'Yan sanda sun kuɓutar da yara tara a Zamfara

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Yadda jami'an NDLEA suka gano tare da lalata matattarar tabar wiwi a Edo

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeirya, NDLEA ta ce ta yi nasarar lalata sama da tan uku na tabar wiwi a wani daji da ke jihar Edo tare da sauran kayan maye da ake shigar da su ƙasar daga Canada.

    Hukumar ta NDLEA din ta shaida wa BBC cewa cikin miyagun kwayoyin da suka yi nasarar kamawa har da wadan da aka yi safararsu don kai su ga mayaƙan boko haram, a jihar Borno.

    Ga ƙarin bayani cikin rahoton Khalifa Shehu Dokaji.

  2. 'Gwamnatin Matawalle ta bar rarar naira biliyan 20 ga sabuwar gwamnatin Zamfara'

    .

    Asalin hoton, @BELLOMATAWALLE1

    Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Zamfara ta yi iƙirarin gwamnatin Muhammad Bello Matawalle ta bar wa sabuwar gwamnatin PDP, ƙarƙashin gwamna Dauda Lawal Dare kimanin naira biliyan 20.5 da kuma dala miliyan 1.9 a lalitar gwamnati.

    APC cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta, Yusuf Idris Gusau ya sanyawa hannu, ta zargi sabuwar gwamnatin da musanta karɓar kuɗaɗen.

    Ta kuma mayar wa da sabuwar gwamnatin martani kan zargin tsohon gwamna, Matawalle da sama da faɗi da wasu motocin alfarma waɗanda ta ce an raba su ne ga amfanin ma'aikatu da hukumomin gwamnatin jihar.

    Tun farko dai gwamnatin jihar ta Zamfara ta bai wa tsohon gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle wa'adin kwanaki biyar da ya bayar da bahasi kan motocin alfarma na biliyoyin naira da aka sayo daga susun gwamnatin jihar, kuma suka yi ɓatan-dabo.

    A cewar sanarwar, "idan har sun tashi tabbatarwa, muna sa ran za su haɗa kai da ma'aikatu da hukumomin gwamnati domin sanin inda motocin suke a maimakon damun Matawalle wanda tuni ya ci gaba da tafiyar da rayuwarsa.

    Sanarwar ta kuma bayyana sabon gwamnan a matsayin wanda ba shi da alƙibla.

    Ta kuma ƙaryata zargin cewa tsohon gwamnan bai miƙa takardun da ya kamata ba kafin barin mulki tana mai cewa "babu wani tsohon gwamna da zai bar kujerarsa ba tare da miƙa takardu ba."

    A cewarta Matawalle ya gabatar da duk wasu takardu ga sabon gwamna ƙarƙashin kwamitin karɓar mulkin da ya wakilce shi.

    APC ta kuma zargi sabon gwamnan da ƙin nuna damuwa kan kashe-kashe da sace-sacen mutane a jihar da kuma yadda a cewarta ya bar lamuran jihar ya koma halartar taruka a Abuja da Bauchi - wanda ke nuna gazawar gwamnati.

  3. 'Yaƙi da Amurka bala'i ne da duniya ba za ta iya jurewa ba'

    .

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Li Shangfu ya zama minsitan tsaro a watan Maris

    Ministan tsaron China ya ce yaƙi da Amurka zai zama wani bala'i da ba za a iya jurewa ba ga duniya.

    Ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko tun bayan da ya hau kan muƙamin.

    A wani taron tsaro, Janar Li Shangfu ya ce wasu ƙasashe suna tseren shigar da makamai nahiyar Asiya.

    Tun farko Amurka ta yi zargin rashin tsaro kan wani jirgin ruwan China da ke watangaririya kusa da wani jirgin ruwan yaƙin Amurka a yankin Taiwan.

    A jiya Asabar ne, rundunar sojin ruwan Amurka ta ce wani jirgin ruwan China ya shiga hanyar da ba ta dace ba kusa da wani jirgin ruwan Amurka yayin da yake ratsa mashigin Taiwan tare da jiragen ruwan Canada.

