Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kotun zaɓen Najeriya ta soki Peter Obi kan rashin shirya wa shari'a

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Muhammad Annur Muhammad and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Gwamnan Kano ya roki dillalan mai su sayar da shi kan tsohon farashi

    Sabon Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bukaci dillalan man fetur da su ci gaba da sayar da man kan farashin da aka saba domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta a halin yanzu.

    Gwamnan ya ce yana sane da cewa har yanzu dillalan na da ragowar man da ya kamata a ce sun sayar a kan tsohon farashi.

    Cikin sanarwar da Sakataren yada labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya ce idan ana son rage wahalhalun ‘yan jihar, ya kamata dillalan su yi hakuri su sake bude duk gidajen mai da ke da man fetur a kasa su kuma sayar a kan tsohon farashi.

    “A matsayina na gwamna, na ji takaicin ganin yadda al’ummar Kano ke shan wahala sakamakon kara farashin man fetur da ba gaira ba dalili, kuma dole a kawo karshen lamarin nan take,” a cewar gwamnan.

    Ya kara da cewa Kano ita ce cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya har ma da wasu kasashen Afirka ta yamma kuma al'ummarta na cigaba da morewa yanayin kasuwanci mai kyau.

    Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar Kano da su ci gaba da bin doka domin gwamnati a ko da yaushe a shirye take ta tabbatar da cewa mutane suna gudanar da harkokinsu cikin sauki.

  2. Za a daina ganin dogayen layuka a gidajen mai nan da ƴan kwanaki - Mele Kyari

    Shugaban Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, Mele Kyari ya bayyana fatan cewa layuka a gidajen sayar da mai a fadin kasar zai zama tarihi nan da kwana biyu masu zuwa.

    Kyari ya shaida hakan ne a hirarsa da gidan Talabijin na Channels inda ya ce halin da aka shiga ba mai dorewa bane.

    A cewarsa, baya tunanin dogayen layukan da ake kafawa zai kai har zuwa ranar Asabar.

    Ya bayyana cewa akwai sama da lita miliyan 810 na man fetur a depo-depo da tankoki da kuma gidajen man da ke fadin Najeriya.

    A ranar Litinin ne yayin jawabinsa bayan shan rantsuwar kama aiki, sabon shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce zamanin biyan tallafin mai ya zo karshe, matakin da ya haifar da tashin farashin man fetur a sassan kasar.

    Sai dai wakilin BBC ya ce an samu raguwar layukan mai a Abuja, babban birnin Najeriya duk da a wasu jihohin, lamarin bai janye ba.

  3. Heitinga ba zai ci gaba da aikin horar da Ajax ba a badi

  4. Amurka ta ƙaƙaba wa sojojin Sudan da dakarun RSF takunkumi

    Gwamnatin Amurka ta kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni hudu na kasar Sudan da wasu mutane da dama saboda hura wutar yakin da ake gwabzawa tsakanin dakarun soji.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka watse a tattaunawar da ake yi tsakanin wakilan sojojin kasar da kuma dakarun RSF ba tare da cimma wata matsaya ba.

    A ranar Laraba akalla farar hula goma sha takwas ne aka kashe a yayin da bangarorin biyu suka yi artabu a Khartoum.

    Ma'aikatar kudi ta Amurka ta ce sabbin takunkuman za su katse muhimman kudade ga bangarorin biyu da ke yaki a Sudan ke samu.

    Kamfanonin da takunkumin ya shafa sun hada da wanda ya mallaki ma’adinan zinare kuma ke karkashin kulawar shugaban rundunar Rapid Support Forces - Janar Dagalo ko Hemedti. Akwai kuma wani makeken kamfani da ke kera makamai yana sayar wa sojojin kasar.

    Sai dai masu lura da al'amura da dama na shakkun ko takunkuman za su yi wani tasiri. Ba yau ba ne Amurka ta fara kakaba wa Sudan tukunkumi.

    Abin ban tsoro shi ne da alamun babu wanda ya san yadda za a iya kawo karshen wannan yakin wanda a ranar Laraba aka kashe farar hula akalla goma sha takwas yayin da bangarorin biyu suka yi artabu da juna a kudancin Khartoum.

