Raɗe-raɗin na mallaki naira tiriliyan tara tsagwaron ƙarya ne – Gwamnan Zamfara

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad, Haruna Kakangi and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Yadda aka kashe mutane bayan ɓarkewar rikici a masallacin Addis Ababa

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    An kashe mutum uku tare da jikkata wasu da dama bayan tashin hankalin da ya barke a daya daga cikin manyan masallatai a Addis Ababa, babban birnin Habasha a ranar Juma'a, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

    Lamarin ya biyo bayan takun saka da aka kwashe kwanaki ana yi tsakanin mabiya addinin musulunci da jami’an tsaro.

    Shaidu sun bayyana wa BBC cewa, sun ga jami’an tsaro suna harbi a inda suka jikkata wasu da dama a kusa da babban masallacin Anuwar.

    Hukumomi sun ce zanga-zanga ce ake gudanarwa a lokacin amma shaidu sun ce jami’an tsaro sun yi harbin ba tare da wani dalili ba.

    An fara zaman dar-dar ne a lokacin da musulmi suka fara gudanar da zanga-zanga a makon da ya gabata domin nuna bacin rai kan rusa masallatai da hukumomin yankin suka ayyana a matsayin an gina su ba bisa ka'ida ba da kuma neman a gaggauta dawo da su.

    Rundunar hadin gwiwa ta tsaro ta gwamnati ta ce jami’an tsaro 63 sun ji raunuka.

    A makon da ya gabata an kashe masu zanga-zanga biyu a wani masallaci da ‘yan sanda suka yi yunkurin tarwatsa zanga-zanga; bayan haka kuma aka kama sama da mutum dari da hukumomi suka yi zargin shirya zanga-zangar.

    A watan Fabrairu hukumomi sun yi artabu da Cocin Orthodox, wadda ita ce daya babbar kungiyar addinin.

    Rikicin da ya barke ya janyo asarar rayuka da dama kuma tun lokacin aka dakile wasu shafukan sada zumunta a kasar.

  2. Raɗe-raɗin na mallaki naira tiriliyan tara tsagwaron ƙarya ne – Gwamnan Zamfara

    ..

    Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya musanta ikirarin da ake yi na cewa ya bayyana kadarorin da ya kai naira triliyan 9.

    Gwamnan a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Idris ya fitar a ranar Juma’a a Gusau, ya bayyana labarin a matsayin ƙage da aka shirya domin kawar da hankalin sabuwar gwamnati daga yunƙurinta na ceto Zamfara.

    Ya kara da cewa wadanda suka fadi zabe ne suka yaɗa ƙarairayin, kamar yadda suka yi a lokacin yaƙin neman zabe.

    Sanarwar ta bayyana cewa sabuwar gwamnati ta fara aiki kuma ta mayar da hankali wajen ganin ta samar da natsuwar da ake bukata a cikin harkokin mulki a jihar domin sauke nauyin alhakin da ke kan ta.

    Sanarwar ta kara da cewa: “Ba za a dauke mana hankali da irin wadannan labaran na karya da ke kafafen sada zumunta ba, domin gwamnatinmu ta kuduri aniya kuma ta mayar da hankali kan kudirinta na magance matsalar tsaro da ilimi da samar da ruwan sha da inganta kiwon lafiya da noma da sauran kalubalen tattalin arziki da suka addabi jihar.

    Muna kuma aiki ba dare ba rana domin ganin mun sauke nauyi da ayyukan da gwamna ya yi alkawrin gudanarwa.” kamar yadda sanarwar ta ce.

    Gwamnan ta bakin mai magana da yawunsa ya ce gwamnatinsa na matukar aiki a kokarinta na cetowa da kuma sake gina jihar Zamfara, inda ta mayar da hankali wajen ganin ta cika alkawuranta.

    Ya kuma buƙaci jama’a da su yi watsi da ƙaryar da ake yaɗawa da gangan domin a ɓata wa sabuwar gwamnatinsa suna.

