Yadda aka kashe mutane bayan ɓarkewar rikici a masallacin Addis Ababa
An kashe mutum uku tare da jikkata wasu da dama bayan tashin hankalin da ya barke a daya daga cikin manyan masallatai a Addis Ababa, babban birnin Habasha a ranar Juma'a, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Lamarin ya biyo bayan takun saka da aka kwashe kwanaki ana yi tsakanin mabiya addinin musulunci da jami’an tsaro.
Shaidu sun bayyana wa BBC cewa, sun ga jami’an tsaro suna harbi a inda suka jikkata wasu da dama a kusa da babban masallacin Anuwar.
Hukumomi sun ce zanga-zanga ce ake gudanarwa a lokacin amma shaidu sun ce jami’an tsaro sun yi harbin ba tare da wani dalili ba.
An fara zaman dar-dar ne a lokacin da musulmi suka fara gudanar da zanga-zanga a makon da ya gabata domin nuna bacin rai kan rusa masallatai da hukumomin yankin suka ayyana a matsayin an gina su ba bisa ka'ida ba da kuma neman a gaggauta dawo da su.
Rundunar hadin gwiwa ta tsaro ta gwamnati ta ce jami’an tsaro 63 sun ji raunuka.
A makon da ya gabata an kashe masu zanga-zanga biyu a wani masallaci da ‘yan sanda suka yi yunkurin tarwatsa zanga-zanga; bayan haka kuma aka kama sama da mutum dari da hukumomi suka yi zargin shirya zanga-zangar.
A watan Fabrairu hukumomi sun yi artabu da Cocin Orthodox, wadda ita ce daya babbar kungiyar addinin.
Rikicin da ya barke ya janyo asarar rayuka da dama kuma tun lokacin aka dakile wasu shafukan sada zumunta a kasar.