Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Harin sojojin Sudan ya kashe mutum 22 a birnin Khartoum

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Za a rantsar da dan luwaɗi a matsayin shugaban kasar Latvia

    Kasar Latvia za zama kasa ta farko a duniya da ta samu shugaban kasa da ya bayyana kansa a matsayin dan luwadi daga Tarayyar Turai, har zuwa tsohuwar tarayyar Soviet.

    Nan gaba kadan ne a yau za a rantsar da Edgars Rinke-vics a matsayin sabon shugaban kasar

    A shekarar 2014 ne Mista Rinke-vics ya fara fitowa fili ya bayyana kansa a matsayin dan luwadi, kuma ya yi fice wajen kare yancin masu auren jinsi tun fil a zal.

    Ko da yake an sha samun da dama da ke rike mukaman gwamanti a Turai, amma wannan ne karon farko da aka samu dan luwadi a matsayin shugaban kasa.

  2. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku domin kawo irin wainar da ake toyawa a fadin duniya, amma za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da makwabtanta.

    Kuna iya lekawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.