APC ta yi alla-wadai da rusau ɗin gwamnatin Abba a Kano

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. An zargi sojojin Sudan da kai harin bam a harabar wata jami’a

    ...

    Asalin hoton, google

    Gwamnatin Congo ta ce mutane 10 ne aka kashe 'yan asalin Jamhuriyar dimokaradiyyar Kwango a wani harin da sojoji suka kai a harabar wata jami'a a Sudan.

    An ce mutanen sun mutu ne a wani harin bam da aka kai da yammacin ranar Lahadi a jami'ar kasa da kasa ta Afirka ta birnin Khartoum.

    Babu tabbacin cewa wadanda harin bam din na ranar Lahadi ya rutsa da su daliban jami'ar ne. Yana yiwuwa ya kasance yanki ne da ke ciki ko kuma kusa da jami’ar inda ’yan kasashen waje daban-daban suka nemi mafaka.

    Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya, Filippo Grandi ya wallafa a shafinsa na twitter cewa ‘yan gudun hijira 10 ne suka mutu a wani hari da aka kai a birnin Khartoum, ba tare da yin wani karin bayani ba.

    Dakarun RSF da na sojojin Sudan sun shafe makonni suna fafatawa a babban birnin Sudan.

    Dakarun na RSF na da sansanoni a wurare da dama a fadin birnin, inda sojoji suka saba kai masu hari daga sama.

  2. Iran ta sake buɗe ofishin jakadancinta a Saudiyya bayan shekara bakwai

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Rahotanni daga Saudiyya na cewa Iran ta sake buɗe ofishin jakadancinta a birnin Riyadh, shekaru bakwai bayan rufe shi.

    Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayar da rahoton cewa, Tehran ta aika da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Reza Bekdli domin halartar bikin, wanda kuma ya samu halartar babban jami'in harkokin wajen Iran Hassan Zarnegar.

    Har ila yau ƙaramin sakatare na ma'aikatar harkokin waje mai kula da harkokin ofishin jakadancin, Ali Al-Youssef ya halarci bukin daga ɓangaren Saudiyya.

    Sake buɗe ofishin ya zo daidai da ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai ƙasar, da nufin ƙarfafa alaƙar Washington da ƙasar mai arziƙin man fetur yayin da ita kuma Saudiyya ke ƙara kusantar abokan gabar Amurka.

    Har yanzu dai Saudiyya ba ta tabbatar da ranar buɗe ofishin jakadancinta a Tehran ba ko kuma zaɓen wanda zai zame mata jakada.

    Masarautar ta yanke hulɗa da Iran a shekarar 2016 bayan da masu zanga-zanga a ƙasar suka kai hari kan ofisoshin jakadancin Saudiyya, sakamakon hukuncin kisa da aka yanke wa malamin Shi'a na Saudiyya Nimr al-Nimr.

  3. Hotunan Karim Benzema wanda ya koma Al-Ittihad ta Saudiyya

    ...

    Asalin hoton, Twitter/@ittihad_en

    Ɗan ƙwallon ƙafar na Faransa, mai shekara 35, Karim Benzema ya amince da kwantaragin zaman shekaru uku a ƙungiyar ta Al-Ittihad.

    Ya bar Real Madrid bayan shekara 14.

    ...

    Asalin hoton, Twitter/@ittihad_en

    ...

    Asalin hoton, Twitter/@ittihad_en

    ...

    Asalin hoton, Twitter/@ittihad_en

  4. Al-Ittihad ta kammala ɗaukar Karim Benzema

  5. Majalisar Wakilan Najeriya ta ce ƙaddamar da jirgin Nigeria Air 'yaudara' ce

    ...

    Shugaban kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan harkokin sufurin jiragen sama, Nnolim Nnaji, ya ce kaddamar da kamfanin Najeriya Air da aka yi yaudara ce.

    Ya bayyana hakan ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama wadanda suka ce ba su da masaniya kan kaddamar da jirgin.

    Ministan sufurin jirgin sama a gwamnatin da ta gabata, Hadi Sirika ne ya ƙaddamar da jirgin a mako na ƙarshe na mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

    Sai dai lamarin ya haifar da ze-ce ku-ce kasancewar jirgin ɗaya ne tal aka bayyana a matsayin jirgin kamfanin, inda daga baya ake rinƙa raɗe-raɗin cewa jirgin ya yi ɓatan-dabo.

    A nasu bangaren kuma kwamitin majalisar dattijan Najeriyar mai kula da harkokin sufurin jiragen sama ya soki kaddamar da kamfanin jirgin na Najeriya Air, inda ya ce lamarin wata rufa-rufa ce.

