Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kotun zaɓen Najeriya ta soki Peter Obi kan rashin shirya wa shari'a

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Muhammad Annur Muhammad and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Ƴan majalisar Najeriya na son a yi bincike kan dala biliyan 25 ta gyaran matatun mai

    Majalisar dokokin Najeriya ta nemi da a gudanar da bincike na ƙwaƙƙwaf bayan da wani rahotonta ya gano cewa an kashe sama da dala biliyan 25 a cikin shekara goma da ta gabata wa wajen gyaran matutun man ƙasar.

    Rahoton ya gano cewa duk da wannan ɗimbin kuɗi da aka kashe matatun hudu suna aiki neƙasa da kashi 30 cikin dari.

    Wannan batun ya taso ne yayin da farashin mai a ƙasar mai arziƙin mai ya ninka sama da biyu bayan da sabon shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin mai, wanda ya ce kasafin kuɗin da ya gada bai tanade shi ba.

    Saboda rashin aikin matatun man yadda ya kamata tsawon shekaru Najeriyar wadda ita ce ta fi kowace ƙasa a Afirka arziƙin man tana fitar da ɗanyen man nata ne ta kuma sayo wanda aka tace daga waje.

    A wata mai zuwa ne ake sa ran katafariyar matar man da babban attajirin Afirka Aliko Ɗangote, ya gina a Lagos za ta fara aiki.

  2. Ba wanda ya isa ya sa mu sauya dokar hukunta ƴan luwaɗi da maɗigo a Uganda - Museveni

    Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya yi watsi da maganganu na suka da adawa da wasu kasashen duniya ke yi a kan matakin da kasarsa ta dauka na sa hannu a dokar haramta harkokin luwadi da madigo a makon nan.

    Mista Museveni ya kafe cewa aikin-gama-ya-gama a kan dokar babu sauran wani abu da za a yi na sokewa ko sauya ta.

    Ya kara da cewa babu wata barazana ko wani abu da wani zai yi ya sa su sauya matsayi a kai.

    A wata sanarwa da ya fitar bayan ya gana da mambobin jam'iyyarsa ta NRM, (National Resistance Movement), ya ma ce, ''Mu yi shirin yaki kawai.''

    Ya jaddada matsayar da cewa, jam'iyyarsu ta NRM ba ta taba magana biyu ba, ''abin da muka gaya muku da safe shi za mu gaya muku da daddare.''

    Shugaban Amurka Joe Biden da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, da sauran manyan kasashen duniya na ta suka a kan dokar wadda tana daga cikin mafiya tsauri a duniya.

    Bisa dokar duk wanda shari'a ta kama da laifin abin da ya shafi luwadi ko madigo za a yi masa hukuncin daurin rai da rai.

    Idan kuma laifin ya yi tsanani, kamar a yi wa wanda bai kai shekara 18 fyade ba na luwadi ko madigo ko kuma wanda aka yi wa tilas har aka yada masa muguwar cuta kamar mai karya garkuwar jiki to hukuncin kisa za a yi wa mai laifin.

  3. Ƴan sanda sun gano wani gida da ake zargi ana haihuwar jarirai ana sayarwa a jihar Rivers

    Ƴan sanda a jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya sun ceto wasu mata masu juna biyu (ciki) guda shida bayan da su kai sumame a wani gida da ake zargin waje ne da ake haifar jarirai a sayar da su.

    Rahotanni sun ce jami'an sun kama wata mata mai shekara 39, wadda ake zargin ita ce mai gidan.

    Kuma ta amsa laifin da ake zarginta da shi na tara matan da gudanar da harkar, inda ta ce ta dade tana yi.

    A yanzu dai matar da sauran wadanda suke taimaka mata wajen tafiyar da harkar na tsare ana gudanar da karin bincike da nufin kamo sauran wadanda ke da hannu a ciki, kamar yadda kwamishinan ƴan sanda na jihar, Polycarp Emeka, ya sanar.

    Wannan dai ba wani sabon abu ba ne a Najeriya musamman a yankin kudancin kasar inda ake tara mata a gida suna haihuwa a sayar da jariran.

    Domin an sha kama irin wadannan wurare da masu tafiyar da su inda ake kubutar da jariran da matan wadanda galibi matasa ne.

  4. Buɗewa

    Assalamu alaikum jama'a barkanmu da sake kasancewa a wannan shafi na BBC da muke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye.

    Ni ne Muhammad Annur Muhammad, zan kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a wannan rana ta Alhamis idan Allah Ya yarda.

    Mu fara da wannan karin maganar da ke cewa ; "Inuwar giginya na nesa ka sha ki''