An zargi sojojin Sudan da kai harin bam a harabar wata jami’a
Gwamnatin Congo ta ce mutane 10 ne aka kashe 'yan asalin Jamhuriyar dimokaradiyyar Kwango a wani harin da sojoji suka kai a harabar wata jami'a a Sudan.
An ce mutanen sun mutu ne a wani harin bam da aka kai da yammacin ranar Lahadi a jami'ar kasa da kasa ta Afirka ta birnin Khartoum.
Babu tabbacin cewa wadanda harin bam din na ranar Lahadi ya rutsa da su daliban jami'ar ne. Yana yiwuwa ya kasance yanki ne da ke ciki ko kuma kusa da jami’ar inda ’yan kasashen waje daban-daban suka nemi mafaka.
Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya, Filippo Grandi ya wallafa a shafinsa na twitter cewa ‘yan gudun hijira 10 ne suka mutu a wani hari da aka kai a birnin Khartoum, ba tare da yin wani karin bayani ba.
Dakarun RSF da na sojojin Sudan sun shafe makonni suna fafatawa a babban birnin Sudan.
Dakarun na RSF na da sansanoni a wurare da dama a fadin birnin, inda sojoji suka saba kai masu hari daga sama.