    China dai ta soki duka ƙasashen biyu sai dai Amurkar da Canada sun ce suna tafiya ne a inda dokokin ƙasa da ƙasa suka amince da.

    Janar Li wanda ya zama ministan tsaro a Maris ya zargi Amurka da tafiya kan zamanin cacar baka abin da ya ce yana barazana sosai ga tsaro.

  4. Messi da Ramos sun buga wasan karshe a PSG

  5. Muna neman ƙarin kashi 200 kan albashinmu – Likitocin Najeriya

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a asibitocin gwamnatin Najeriya sun dage kan ƙarin albashi na kashi 200.

    Ƙungiyar ta bayyana haka ne makwanni biyu bayan janye yajin aikin gargaɗi na yini biyar da suka yi domin jiran gwamnati ta yi wani abu kan buƙatunsu.

    Cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta ce ba za ta amince da ƙarin albashi na kashi 35 cikin 100 da gwamnatin da ta shuɗe ta yi ba sannan kuma sauran ɓuƙatunsu har yanzu ba a yi komai a kai ba.

    Janye wani ƙudiri da ke neman hana likitocin da suka kammala karatu a baya-bayan nan ficewa daga ƙasar har sai sun yi aikin shekara biyar da ɗiban likitoci aiki domin manye ƙwararrun da suka daina aiki da kuma gaggauta inganta asibitocin gwamnati wasu ne daga cikin buƙatun ƙungiyar.

    Likitocin na son Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta warware matsalolinsu ya kuma aiwatar da matakan rage wa ƴan Najeriya raɗaɗin janye tallafin mai.

    Shugaban ƙungiyar Dr Emeka Orji ya buƙaci sabuwar gwamnati da ta fifita batun barin ƙasar da likitoci suke yi.

    Akwai likitoci 10,000 da ke aiki a asibitocin gwamnati zuwa Nuwamban bara sai dai rashin albashi mai kyau da ƙarancin kayan aiki da kuma rashin walwalar ma'aikatan lafiya ya sa ƙwararru a ɓangaren lafiya na neman wasu damarmakin a ƙasashen waje.

  6. Cire Tallafin Mai: Gwamnatin Najeriya na ganawa da TUC

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta shiga wata ganawa da ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Fadar gwamnati domin tattauna batun cire tallafin man fetur.

    Wannan ɗorawa ne kan ganawar da suka yi da ƙungiyar NLC wadda aka tashi ba tare da cimma wata matsaya ba.

    A taron, NLC ta nemi gwamnati ta koma sayar da man fetur kan farashin da aka saba kafin ta koma tattaunawa da kungiyar.

    A taron na yau, tawagar gwamnatin tarayya ta samu jagorancin Sakataren gwamnati, Sanata Goerge Akume. Sauran sun haɗa da Gwamnan Babban banki, Godwin Emefiele da tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomhole da shugaban Kamfanin mai na Najeriya, Mele Kyari.

    Akwai kuma mambobin ƙungiyar TUC guda bakwai ƙarƙashin jagorancin Mista Festus Osifo.

  7. Hazard ya amince Real Madrid ta soke kwantiraginsa

  8. 'Yan sanda sun kuɓutar da yara tara a Zamfara

    ss

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kubutar da wasu kannana yara tara da 'yan bindiga suka sace.

    A cikin wata sanarwa da Rundunar 'yan sandan jihar ta fitar mai ɗauke da sa hannun kakakin rundunar jihar ASP Yazid Abubakar, ya ce a ranar 3 ga watan Yuni ne rundunar ta samu bayanai daga dagacin ƙauyen Gora Namaye cewa 'yan bindiga sun sace wasu yara maza da mata waɗanda suka tafi neman itace a jeji.

