Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe don ɗorawa daga inda muka tsaya a wani shafin daban.
Sai da safenku.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe don ɗorawa daga inda muka tsaya a wani shafin daban.
Sai da safenku.
Ƙungiyar 'yan Shia ta Houthi da ke iko da arewacin Yemen ta ce ta hana shigar da kayan da aka sarrafa a Sweden don nuna ɓacin ranta da ƙona Ƙur'ani mai tsarki da aka yi a ƙasar.
Gidan talabijin da Houthi ke gudanarwa na Al Masirah TV ya ruwaito ministan kasuwanci na ƙungiyar yana cewa su ne ƙasar Musulmi ta farko da ta ɗauki irin wannan mataki.
Duk da ya ce kayan Sweden "ba su da yawa", ya bayyana matakin da "na musamman" kuma ya nuna "irin abin da Houthi ke iya yi".
Ya kuma yi kira ga ƙasashen Musulmai da su bi sawunsu.
A ranar jajiberin Babbar Sallah ne wani mutum ya ƙona Ƙur'anin a wajen wani masallaci na birnin Stockholm bisa kariyar 'yan sanda, yana mai cewa ya yi ne don ya nuna 'yancinsa na faɗar albarkacin baki.

Asalin hoton, Social Media
Bayan tabbatar da sakamakon jarrabawar JAMB da Mmesoma Ejikeme ta gabatar na ƙarya ne, kamfanin ƙera motoci na Innoson Group ya janye tallafin karatu na naira miliyan uku da ya bai wa matashiyar.
Ejikeme mai shekara 19 ta yi iƙirarin cewa ta ci maki 362 a jarrabawar, wanda ya sa ta zama cikin mafiya hazaƙa a jarrabawar ta wannan shekarar.
Hakan ne ya sa mamallakin kamfanin, Innocent Chukwuma, ya ba ta naira miliyan uku a matsayin tallafin karatu.
Saii dai daga baya hukumar shirya jarrabawar ta shiga manyan makarantu a Najeriya ta musanta iƙirarin matashiyar, tana mai cewa 269 ne haƙiƙanin makin da ta ci.
"...Saboda waɗannan ƙa'idojin da kuma sakamakon bincike, mun ɗauki matakin janye tallafin karatun da muka bai wa Miss Joy Mmesoma Ejikeme," a cewar sanarwar da kamfanin ya wallafa a yau Asabar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya jaddada cewa ƙasarsa "ba ta goyon bayan" amfani da bam mai 'ya'ya da Amurka ke shirin bai wa Ukraine.
Birtaniya na cikin ƙasashen da suka haramta amfani da bam ɗin, wanda ke kashe fararen hula, a ƙarƙashin wata yarjejeniya.
Sai dai firaministan ya nanata goyon bayansa ga Ukraine din a yaƙin da take yi da Rasha.
A ranar Juma'a, Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya ɗauki "mataki mai tsauri" na bai wa Ukraine makaman.
Sifaniya da Kanada, biyu daga cikin da suka hana amfani da bam ɗin, sun soki matakin samar da su ga Ukraine, tare da kuma sauran ƙungiyoyin kare haƙƙi.
Bam mai 'ya'ya wani nau'in makami ne da ke harba ƙananan bama-bamai daga makamin roka, ko mai linzami, ko atilare kuma su warwatsu zuwa yankuna daban-daban.
Wasu daga cikinsu kan ɗauki tsawon shekaru ba su tashi ba bayan harba su, abin da ke jefa rayuwar 'yan Adam cikin haɗari tsawon lokaci bayan gama yaƙi ko rikici.

Asalin hoton, State House

Asalin hoton, State House

Asalin hoton, State House

Asalin hoton, Reuters
Wani hari da rundunar sojan Sudan ta kai ta sama a birnin Khartoum ya kashe aƙalla mutum 22 tare da jikkata wasu da dama, a cewar wani shaida.
Mata da yara na cikin waɗanda lamarin ya ritsa da su, kamar yadda waɗanda suka shaida lamarin suka bayyana wa BBC.
Harin ya sauka a kan gundumar Dar es Salaam da ke tsallaken Kogin Nilu ta ɓangaren Khartoum a yau Asabar.
Rundunar RSF da sojojin ƙasar sun shafe aƙalla wata biyu suna yaƙar juna tun daga watan Afrilu.
Wata majiya daga ma'aikatar lafiya da kamfanin labarai na Reuters ya ambato ta ce mutum 22 ne suka mutu, yayin da RSF ke cewa sun kai 31.
Yaƙin ya ɓarke ne bayan shugaban sojojin ƙasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan, da kuma shugaban Rapid Support Forces (RSF), sun samu saɓani game da makomar ƙasar.

Asalin hoton, AFP
Jami'an tsaro a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce sun ceto ƙarin mutum biyar daga hannun 'yan fashin daji a yau Asabar bayan an yi garkuwa da su.
Kwamandan Rundunar Hadarin Daji Janar Sani Ahmed ne ya tabbatar wa da BBC Hausa kuɓutar mutanen waɗanda dukkansu mata ne.
An ceto su ne a Ƙaramar Hukumar Maru da ke jihar ta Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, yankin da ke fama da hare-haren 'yan bindiga masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Adadin ƙari ne a kan sama da mutum 60 da rundunar ta ce ta ceto a farmakin da ta kaddamar kan 'yan fashin dajin daga jihar Kebbi mai maƙwabtaka zuwa Zamfara cikin kwana tara da suka gabata.

