɗu na fadar Windsor
    Biden
    Bayanan hoto, Sarki Charles da shugaba Biden yayin gaisawa da juna
    Biden
    Bayanan hoto, Biden ya dora hannunsa na dama bisa ƙirjinsa yayin da ake rera taken ƙasar Amurka
    Biden/Charles
    Bayanan hoto, Shugaba Biden da Sarki Charles sun duba jami’an tsaron Welsh
  16. Biden na ganawa da Sarki Charles a Fadar Windsor

    Biden

    Asalin hoton, PA Media

    Bayan barin fadar Downing Street, shugaban Amurka Joe Biden yanzu ya isa Fadar Windsor don ganawa da Sarki Charles.

    Za kuma a yi babban biki don maraba da zuwan shi a fadar Windsor Castle.

    Biden zai karɓi gaisuwar sarauta tare da sauraron taken ƙasar Amurka da masu tsaron Welsh suka yi kafin tattaunawa da Sarki Charles.

    Da zarar sun shiga cikin gidan sarki, za su sha shayi kafin su fara tattaunawa akan abubuwan da suka shafi Amurka daga tarin Sarauta.

    Sannan, za su haɗu da mutanen da ke halartar taron koli game da tara kuɗaɗe don magance sauyin yanayi, abin da ke nufin za a karfafa kokari na bayar da tallafi ga ƙasashe masu tasowa.

  17. Jami'an Gabashin Afrika sun isa Habasha domin tattaunawa kan rikicin Sudan

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Jami'ai daga sassan gabashin Afirka sun fara isa Addis Ababa babban birnin ƙasar Habasha a wani yunkurin sasanta ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan.

    Rikicin da aka kwashe watanni uku ana yi ya raba mutane kusan miliyan uku da muhallansu tare da yin barazana ga zaman lafiyar yankin baki-ɗaya.

    Ana sa ran cewa sojojin Sudan da kuma dakarun RSF za su tura wakilai zuwa taron.

    Ana dai samun rahotannin cin zarafi da ake tafkawa kan fararen hula - musamman na mayakan sa-kai da ke ƙawance da mayaƙan RSF a yankin Darfur.

    An kasa samun nasara a kokarin tabbatar da tsagaita buɗe wuta a baya, inda a yanzu Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin ɓarkewar yaƙin sosai.

    Shugaban sojojin Sudan Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ce ba zai halarci taron bayan da ya ƙi amincewa da shugabancin Kenya a yunkurin samar da zaman lafiya bisa zargin nuna son kai.

    A baya dai Kenya ta yi alkawarin cewa za ta zama yar ba ruwanmu a rikicin, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

    • Likitoci sun kaɗu da yawaitar fyaɗe a Khartoum
    • Me za a yi da gawawwakin mutanen da aka kashe a Khartoum?
  18. Hotuna: Shugaba Biden ya isa Fadar Downing Street

    Biden

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ayarin motocin shugaban Amurka Joe Biden lokacin da ya isa titin Downing a ziyara da ya kai Birtaniya
    Biden/Sunak

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Nan kuma shugaba Biden ne ke gaisawa da firaministan Birtaniya Rishi Sunak a kan wata shimfiɗar alfarma
    Birtaniya
    Bayanan hoto, Da yake magana a taronsa na Downing Street tare da Rishi Sunak, Biden ya ce dangantakar Amurka da Birtaniya "tana da karfi"
    Biden/Sunak

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Biden ya gaya wa Sunak cewa shi ne amini mafi kusanci da kuma babban abokin zance da yake ganawa da shi
    Biden

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Bayan kammala tattaunawar a fadar Downing Street, shugaba Biden zai kama hanya zuwa Windsor don ganawa da Sarki Charles
  19. Kwalara ta hallaka mutum 50 a Afirka ta Kudu

    Kwalara

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin lafiya a Afirka ta Kudu sun gargaɗi mazauna lardin Gauteng da ke ƙasar da su yi taka tsantsan game da amfani da ruwan da suke sha a daidai lokacin da ɓarkewar cutar kwalara ya hallaka kusan mutum 50.

    Ƙungiyoyi al'umma sun bukaci gwamnati da tashi tsaye don inganta da kuma samar da tsaftataccen ruwan sha.

    Galibin mace-macen da aka samu a cikin makonni shida da suka gabata, sun faru ne a yankin Hammanskraal, inda mazauna yankin suka ce sun shafe makonni suna cikin wahala wajen ganin sun samu ruwa mai tsafta.

    Sai dai suna cikin hana kwatsam aka samu bullar cutar a faɗin ƙasar.

    Ruwan famfo da ake samu ya kasance ba shi da tsafta a yankuna da dama, inda ya zama tilas mutane suka koma dogaro da motocin dakon ruwa da gwamnati ke samar wa.

    Cutar kwalara, wadda gurɓatacciyar abinci da ruwa ke haddasa yaɗuwarsa, na haifar da gudawa da amai kuma mutum na iya mutuwa cikin sa'o'i idan bai samu agajin gaggawa ba.

  20. An ceto mutum 30 daga hannun ƴan bindiga a Kebbi

    An ceto mutane akalla 30 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Danko Wasagu da ke jihar Kebbi.

    Waɗanda aka ceto ɗin sun fito ne daga garin Kontagora na jihar Neja da Danmari da Kaba da kuma Kajiji a jihar Zamfara da kuma Bena ta jihar Kebbi.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban karamar hukumar Danko Wasagu, Alhaji Useni Aliyu Bena ne ya bayyanawa manema labarai game da rahoton ceto mutanen.

    Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar kan yadda take aiki da jami’an tsaro, tare da ba su tallafi domin ganin an fatattaki ‘yan fashin dajin da suka addabi jihar da ma maƙwabtanta, tare da kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su.