  3. Yan gudun hijrar Sudan a Chadi sun zarce 100,000

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta ce mutanen da ke hijira sakamakon rikicin da ake yi a Sudan zuwa makwabciyarta Chadi sun zarce 100,000.

    Hukumar ta ce mafi yawan sabbin 'yan gudun hijirar sun fito ne daga yankin Darfur, yankin da ke fama da tashin hankali da rashin zaman lafiya.

    Sabbin alkaluman dai na zuwa ne bayan da Amurka ta kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni na Sudan guda hudu da wasu mutane da dama saboda hura wutar yakin da ake gwabzawa tsakanin sojojin ƙasar da dakarun kungiyar RSF

    Wakiliyar UNHCR a kasar Chadi, Laura Lo Castro, ta yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta taimaka wa 'yan gudun hijira a kasar Chadi, yayin da adadinsu ke karuwa.

    A ranar litinin din nan, ta ce ana sa ran sama da mutane 200,000 za su kauracewa yakin zuwa gabashin Chadi cikin watanni uku masu zuwa.

    Hukumar kula da ‘yan hijirar ta duniya ta ce sama da mutum miliyan 1.2 ne kuma suka rasa matsugunansu a cikin Sudan sakamakon rikicin.

    Ana ci gaba da gwabza fada a birnin Khartoum da kuma wasu sassan kasar da suka hada da yankin Darfur.

  4. Mutanen da suka mutu bayan hatsarin jirgin ƙasa a Indiya sun kai 30

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Yadda mutane ke ƙoƙarin neman tsira

    Hukumomi a jihar Odisha da ke gabashin Indiya sun sanar da mutuwar aƙalla mutum 30 da mutuwar ɗaruruwa sakamakon taho mu gama da wasu jiragen ƙasa guda biyu suka yi.

    Kusan motocin daukar marasa lafiya 50 ne aka aika zuwa wurin da lamarin ya faru a Lardin Balasore, a cewar babban sakataren jihar.

    Ana kuma fargabar cewa mutane da dama sun rasa ransu.

    Firaministan Indiya Narendra Modi ya wallafa a shafinsa na Twitter inda yake cewa yana cikin matukar damuwa sakamakon hadarin kuma ya na taya wadanda suka rasa 'yanuwansu jimamin rashin.

    Taragan jirgi da dama ne suka kauce daga layin dogo.

    Ana kuma ci gaba da aikin agaji domin kuɓutar da mutane.

    Ana yawan samun haɗarin jirgin ƙasa a India, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

  5. An girke sojoji a titunan Dakar bayan ɓarkewar zanga-zanga a Senegal

    .

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Senegal ta baza sojoji a fadin Dakar, babban birnin kasar, yayin da mazauna yankin ke zaman dar-dar inda su ke tsammanin ci gaban tashin hankali.

    Mutane 9 ne suka rasa ransu a ranar Alhamis sakamakon artabu tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga.

    Hakan ya biyo bayan yanke hukuncin daurin shekara biyu da aka yi wa dan siyasar nan Ousmane Sonko kan rashin da'a.

    Mista Sonko ya ci gaba da cewa tuhumarsa da aka yi na da nasaba da siyasa domin a hana shi tsayawa takara a zaben shugaban kasa na badi.

    'Yan sanda sun kewaye gidansa, sannan gwamnati ta rufe wasu shafukan sada zumunta.

  6. Ƴan sanda sun kama mutumin da ake zargi da lalata ƴar shekara 10 a Bauchi

    .

    Asalin hoton, Ahmed Mohammed Wakil/Facebook

    Bayanan hoto, Kwamishinan ƴan sandan jihar Bauchi

    Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta cafke wani mutum mai shekara 33 saboda zarginsa da yin lalata da ƴar shekara 10 bayan da ya bata wani abun sha da ya gusar da tunaninta.

    Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Ahmed Mohmammed Wakil ne ya bayyana kame mutumin cikin sanarwar da ya fitar yau Juma'a.