    Sanarwar ta ce bayan samun labarin ne 'yan sanda tare da hadin gwiwwa jami'an tsaro suka ƙaddamar da bincike domin ceto yaran, lamarin da ya sa suka samu nasarar ceto yaran tara, tare da mayar da su hannun iyayensu.

    Rundunar ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo maharan tare da gurfanar da su a gaban kotu.

    A ranar Asabar ne 'yan bindigar suka kai hari tare da sace yaran a ƙauyen Gora da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Maradun a jihar zamfara.

  9. Ta yaya jiragen ƙasa uku suka yi hatsari a Indiya?

  10. Gwamnatin Zamfara ta bai wa Matawalle wa'adin mayar da motocin alfarma na biliyoyin naira

    Matawalle

    Asalin hoton, Zamfara State Govt

    Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta bai wa tsohon gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle wa'adin kwanaki biyar da ya bayar da bahasi kan motocin alfarma na biliyoyin nairori da aka sayo daga susun gwamnatin jihar, kuma suka yi ɓatan-dabo.

    A cikin wata sanarwa da babban mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin yaɗa labarai Sulaiman Bala Idris ya fitar ya ce sabuwar gwamnati ta samu hujja da alaƙaluman kuɗin da aka ware wajen sayo wasu manyan motocin alfarma.

    Sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta samu hajja mai ƙarfi da ke nuna cewa tsohon gwamnan ya ware biliyoyin nairori wajen sayo manyan motocin alfarma da gwamnati za ta yi amfani da su.

    Sai dai sanarwar ta ce sabuwar gwamnati ba ta samu ko da mota guda cikin motocin da tsohuwar gwamnatin ta ce ta sayo, kamar yadda bayanai suka nuna.

    A baya-bayan nan dai tsohon gwamnan na ta samun taƙun-saka da hukumar yaki da cin hanci da rasha EFCC bayan da ya zargi shugaban hukumar Abdurrasheed Bawa da aikata almundaha iri-iri.

    A cikin wata sanarwa da EFCC ta fitar cikin makonni da suka gabata, ta ce tana bincikar gwamna Matawalle ne kan zargin karkatar da N70bn da bayar da kwangiloli ba bisa ƙa'ida ba.

    "Kuɗin wanda aka samu a matsayin bashi daga wani banki domin aiwatar da ayyuka a sassan ƙananan hukumomin jihar, ana zargin gwamnan ya karkatar da shi ne," kamar yadda sanarwar EFCCn ta bayyana.

    A martanin da ya mayar tsohon gwamnan ya kalubalanci Bawa da ya sauka daga kan kujerarsa ya bayar da damar a bincike shi ya ga irin abubuwan da za a bankaɗo.

    Cikin wata hira da ya yi da BBC Matawalle ya ce “Bincike gaskiya ne, ba a hana a yi bincike ba, amma kuma ya kamata binciken ya zamo na kowa da kowa, don bai kamata a ce komai sai dai a ambaci gwamna ba, ai ba gwamna ne kadai ke da asusun ajiya ba.”

    Ya ce, “Kamar yadda shugaban EFCC ya ce ya tanadi takardu na gwamnoni, to muna so ya nuna wa duniya takardu na wadanda yake aiki tare da su, sannan shi kansa ya kamata ya rubuta wa kansa takarda don a bincike shi saboda akwai zarge-zarge masu dumbin yawa a kansa.”

  11. ''Yan bindiga sun halaka fiye mutum 30 a Sokoto'

    ss

    Asalin hoton, others

    'Yan bindiga sun far wa ƙauyukan Raka da Bilangawa da Tudun Anga a yankin ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto da ke arewa maso yamacin Najeriya.

    Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa akalla mutum 30 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar lamarin. Mazauna ƙauyukan sun shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun yi wa ƙauyukan ƙawanya a ranar Asabar da rana inda suka riƙa buɗe wa al'umma wuta.

    Wani mazaunin ƙauyen Raka da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa maharan sun je kauyen Raka a kan babura inda suka yi wa kauyen kawanya tare da buɗe wuta.