    Mambobin kwamitin sun bayyana rashin jin dadinsu game da kaddamar da jirgin na kasa a wata ganawa da babban sakataren ma'aikatar sufurin jiragen sama, Emmanuel Meribole da babban darektan rikon kwarya na kamfanin Najeriya Air, kyaftin Dapo Olumide da kuma shugabannin hukumomin sufurin jiragen sama.

    Da yake mayar da martani ga kwamitin, Kyaftin Dapo Olumide ya ce an kaddamar da jirgin ne a wannan lokacin domin a tabbatar wa 'yan Najeriya cewa lamarin ba karya ba ne.

    Najeriya wadda ita ce ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka ba ta da kamfanin jirgi mallakinta.

    Wannan ne ya sanya gwamnatin da ta gabata ta yi yunƙurin samar da kamfanin jirgin wanda aka raɗa wa suna 'Nigeria Air', sai dai an gaza kammala tabbatar da yarjejeniyar bayan da wasu ƴan kasuwa a ɓangaren sufurin jiragen sama na Najeriyar suka shigar da ƙara a kotu suna ƙalubalantar tsarin da aka bi wajen kafa kamfanin.

  6. Wata shida bayan kisan makiyaya a Nasarawa har yanzu ba a yi bincike ba - HRW

  7. Ƴan sanda sun banka wa masu zanga-zanga hayaki mai sa hawaye a Kenya

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ƴan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zanga a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

    Al'umma sun fita kan tituna ne domin nuna adawa kan wasu matakan da gwamnatin kasar ta dauka na sanya sabbin haraji da kuma yin kari a harajin da ke kan wasu kayayyaki da suka hada da man fetur.

    Ɗaya daga cikin mahimman matakan da ake jayayya a kai da ke kunshe a cikin sabon kudurin kashe kudi na gwamnati shi ne sabon harajin asusun gidaje na kashi 3 kan duka ma'aikata masu albashi da kuma kara yawan harajin kan kudin man fetur zuwa kashi 16.

    Har ila yau, kudurin ya ɗora haraji a kan kayan ado da kudaden crypto da haraji kan kudin da masu tasiri a kafofin sada zumunta ke samu. Duk suna daga cikin matakan da 'yan Kenya da dama ke adawa da su.

    Gomman masu zanga-zangar sun nemi yin taro a wani wurin shakatawa da ke tsakiyar birnin Nairobi kafin su yi tattaki zuwa majalisar dokokin kasar domin yin kira ga 'yan majalisar da su yi watsi da kudurin harajin.

    Kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa an kama wasu daga cikin masu zanga-zangar.

    A ranar Alhamis ne ‘yan majalisar za su yi muhawara kan kudirin dokar, a daidai lokacin da shugaban kasar William Ruto da mataimakinsa Rigathi Gachagua suka yi gargadi ga masu adawa da kudurin.

  8. Benzema ya koma Al-Ittahad in ji wata majiya daga kungiyar

  9. Rasha ta ce an kashe sojojinta 71 cikin kwana uku

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Rasha ta amince cewa an kashe sojojinta 71 a lokacin da suke mayar da martani kan harin da Ukraine ta kai a birnin Bakhmut da ke kasar Ukraine.

    Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya ce, "An yi kwana uku gwamnatin Ukraine na kai farmaki, wanda ta dade tana shan alwashin za ta yi a bangarori daban-daban."

    "Adadin mutanenmu 71 aka kashe inda 210 suka jikkata" in ji Shoigu.

    A ranar Litinin ne Rasha ta ce ta dakile wani gagarumin harin da aka kai mata, yayin da Ukraine ta yaba da nasarorin da ta samu a yankin Bakhmut da kewayen gabashin kasar.

  10. APC ta yi Allah wadai da rusau ɗin gwamnatin Abba a Kano

    hh

    Asalin hoton, Fai'izu Alfindiki/Facebook

    Babbar jam'iyyar adawa a Kano wato APC ta yi Allah wadai kan abin da ta bayyana da cewa "kai farmaki ne kan dukiyoyin al'umma" da gwamnatin NNPP ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ke yi a jihar.

    A cikin wata sanarwa da muƙaddashin shugaban jam'iyyar na jihar Kano, Hon. Shehu Maigari ya aika wa manema labarai, APC ta ce ''a yau Kano ta kasance abin tausayawa sakamakon halin da jam'iyyar NNPP ta jefa jihar ciki''.

    Jam'iyyar ta APC ta zargi NNPP da gwamnatin Abba Gida-Gida da jefa 'yan kasuwa cikin mawuyacin hali, inda ta ce harkokin kasuwancin Kano sun tsaya cik.