    Ya ce "a ranar 25 ga Mayu, 2023 da misalin karfe 1233 na safe mahaifin yarinyar da ke kauyen Nasaru a karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi, ya kai rahoto ofishin 'yan sanda cewa, da safiyar wannan ranar wanda ake zargi ya yi lalata da diyarsa ta hanyar ba ta wani abun sha daya sa ta fita daga hayyacinta.

    A sakamakon haka yarinyar ta ji mummunan ciwo a al'aurarta tare da zubar da jini.

    Sanarwar ta ƙara da cewa "bayan samun rahoton, tawagar jami’an tsaro karkashin jagorancin babban jami'in ɗan sanda suka garzaya wurin da lamarin ya afku, inda suka dauki yarinyar zuwa babban asibitin Ningi domin kula da lafiyarta, daga bisani kuma aka kai ta cibiyar kula da masu fama da cutar yoyon fitsari (NOFIC) da ke Ningi."

    Sai dai kuma rundunar 'yan sandan ta sha alwashin kaiwa ga tushen lamarin tare da tabbatar da cewa an gurfanar da mutumin da ya aikata laifin domin zama izina.

    A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike, daga nan kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin ya fuskanci hukunci. A cewar Wakil, mutumin ya tabbatar da aikata laifin.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar sun sa ido a kan 'ya'yansu tare da sanin inda suke da kuma halin da su ke ciki a ko da yaushe.

  7. Abin da aka tattauna a taron Tinubu da gwamnonin Jam’iyyar APC

    .

    Asalin hoton, DOlusegun/Twitter

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce inganta rayuwar ‘yan Najeriya ne babban abin da gwamnatinsa ta fi baiwa muhimmanci.

    A cewar Daraktan yada labarai na fadar shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye, shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar gwamnonin APC karkashin jagorancin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a fadar gwamnati.

    Rahotanni sun ce shugaban ya ce gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi za su yi aiki tare a kan mafi karancin albashi, wanda abu ne da ya ce ya kamata a duba.

    Tinubu ya bukaci gwamnonin da su yi amfani da damar da miliyoyin ‘yan kasa suka ba su domin kawo sauyi a rayuwar jama’a. Ya kuma kara da cewa zai yi aiki don jin dadin ‘yan Najeriya.

    “Wannan taron ba bakon abu bane a gare ni, kuma abubuwan da taron ya kunsa na da matukar muhimmanci. Hadin kan na da ban sha'awa sosai. Wannan ya shafi aikin Najeriya ne ba Bola Tinubu ba,’’ in ji shi.

    .

    Asalin hoton, Abdulfagge/Twitter

    Shugaban ya ce za a daidaita farashin canjin dala, a inda yake cewa gwamnati abu ne mai ci gaba.

    “Na gaji kadarori da kuma basussukan wanda ya gabace ni. Wannan shi ne karon farko da kuka shiga zauren majalisar, kuma wannan ne karo na farko da zan yi taro“.

    Tinubu ya bayyana farin cikinsa da ganin cewa jam’iyyar APC ke da rinjaye a Majalisar dokoki ta kasa da na wasu jihohi, wanda hakan zai sa a samu sauki wajen samar da manufofin da za su shafi tattalin arziki da jama’a kai tsaye.

    A nasa jawabin mataimakin shugaban kasa, Sen. Kashim Shettima, ya yi kira ga gwamnonin da su bai wa shugaban kasa hadin kai yayin da yake tunkarar kalubalen da ke durkusar da tattalin arzikin kasar, kamar tallafin man fetur da kuma farashin canji da ake da su daban-daban..

  8. Cire tallafin man fetur a Najeriya ya haifar da tashin farashi a Jamhuriyar Benin

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin man fetur ya ninka kusan biyu a wuraren da ake sayar da man a Jamhuriyar Benin mai makwabtaka da Najeriya.

    Wannan ya faru ne sakamakon matakin cire tallafin man a Najeriya, inda tashin farashin ya haifar da tsadar sufuri a kasar.