Asalin hoton, JOE BIDEN
Shugaban Amurka Joe Biden ya kare matakin ƙasarsa na bai wa Ukraine boma-bomai masu 'ya'ya, waɗanda suke da tarihin kisan fararen hula.
shugabn ya ce an ɗauki lokaci kafin ya amince da matakin, to amma ya ce ya amince da matakin ne saboda sojojin Ukraine na fama da rashin makamai.
Shugaban Ukraine ya yaba da matakin, to sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama da wasu 'yan jam'iyyar Demokrats sun soki matakin.
Mista Biden ya shaida wa kafar yada labarai ta CNN ranar Juma'a cewa ya tuntubi ƙawayen Amurka game da matakin.
Matakin na Amurka na zuwa ne gabanin taron kungiyar tsaro ta NATO da za a gudanar a Lithuania a mako mai zuwa.
Kasashe fiye da 120 ne a duniya ciki har da kawayen Amurka suka haramta amfani da bama-baman, wadanda ke tarwatsewa su watsa ‘ya’ya bayan an harba su.
To sai dai duka duka ƙasashen Rasha na Ukraiane sun yi amfani da makaman a wannan yaƙin.

Asalin hoton, STATE EMERGENCY SERVICE UKRAINE
Hukumomin Ukraine sun ce akalla mutum takwas ne suka mutu, bayan da Rasha ta kai hari yankin Donetsk da ke gabashin ƙasar.
Ministan harkokin cikin gida na Ukraine ya ce mutum 13 sun jikkata sakamakon hare-hare da Rasha ta kai wa birnin Lyman.
Hare-haren sun haddasa ƙonewar wasu gidaje da shagon buga littattafai da wasu kananan motoci uku, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake cika kwana 500 da mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.
A watan da ya gabata ne Ukraine ta fara kaddamar da hare-hare a ƙoƙarin da take yi na kwace iko da yankunan Donetsk da Zaporizhzhia.
To sai dai a yanzu dakarun Rasha sun ci gaba da kai hare-hare da jirage marasa matuƙa a yankunan.
Birnin Lyman - wanda shi ne cibiyar jiragen kasa ta yankin Donetsk - a baya Rasha ta taɓa karɓe iko da shi, kafin dakarun Ukraine su kwace shi a watan Octoban da ya gabata

Asalin hoton, @INSIDEAREWA
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin dakatar da hukumar yaki da rasahawa ta jihar PCACC da hukumar 'yan sanda da jami'an tsaron farin kaya na DSS da jami'an tsaro na Civil Defence daga kama tsohon gwamnan jihar Abdulahi Umar Ganduje.
Kotun ta bayar da umarnin hana waɗannan kama tsohon gwamnan ko iyalansa ko kuma jami'an tsohuwar gwamnatinsa.
Umarnin na zuwa ne bayan da hukumar yaki da rashawa ta jihar ta gayyaci tsohon gwamnan domin amsa wasu tambayoyi kan 'bidiyon dala' da jarida Daliy Najerian ta wallafa a shekarar 2018, wanda ya zargi tsohon gwamnan da karɓar kuɗaɗe daga hannun 'yan kwangila.
A ranar Laraba ne shugaban hukumar karbar korafi da yaki da rashawa ta jihar Muhuyi Magaji Rimingado ya ce bincike ya tabbatar da sahihancin bidiyon.
Yayin yanke hukunci kan ƙarar da Ganduje ya shigar gabansa, mai shari'a A Liman ya bayar da umarnin dakatar da hukumomin ko jami'ansu daga kama tsohon gwamnan, har zuwa lokacin da za a saurari karar ranar 14 ga watan Yuli.

Asalin hoton, Presidency
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS karo na 63 da za a gudanar a ƙasar Guinea-Bissau.
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan ayyukan na musamman Dele Alake ya fitar, ya ce shugaban zai bar Najeriya a yau Asabar domin halartar taron wanda za a gudanar ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce shugaban zai samu rakiyar wasu daga cikin masu ba shi shawara tare da wasu manyan jami'an gwamnatinsa.
Ana sa ran tattauna muhimman batutuwan da ke damun ƙasashen ƙungiyar ciki har da matsalar tsaro da ƙasashen yankin ke fuskanta, tare da yin nazari kan rahoton da majalisar ministocin ƙungiyar suka fitar a taronsu na 90 da suka gudanar.
Haka kuma akwai batun hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka tare da yin nazari kan batun miƙa mulki hannun farar hula a ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.
Sauran batutuwan da ake sa ran taron zai tattauna sun haɗar da batun kudin bai ɗaya na ƙungiyar, da matsalar da ake samu wajen safarar kayayyaki tsakanin wasu ƙasashen yankin.
Wannan shi ne karo na biyu da shugaban ƙasar zai halarci taro a ƙasashen waje tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar ranar 29 ga watan Mayu.
Taro na farko da Tinubu ya halarta a ƙasashen waje, shi ne taron harkokin kuɗi da ya gudana a Faransa cikin watan Yuni.
Ana ra ran shugaban ƙasar zai koma Najeriya bayan kammala taron