    APC ta kuma yi zargin cewa matakin da NNPP ta ɗauka na rusa wasu wuraren kasuwanci a jihar ya sanya wasu matasa a Kano sun zama ɓarayi, inda ta ce matasan suna yawo da makamai tare da fasa shagunan mutane domin satar kaya.

    Haka kuma jam'iyyar adawar ta yi kira ga iyayen yara musamman matasan da ta ce gwamnatin NNPP na amfani da su wajen ɓarnata kayan al'umma, su ja kunnen 'ya'yan nasu.

    Ita dai jam'iyyar NNPP tare da Abba Gida-Gida sun sha alwashin ƙwace wurare da suka ce mallakar al'ummar Kano amma gwamnatin APC ta sayar a lokacin da take kan karagar mulkin jihar.

    Kwanaki ƙalilan bayan rantsar da sabon gwamnan na Kano, Abba Kabir Yusuf ya fara rusa wasu gine-gine a filayen da ya ce na al'ummar Kano ne, a cikinsu har da filin sukuwa da otal din Daula da sansanin alhazan jihar da Babban Filin Idin Kano.

  11. Kotu ta ce masu ƙalubalantar nasarar Tinubu su biya miliyan goma-goma

    Tinubu

    Asalin hoton, FACEBOOK/ BOLA AHMED TINUBU

    Babbar kotun tarayya da ke Abuja baban birnin Najeriya ta yi watsi da ƙasar da wasu mazauna birnin suka shigar a gabanta suna neman ta hana rantsar da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu.

    Yayin da yake yanke hukuncin ranar Talata, alƙalin kotun, Mai shari'a Inyang Ekwo, ya umarci masu ƙarar da kowannensu ya biya naira miliyan 10 ga ministan shari'a kuma Atoni janar na ƙasar.

    Masu ƙarar dai na iƙirarin cewa shugaban ƙasar Bola Tinubu bai samu samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a baban birnin tarayyar Abuja, dan haka suke ganin bai cancanci zama shugaban ƙasar ba.

    Mai shari'a Ekwo ya ce masu karar ba su da 'yancin shigar da ƙarar a kotun, yana mai cewa a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ne kawai ya kamata a shigar da ƙasar, a maimakon babbar kotun tarayyar da ke Abuja.

  12. Tottenham ta dauki Ange Postecoglou sabon kocinta

  13. Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗa masu bayar da shawara 20 ga Tinubu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dattawan Najeriya ta amince da naɗa mutum 20 da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya aike mata domin amincewarta ya naɗa su a matsayin mashawartansa.

    Matakin na zuwa ne bayan da shugaban ya aike wa majalisar wasiƙar neman amincewa majalisar domin naɗa mutanen.

    To sai dai a wasiƙar da shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ya karanto a gaban majalisar a lokacin zamanta na ranar Talata, babu sunayen mutanen a cikinta.

    Amma ana kallon sabbin naɗe-naɗen da shugaban ƙasar zai yi a matsayin wata manuniya kan inda alƙiblar gwamnatinsa za ta fuskanta wajen magance tarin matsalolin da ƙasar ke fuskanta kama daga matsalar tsaro da tattalin arziki.

  14. Abu bakwai da gwamnatin Najeriya ta cimma da 'yan ƙwadago

  15. Obasa ya sake zama kakakin majalisar dokokin jihar Legas karo na uku

    Mudashiru Obasa

    Asalin hoton, Mudashiru Obasa/Wikipedia

    Majalisar dokokin jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta karo na uku.

    Dan majalisar mai wakiltar mazaɓar Agege 1 ya samu nasarar zama kakakin majalisar ne jim- kaɗan baya da gwamnan jihar Babajide Sanwu-Olu ya ƙaddamar da sabuwar majalisar ta 10 da safiyar ranar Talata.

    Majalisar Jihar na da mambobi 40, inda jam'iyyar APC mai mulkin jihar ke da mambobi 38 sai kuma jam'iyyar LP mai hamayyar wadda ke da mambobi biyu.

    Majalisar dokokin jiha dai wani ɓangare ne mai matuƙar muhimmanci ga gwamnatin jiha.

    Wadda ke da alhakin tsara dokokin da amincewa da ƙudurori da wasu naɗe-naɗe da gwamna zai yi a jihar.