    Wani dan jarida da ke kasar ta yammacin Afirka, Clément Sodji ya gaya wa BBC cewa farashin man ya tashi daga CFA 450 zuwa CFA 700 ko ma CFA 800 CFA.

    Daman ana satar shigar da man fetur daga Najeriya zuwa kasar ta Benin, inda yawanci ake sayar da shi a kasuwar bumburutu a sassan kasar daban-daban.

    Man na sumogal wanda mutane ke kiransa kpayo — ma'ana wanda ba na ainahi ba, da harshen kasar, Goun, ya fi araha a kan wanda ake sayarwa a gidajen mai - CFA 650.

    Ana sayar da mai a Najeriya a farashin da yake kusan rabi na kasashe makwabtanta wannan ne ya sa ake satar fitar da man na Najeriya zuwa wadannan kasashe inda ake sayar da shi a kasuwar bayan-fage wato bumburutu inda yawancin jama'a ke saye.

    Kusan a iya cewa jama'a ba sa sayen mai a gidajen mai a yawancin wadannan kasashe makwabtan Najeriya saboda wanda ake satar shigar da shi daga Najeriyar ya fi sauki.

  9. Ƙungiyar ƙwadago ta NLC za ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani a Najeriya

    NLC

    Asalin hoton, OTHERS

    Bayanan hoto, NLC ta yanke shawarar shiga yajin aikin ne saboda janye tallafin mai da gwamnati ta yi

    Kungiyar kwadago ta Najeriya ta NLC ta ce za ta fara yajin aiki na gama-gari daga ranar Laraba, 7 ga watan nan na Yuni.

    Shugaban kungiyar Joe Ajaero shi ne ya sanar da haka, bayan wani taron gaggawa da shugabannin kungiyar suka yi yau a Abuja.

    Kwamared Ajaero ya ce gwamnati musamman ma kamfanin mai na kasar NNPC na da wa'adin daga yanzu zuwa ranar Laraba ta mako mai zuwa ya mayar da farashin man kamar yadda yake a da idan ba haka ba za su shiga yajin aikin na sai-abin-da-hali-ya-yi da kuma zanga-zanga a fadin kasar.

    Daman a yau ne shugabannin suka kira wannan taro domin tattaunawa da bayyana matakin da za su dauka bayan da sabon shugaban kasar ya furta cewa kasar ta janye tallafin mai.

    Wannan sanarwa ta shugaban ta janyo tashin farashin man a sassan kasar, inda aka rinka samun dogayen layukan ababan hawa a gidan mai.

  10. Ana taƙaddama kan shiga gidan gwamnatin Zambia da jakar mata ta hannu

    Jakar mata ta hannu

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Da farko mata na korafin cewa an hana su shiga gidan da jakar-hannu

    Fadar gwamnatin Zambia ta fayyace matsayinta kan wani ce-ce-ku-ce da ake yi cewa ta hana mata rike da jakar hannu shiga cikinta da halartar duk wani taro nata.

    Gwamnatin ta yi wannan bayani ne bayan da ake ta korafi a kan wasu matakai na tsaro da ta bullo da su a gidan shugaban kasar, wadanda ba sa la'akari da mata ko maza wajen bincike.

    A kan hakan ne shugabar wata kungiyar kare hakkin mata a kasar Grace Sinkamba, ta fito take korafi da cewa matakin na nuna wariya ga mata da 'yan mata.

    Sai dai kakakin gwamnatin kasar ta Zambia ya mayar da martani da cewa babu wata mata da aka hana shiga fadar gwamnatin saboda kawai tana rike da jakar hannu.

    Ya kara da cewa duk matar da ta ki yarda a duba jakarta wajen shiga to ita da kanta ta saryar da damarta ta shiga.