    ''A ƙauyen Raka sun kashe mutum 14, sannan cikin garin Bilingawa sun kashe mutum 18, sai garin Raka ƙarama inda aka kashe musu mutum biyu, sai garin Tudun Anza sun kashe mutum biyu, shi ne abin da ya kawo adadin mutanen da aka kashe a ƙauyukan ya kai mutum 36'', kamar yadda wani mazaunin ƙauyen Raka ya bayyana wa BBC.

    Shi ma wani mazaunin ƙauyen ya shaida wa BBC cewa yanzu haka ana cikin zaman ɗar-ɗar a ƙauyukan da ke maƙwabtaka da ƙauyukan da lamarin ya faru.

    BBC ta tuntuɓi kakakin Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ASP Ahmad Rufai, wanda ya ce ba shi da cikakken labarin abin da ya faru, sai dai ya ce zai yi wa BBC ƙarin bayani da zarar ya kammala tattara bayanai game da harin.

    Hare-haren 'yan bindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya na yunkurin dawowa bayan da a baya suka ɗan lafa.

    Ko a ranar Asabar da safe ma rahotonni sun ce an sace wasu ƙananan yara fiye da 30 a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

  12. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 04/06/23

    Badariyya Tijjani Kalarawi tare da Haruna Ibrahim Kakangi ne suka gabatar da shirin na wannan mako

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  13. Cire tallafin mai: Kungiyar ma'aikatan lantarki ta Najeriya za ta shiga yajin aiki

    Lantarki

    Asalin hoton, TCN

    Ƙungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta Najeriya ta ce za ta tsunduma yajin aiki sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

    Ƙungiyar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan da ƙungiyar kwadogo ta ƙasar NLC ta sanar da matakin tsunduma yajin aiki sakamon cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi, lamarin da ta ce ya haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.

    Shugaban ƙungiyar mai lura da shiyyar birnin tarayya Abuja da Kogi, Godfrey Aba ya tabbatarwa da BBC cewa ƙungiyar za ta shiga yajin aikin daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni, matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta janye matakin cire tallafin man ba.

    Ya ƙara da cewa ''ƙungiyar za ta shiga yajin aikin ne har sai gwamnati ta janye matakin da ta ɗauka''.

    A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sannun muƙaddashin sakataren ƙungiyar na ƙasar Dominic Igwebike, ta yi kira ga mambobinta da su yi biyayya ga matakin ƙungiyar na tsunduma yajin aiki a tsakiyar makon da ke tafe.

    s

    Asalin hoton, NUOEE

    Ƙungiyar ƙwadado ta ƙasar NLC dai ta ce za ta fara yajin aiki tare da zanga-zanga daga ranar Laraba mai zuwa a wani mataki na nuna rashin amincewarta kan cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

    Sabon Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ne ya sanar da matakin cire tallafin man fetur ɗin a cikin jawabin da ya gabatar cikin makon jiya a lokacin bikin rantar da shi.

    Ita ma dai kungiyar 'yan jarida ta ƙasar NUJ ta sanar da ɗaukar makamancin wannan mataki a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.

  14. Benzema zai bar Real Madrid bayan shekara 14

    Benzema

    Asalin hoton, Getty Images

    Fitaccen ɗan wasan gaban Real Madrid Karim Benzema zai bar ƙungiyar bayan shafe shekara 14 a Santiago Bernabéu.

    Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or a shekarar da ta wuce, ya fara taka leda ne a Madrid a shekarar 2009 bayan da ƙungiyar ta ɗauke shi daga Lyon.

    Benzema mai shekara 35 zai bar Real Madrid ne bayan da kwantiraginsa da ƙungiyar ya zo ƙarshe a kakar da muke ciki.

    Benzema ya ci manyan kofuna 25 a tsawon shekaru 14 da ya yi a ƙungiyar, ciki har da kofunan Gasar Zakarun Turai na Champions Leagues biyar, tare da kofunan Laliga huɗu.