  16. EFCC za ta ɗaukaka ƙara kan wanke Oronsaye daga zargin cin hanci

    Mista Steve Oronsaye

    Asalin hoton, EFCC/Facebook

    Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattali arzikin Najeriya zagon ƙasar EFCC ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke, na wanke tsohon shugaban ma'aikata na ƙasa daga zargin halasta kuɗin haram na wajen naira biliyan biyu da hukumar ke yi masa shi da wasu.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce za ta ƙalubalancin hukuncin a gaban kotun ɗaukaka ƙara.

    EFCCn dai na zargin Steve Oronsaye da mutunen da ake zarginsu tare da yin amfani da wasu kamfanoni wajen karkatar da kuɗin gwamnati ta hanyar amfani da kwangilolin bogi.

    Yayin da yake watsi da ƙarar, alƙalin kotun mai shari'a Inyang Ekwo ya ce hukumar EFCCn ta kasa tabbatar da zarge-zargen da take yi wa mista Oronsaye.

    To sai dai a cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya fitar ya ce alƙalin ya yi kuskure, saboda a cewarsa bai yi la'akari da shaidun da masu ƙara suka gabatar ba, a tsawon shari'ar, tare da bahasin da ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙarar Osarenkhoe Afe ya furta da bakinsa a gaban kotun.

    A shekarar 2015 ne hukumar EFFC ta gurfanar da Mista Oronsaye tare da shugaban kamfanin Fredrick Hamilton Global Services Limited, Osarenkhoe Afe da wasu kamfanoni uku bisa zarginsu da yin amfani da wasu kamfanoni wajen karkatar da kuɗin gwamnati ta hanyar amfani da kwangilolin bogi.

  17. An kashe 'yan Kongo a wani hari da aka kai ta sama a Sudan

    as

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Jamhuriyar Dimkoradiyyar Kongo ta ce 'yan ƙasarta 10 ne suka mutu bayan da aka kai hari ta sama kan makarantar da suke a birnin Khartoum na ƙasar Sudan.

    A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar ta ce ta kaɗu matuka da kashe 'yan ƙasarta da ke karatu a jam'iar Afirka da ke Sudan.

    Ministan harkokin wajen Kongo Christophe Lutundula ya ce alamu sun nuna cewa sojojin da ke iko da yankin ne suka kai harin wanda ya yi sandin mutuwar fararen hula masu yawa tare da jikkata da dama, ciki har da 'yan ƙasashen waje.

    Ministan ya ce suna jiran hukumomin Sudan da su yi ƙarin bayani game da faruwar lamarin.

    Birnin Khartoum ya kasance wani fagen daga a yaƙin da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF masu sanya da kayan sarki.

    Gwamnatin ƙasar Kongo ta yi kira da hukumomin bayar da agaji da su taimaka wajen kwashe 'yan ƙasarta da suka maƙale a birnin Khartoum.

  18. Ambaliya ruwa ta halaka sama da fiye da mutum 40 a Haiti

    Ambaliya

    Asalin hoton, REUTERS

    Jami'ai a Haiti sun ce akalla mutum 42 sun rasa ransu tun bayan mamakon ruwan saman da aka yi da ya janyo ambaliyar ruwa.

    Wasu hotuna da gidan talbijin din ƙasar ya yaɗa, sun nuna yadda mutane ke tafiya a kan wani ruwa,da launinsa ya koma ruwan ƙasa.

    Gidaje fiye da 1300 ne ambaliyar ta shafa, yayin da kuma har yanzu ba a ga wasu mutanen ba.

    Ambaliyar ruwan dai ta shafi wurare da dama a ƙasar tare da lalata ababan more rayuwa masu yawa.

  19. Amurka da China sun amince da kyautata dangantaka tsakaninsu

    Amurka China

    Asalin hoton, REUTERS/EPA

    China da Amurka sun yi tsokaci kan ci gaban da aka samu wajen amincewa su ci gaba da hulɗa a tsakaninsu bayan kwashe wasu lokuta suna zaman doya da manja.

    Wata sanarwa da aka fitar bayan taron da manyan jami'an diplomasiyyar ƙasashen suka yi a China, ta bayyana cewa an samu ci gaba sosai a tattaunawar da ƙasashen biyu suka yi.

    Daga cikin batutuwan da sanarwar mai ɗauke da sa hannun mataimakin sakataren ƙungiyar ƙasashen gabashin Asiya da na yankin pacific, ya fitar har da batun 'yancin ɗan adam da kuma halin da ake ciki a Taiwan.

    Ya ce Amurka na kokari sosai wajen daidaita dangantakarta da China.

  20. Sallama

    Masu bin mu a wannan shafi Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku wannan rana ta Talata.

    Barkanmu da safiya, fatan an wayi gari lafiya, ku biyo mu a wannan shafi domin sanar da ku halin da duniya ke ciki.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.