  11. Shugaba Tinubu ya naɗa Femi Gbajabiamila Shugaban Ma'aikatan Fadarsa

    Tinubu and Femi

    Asalin hoton, @DOlusegun

    Bayanan hoto, Tinubun ya kuma nada Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya

    Shugaba Bola Tinubu ya nada Shugaban Majalisar Wakilai a matsayin shugaban ma'aikatan fadarsa (Chief of Staff) Femi Gbajabiamila da Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, a matsayin mataimakinsa

    Sanarwar da ta fito daga darektan yada labarai na fadar shugaban kasar, Abiodun Oladunjoye, a yau Juma'a, ta kuma ce Tinubun ya nada tsohon gwamnan jihar Benue kuma tsohon ministan ayyuka na musamman na gwamnatin Buhari, Sanata George Akume, a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

    Takardar ta ce shugaban ya yi wadannan nade-nade ne a yayin taron da gwamnonin jihohi na jam'iyyarsa ta APC.

  12. Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ganawa da gwamnonin APC a Abuja

    Shugaba Bola Tinubu tare da gwamnonin APC

    Asalin hoton, TWITTER/@DOlusegun

    Bayanan hoto, Wannan ne karon farko da shugaban ke ganawa da gwamnonin bayan rantsar da shi

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yana taro da gwamnonin jam'iyyarsa ta APC a fadarsa da ke Abuja, a yau Juma'a.

    Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma, wanda aka zaba kwanan nan a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin na APC, shi ne ya jagoranci tawagar.

    Babu wata masaniya kan ainahin abin da traon zai tattauna amma ana ganin cewa ba zai rasa nasaba da zaben shugabannin majalisar dokoki ta kasar ta goma da za a kafa ba.

    Bayan nan akwai batun nadin ministoci da kuma maganar janye tallafin mai, lamarin da ya tayar da hankalin 'yan kasar a halin yanzu.

    Wadanda ke wajen taron sun hada da gwamna Babajide Sanwo-Olu na Lagos, da Abdullahi Sule na Nasarawa, da Umar Namadi na Jigawa, da Inuwa Yahaya na Gombe, da Yahaya Bello na Kogi, da Farfesa Babagana Zulum na Borno, da Mai Mala Buni na Yobe.

    Sauran su ne Uba Sani na Kaduna, da Dikko Radda na Katsina, da Hyacinth Alia na Benue, da AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara, da Dapo Abiodun na Ogun, da Umar Bago na Niger, da Aliyu Ahmed na Sokoto, da Francis Nwifuru na Ebonyi da kuma Bassey Otu na Cross River.

    Kafar talabijin ta Channels ta ruwaito cewa gwamnonin APCn da ba a gani ba a wajen taron su ne Oluwarotimi Akeredolu na Ondo, da Biodun Oyebanji na Ekiti, da kuma Dr Nasir Idris na Kebbi.

    Haka kuma akwai mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima, da babban sakataren gidan gwamnati Tijjani Umar, da kuma tshon shugaban EFCC Mallam Nuhu Ribadu.

    A jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa Tinubu, ya bayyana karara cewa zai saurari kowa ya kuma janyo dukkanin masu ruwa da tsaki a wajen yanke wani hukunci da zai shafi kasa.

    Ana ganin watakila shugaban ya nada ministocinsa a cikin kwana 60 da rantsar da shi, abin da 'yan kasar ke hakon ganin.

  13. Ana ɓarnata kuɗin gwamnati a Majalisar Dokokin Tarayya - Shekarau

  14. Ƴan sanda sun kewaye gidan jagoran ƴan hamayya na Senegal

    Senegal

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Hukuncin ɗaurin shekara biyu da aka yi wa Ousmane Sonko zai hana shi takara a 2024

    Ƴan sandan Senegal sun kewaye gidan jagoran ƴan hamayya Ousmane Sonko, a babban birnin kasar, Dakar, bayan mummunan rikicin da ya biyo bayan hukuncin da aka yanke masa na shekara biyu a gidan yari.

    A lokacin bayyana hukuncin kan laifin badala ko rashin da'a, a jiya Alhamis Mista Sonko ba ya kotun, to amma yanzu ministan shari'a ya ce za a iya kama shi kowa ne lokaci daga yanzu.