    Ƙungiyar Real Madrid ta ce ''Benzema zaƙaƙurin ɗan wasa ne mai kyakkaywar mu'amala, kuma ya ɗaga martabar ƙungiyarmu, dan haka yana da damar fayyace makomarsa''.

    Dan wasan ya buga wa Real Madrid wasa 647, ya kuma zira ƙwallaye 353, shi ne ɗan wasa na biyu da ya fi ci wa ƙungiyar ƙwallo bayan Cristiano Ronaldo.

    Ana sa ran wasansa na ƙarshe a ƙungiyar shi ne wanda Real Madrid za ta kara da Athletic Bilbao a yau Lahadi a wasan ƙarshe na gasar Laliga ta kakar bana.

    Ana dai rade-radin cewar ɗan wasan zai koma taka-leda a ƙasar Saudiyya bayan da ya samu tayi mai gwaɓi daga wata ƙungiya a ƙasar.

  15. Amsoshin Takardunku

    Shin kun san me ake nufi da cire tallafin man fetur?

    Shirin namu na wannan makon wanda Rabi'atu Kabir Runka ta gabatar ya duba batun cire tallafin man fetur, da abin da hakan ke nufi ga tatalin arzikin Najeriya.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  16. OPEC za ta yi taro don duba yiwuwar rage yawan man da take fitarwa

    OPEC

    Asalin hoton, EPA

    Ƙungiyar ƙasashe Masu Arzikin Man Fetur ta OPEC za ta gudanar da taro a yau Lahadi tare da ƙawayenta domin tattauna batun rage yawan man da ƙungiyar ke fitarawa zuwa kasuwannin duniya.

    OPEC ta shirya taron ne a daidai lokacin da farashin man ke faɗuwa a kasuwannin duniya sakamon matsin tattalin arziki da mafiya yawan ƙasashen duniya ke fuskanta, lamarin da ya haifar da rage yawan buƙatar man a ƙasashen.

    Ministocin ƙasashe mambobin ƙungiyar 13 tare da ƙawayenta da Rasha za su gana a shalkwatar ƙungiyar da ke birnin Vienna domin tattaunawa game da batun.

    A watan Afrilun da ya gabata ne ƙungiyar ta rage adadin man da take fitarwa zuwa kasuwannin duniya a wani mataki na farfado da farashin man a kasuwannain duniya.

  17. Mayaƙan al-Shabab sun kashe sojoji Uganda 54

    Uganda

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya ce an kashe sojojin ƙasarsa 54 a wani hari da mayaƙan ƙungiyar al-Shabbab suka kai a watan daya gabata.

    Mista Museveni ya ce wannan babban rashi ne a wani hari guda da aka kai wa tawagar sojojin ƙasarsa da ke aiki da sojoji haɗaka na ƙungiyar tarayya Afirka domin wanzar da zaman lafiya a Somaliya.

    Mayaƙan na al-Shabab sun afka wa sansanin sojojin ne, lamarin da ya sa suka kashe da dama daga cikinsu.

  18. Rasha ta ƙaddamar da sabbin hare-hare zuwa Ukraine

    Rasha

    Asalin hoton, Reuters

    Rasha ta ƙaddamar da wasu hare-hare ta sama a Kyiv babban birnin ƙasar Ukraine da kuma wasu birane a arewa da gabashin ƙasar a yau Lahadi.

    Aƙalla mutum 20 sun jikkata a wani harin da ya faɗa kan wani ginin da mutane ke zaune a cikinsa a birnin Dnipro da ke kudancin ƙasar.

    Ana fargabar mutane da dama sun maƙale a cikin baraguzan ginin.

    Wani babban jami'in soji a Ukraine ya ce an kakkaɓo duk abubuwan da aka harba cikin birnin Kyiv.

    Mazauna wuraren sun ce sun hango fashewar abubuwan a sararin samaniyar birnin cikin daren da ya gabata.

  19. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna iya bin mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.

    Mu je zuwa ...