Asalin hoton, Nigerian Police/Twitter
Rundunar 'yan sandan jihar Enugu ta ce jami'anta sun samu nasarar tarwatsa wani gungun 'yan bindiga ke kokarin kakaba dokar zaman gida a jihar.
Cikin wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce a ranar Juma'a da safe ne jami'anta suka gano gawarwakin hudu daga cikin 'yan bindigar a wani daji da ke garin Awkunanaw, inda suka gudu domin buya.
Sanarwar ta ce dama a ranar Alhamis, jami'a 'yan sandan suka fatattaki wasu 'yan bindiga da suka yi yunƙurin kwace wata mota daga hannun wani direba, inda maharan suka gudu tare da munanan raunukan harbin bindiga a jikinsu.
Daga nan ne kuma 'yan sanda suka ce suka fara farautar maharan, inda suka gano makamai masu tarin yawa a lokacin binciken nasu
Kwamishinan 'yan sandan jihar CP Ahmed Ammani ya tabbatar da cewa jami'an 'yan sandan jihar da sauran jami'an tsaro ba za su yi kasa a gwiiwa ba har sai sun tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar, ta yadda mazauna jihar za su rika fita harkokin kasuwancinsu a kowacce rana.
Kungiyar masu tayar da kayar baya ta IPOB dai na tilasta wa mutane zaman gida a wasu ranaku, a wasu yankuna da ke kudu maso gabashin kasar.

Asalin hoton, FACEBOOK/JAMB
Yarinyar nan da ake zargi da kara wa kanta maki a jarrabawar JAMB ta amince cewa da kanta da sauya sakamakon jarrabawar.
Ejikeme Mmesoma mai shekarar 19, wadda tsohuwar ɗaliba ce a makarantar 'Anglican Girls’ Secondary School' a jihar Anambra, ta bayyana yadda ta kara wa kanta maki a takardar sakamakon jarrabawar.
A 'yan kwanakin nan, batun ya janyo ce-ce-ku-ce, tun bayan da hukumar da ke shirya jarrabawar ta karyata makin da dalibar ta yi ikirarin samu a jarrabawar.
Ita dai hukumar JAMB ta ce dalibar ta samu maki 249, saɓanin maki 362 da take ikirarin samu, to sai dai a lokacin ɗalibar ta kafe cewa sakamakon da take ikirari shi ne na gaskiya.
Lamarin da ya sa gwamnan jihar Anambra Charles Soludo ya kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan lamarin.
Kwamitin ya gayyaci ɗalibar da shugabar makarantar da kuma jami'an hukumar JAMB domin jin bahasin kowanne ɓangare.
Hukumar ta JAMB ta ce sakamakon da ɗalibar ke ikirarin samu wanda ke dauke da maki 362 sakamako ne na bagi, ba na gaskiya ba.
Haka kuma JAMB din ta bayyana yadda Ejikeme Mmesoma ta yi ta yunkurin neman samakamon jarrabawar tata a shafin hukumar cikin sa'o'i da dama, kuma a duk wadannan lokuta sakamako daya take samu daga hukumar wanda ke nuna cewa ta samau maki 249.
To sai dai Ejikeme Mmesoma ta shaida wa kwamitin cewa ta amince da wanna bayani da hukumar jami'an hukumar ta JAMB suka yi wa kwamitin.
Tana mai cewa da kanta ta kara makin sakamakon jarrabawar tata.
Ta ce ta yi amfani da wayarta wajen sauya sakamakon jarrabawar, kafin ta fitar da takardar sakamakon jarrabawar.
Kwamitin ya yi kokarin gano dalilin ɗalibar na aikata wannan laifi, to sai dai ta ce ba ta da wani kwakkwararn dalili.
Daga ƙarshe kwamitin ya bukaci ɗalibar ta gaggauta neman afuwa bisa wannan laifi da ta aikata, ta hanyar rubuta wasikar neman afuwa ga hukumar JAMB da hukumar Makarantar da ta kammala, sannan zuwa ga gwamnatin jihar Anambar.
Sannan kwamitin ya bukaci dalibar ta je a duba lafiyar kwakwalwarta, tare da yin kira da duka ɗaliban da ke rubuta jarrabawar da su tsaya inda dokokin hukumar ya iyakance musu.

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanonin dillancin labaran Iran guda biyu sun rawaito cewa an rataye wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a wani mummunan hari da aka kai wani masallacin mabiya mazhabar Shi'a a kudancin birnin Shiraz a bara.
Harin - wanda kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaiwa, ya kashe akalla mutum 13 tare da jikkata wasu da dama.
Tun a watan Maris, aka yanke musu hukuncin bisa tuhumarsu da kawo cikas ga tsaron kasa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce a wannan shekarar kadai an zartar da hukuncin kisa kan mutum 200 a Iran.