    Akalla mutum tara aka kashe a Dakar da birnin Ziguinchor na kudancin kasar, inda magaoya bayan Mista Sonko suka yi dauki-ba-dadi da 'yan sanda.

    Gwamnatin Senegal din ta toshe hanyoyin samun wasu shafukan sada zumunta da muhawara saboda abin da ta kira kokarin tabbatar da doka.

  15. Angola ta ƙara farashin mai amma banda masu motoci da baburan haya

    Gidan mai

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Angola ta yi hakan ne 'yan kwanaki bayan Najeriya sanar da cire tallafin

    Gwamnatin Angola ta ce ba matsin lamba daga asusun bayar da tallafi na duniya, IMF ba ne ya sa ta soke tallafin mai a kasar.

    A jiya Alhamis ministar kudi Vera Daves ta ce matakin ya biyo bayan nazarin da gwamnatin kasar mai cin gashin-kanta ta yi ne a kai.

    Batun ya taso ne bayan da gwamnati ta kara farashin man daga kudin kasar kwanza 160 zuwa kwanza 300 a kan lita daya, wanda yake kwatankwacin dala $0.27 zuwa $0.51.

    Sai dai karin farashin bai shafi motoci da baburan haya ba, inda ake ba wa masu sana'ar sufurin wani kati na musamman na sayen man da shi.

    Kasar ta Angola wadda ke yankin kudancin nahiyar Afirka, ita ce kan gaba a yanzu wajen yawan man da ake fitarwa kasuwar duniya daga nahiyar duk da cewa ba ta kai Najeriya yawan arzikin ba.

  16. Ƙungiyar ƙwadago ta NLC za ta yi taro kan janye tallafin mai a Najeriya

    NLC

    Asalin hoton, OTHERS

    Bayanan hoto, Shugabannin kungiyar za su yanke shawara kan matakin da za su dauka kan lamarin

    Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya za ta yi wani taro na manyan shugabanninta domin daukar matakin da ya kamata bayan da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cire tallafin mai, abin da ya sa farashin ya tashi kusan ninki uku.

    Sakataren kungiyar Nasir Kabir ya sheda wa BBC cewa shugabannnin za su yi wannan ganawa ne ta hanyar intanet ta Zoom.

    Tun bayan furucin da Shugaba Tinubun ya yi ne kasar wadda ta fi yawan jama'a da kuma kasancewarta gaba-gaba a arzikin mai ta fada wani yanayi na tashin farashin man da kuma dogayen layin ababan hawa a gidan sayar da mai.

    Yanzu dai layikan kusan sun ragu kasancewar yawancin gidajen mai a manyan biranen kasar suna amfani da farashin da ya kama daga naira 500 zuwa 600.

    Kamfanin man fetur na Najeriyar, NNPC ya tabbatar da cewa ya ƙara kuɗin litar mai a ƙasar.

    A wata sanarwa da ta kamfanin ya wallafa a shafinsa na twitter, ya ce ya yi karin farashin domin ya yi daidai halin da ake ciki.

    Kuma ya roƙi afuwa kan wahalhalun da hakan zai iya haifarwa.

    Kafin yanzu dai ana sayar da man a farashin da ya kama daga naira 180 zuwa naira 220 kan kowa ce lita, a sassan kasar daban-daban.

    Tun da aka shiga yanayin kungiyar kwadagon ta sha alwashin yin fito na fito da gwamnatin kasar a kan batun janye tallafin man.

    Kungiyar ta ce ba za ta amince ba, saboda cire tallafin zai jefa al'umma a cikin wahala.

    Sayar da man a farashi mai yawa ana ganin zai kara irin wahalhalun da jama'a ke sha a kasar wadda dama tuni take fama da matsaloli na bunkasa da kuma tsadar rayuwa wadda ba ta taba gani ba a kusan shekara ashirin baya.

  17. Fadar Amurka ta ce Shugaba Biden na nan lafiya, bayan ya faɗi

    Joe Biden

    Fadar White House ta ce shugaba Biden na cikin koshin lafiya bayan ya faɗi a bainar jama'a ana tsaka da taron yaye sojoji a Colorado.

    Shugaban ya yi tuntuɓe ne da wata jakar tara kasa sannan ya hantsila.

    Mista Biden, mai shekaru 80, ya samu taimako daga jami'an tsaro nan take, sai dai kuma ya warware ya koma kujerarsa da kansa.

    Ya shafe sama da sa'a guda yana karrama sojojin a tsaye kafin faruwar al'amarin.

    Tsohon Shugaba Trump kenan a Iowa, yake yi masa tsiya cewa tooo ka fadi, to ina fatan ba ka ji rauni ba, amma dai abun naka akwai mamaki.

    Shugaba Biden ya sha watsi da masu sukar cewa ya tsufa da sake neman wa'adi na biyu na mulkin Amurka.

    Kuri'ar jin ra'ayi ta baya-bayan nan na nuna cewa Amurkawa da dama na nuna damuwa kan yawan shekarunsa.

  18. Ƴan majalisar dokokin Amurka sun ceto ƙasar daga faɗawa bala'in tattalin arziƙi

    Joe Biden

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Shugaba Biden ya ce wannan gagarumar nasara ce ga Amurkawa

    Majalisar dattawan Amurka ta amince da kudirin bai wa gwamnati damar kara yawan bashin da take ci, domin ceto kasar daga matsin tattalin arziki.

    Kudirin ya samu amincewar kowanne bangare na jam'iyyun kasar da rinjayen kuri'u 63 da ke na'am da shi, yayin da mutum 36 suka nuna adawa, ko da yake akasari 'yan Republican ne suka nuna tirjiya.

    Shugaba Biden ya ce wannan gagarumar nasara ce ga tattalin arziki da kuma Amurkawa.

    Shugaban masu rinjaye daga jam'iyyar Democrats a majalisa, Sanata Chock Schumer, ya ce kuskuren kin amincewa da wannan kudiri zai kasance babban bala'i da zai haifar da radadi ga milyoyin Amurkawa.

    Ya ce an jima 'yan Republican na jayayya da wannan kudiri, sai dai yanzu abin farin ciki ne da zai inganta rayuwar Amurkawa da tattalin arzikinta.

    A yanzu Mista Biden zai sanya hannu a kan kudirin ya zama doka.

    Tun a jiya Laraba ne majalisar wakilai ta nuna goyon-baya ga kudirin.

  19. An toshe Facebook da WhatsApp a Senegal saboda rikici

    Rikici a Senegal

    Asalin hoton, OTHERS

    Bayanan hoto, Akalla mutum tara ne suka mutu a rikicin zuwa yanzu

    Hukumomi a Senegal sun toshe hanyoyin shiga shafukan sada zumunta da muhawara da suka hada da Facebook da WhatsApp sakamakon kazamin rikicin da ya biyo bayan hukuncin daurin shekara biyu da kotu ta yanke wa jagoran 'yan hamayya na kasar.

    Daman gwamnatin ta ce za ta dau duk wani mataki da ya dace domin kare rayuwar al'umma da dukiyoyi bayan mutuwar mutane sakamakon rikicin.

    Akalla mutum tara ne suka mutu a rikici tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga, bayan yanke wa Ousmane Sanko hukuncin a jiya Alhamis.

    Ministan cikin gida, Antoine Diome a wani taron 'yan jarida a cikin dare, ya ce an toshe kafofin ne, yana mai nuna takaicin abubuwan da suka faru.

    Rikicin ya fi baci a yankin Ziguinchor - (Zi-gan-shiyo)- da ke kudancin kasar, inda Mista Sonko ke rike da mukamin magajin gari.

    Hukukuncin kotun da aka yanke a bayan idonsa na iya hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓen shekara mai zuwa.

    An same shi da laifin nuna rashin ɗa'a, amma an wanke shi daga zargin aikata fyaɗe.