  5. Zanga-zanga ta ɓarke bayan yanke wa Ousmane Sonko hukunci

    Ana zaman dar-dar a Senegal bayan da wata kotu ta yanke hukuncin daurin shekara biyu kan madugun 'yan adawa, Ousmane Sonko.

    An yanke wa dan siyasar mai shekaru 48 da haihuwa hukunci bisa zargin gurbata matasa amma an wanke shi kan zargin aikata laifin fyade da barazanar kisa da wata ma’aikaciyar shagon kwalliya ta yi.

    Wannan hukunci dai ya haramta wa Sonko tsayawa takara a zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a watan Fabrairun badi.

    Yanke hukuncin dai ya haifar da arangama tsakanin 'yan sanda da magoya bayan Sonko, wadanda suka taru domin nuna adawa da hukuncin da kotun ta yanke a sassan babban birnin kasar, Dakar.

    An kuma yanke wa mai shagon kwalliyar inda ake zargin al’amarin ya faru, hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari.

    Yayin da tawagar lauyoyin da ke wakiltar ma’aikaciyar suka nuna gamsuwarsu da hukuncin, lauyoyin Sonko sun nuna cewa suna tunanin daukar wasu matakai a shari'ance.

    Ana yi wa Sonko, wanda ya zo na uku a zaben shugaban kasar Senegal na karshe, kallon daya daga cikin manyan masu adawa da shugaban kasa Macky Sall.

    An kara dagula al'amura a kasar saboda hasashen da ake yi cewa shugaba Sall na iya sake neman wa'adi na uku.

  6. Kotun zaɓen Najeriya ta soki Peter Obi kan rashin shirya wa shari'a

    Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta caccaki jam’iyyar Labour da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, kan rashin shiryawa karar da aka shigar na kalubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu.

    A ci gaban zaman kotun a ranar Alhamis, daya daga cikin manyan lauyoyin da ke cikin tawagar lauyoyin masu shigar da kara, Emeka Okpoko, ya nemi gabatar da takardun zabe a matsayin shaida a gaban kotu amma an ce ba a gabatar da takardun yadda ya kamata ba kuma ba a shirya su a gaban kotun ba.

    Don haka kotun ta dage sauraron karar na tsawon mintuna 10 sannan ta bukaci tawagar lauyoyin da ta sake gabatar da jadawalin takardun kamar yadda aka tanadar da rahoton gabanin sauraron karar.

    Duk da haka, bayan da kotun ta dawo, tawagar lauyoyin ta kasance cikin rashin tsari.

    Cikin rashin jin dadi, kwamitin mutum biyar na alkalan kotun karkashin jagorancin Haruna Tsammani, ya shawarci masu shigar da karar da su nemi a dage zamansu domin su tsara takardunsu yadda ya kamata.

    Sun bayyana abin da aka yi a yau a matsayin bata lokaci, inda suka ce lauyoyin masu shigar da karar sun raina muhimmancin aikin da ya kamata su yi.

    Da yake mayar da martani, Awa Kalu, wani babban lauya a tawagar masu shigar da karar, ya ce ba za su karbi shawarar dage zaman ba, sai dai za su mika shaidun kananan hukumomi 16 da ke kasa.

    Zuwa yanzu dai Jihohi shida ne Jam’iyyar Labour ta kawo shaida a kan su.

    An kuma dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Yuni.

  7. An yi auren ƙasaita na Yarima mai jiran-gado na Jordan

    Yarima William na Birtaniya da matarsa Kate na daga cikin manyan baki na duniya da suka halarci bikin auren Yarima mai jiran-gado na Jordan Hussein.

    Yarima Hussein ya auri wata kwararriyar mai zayyanar gine-gine ce ƴar kasar Saudiyya, Rajwa Alseif. inda aka yi bikin a Amman babban birnin kasar ta Jordan.

    Matar Shugaba Biden na Amurka Jill Biden tare da Sarkin Netherlands da matarsa su ma sun kasance a bikin.

    An yi taron bikin ne a Fadar Zahran inda a nan ne aka daura auren shi ma mahaifin Yariman wato Sarki Abdullah na biyu a ranar 10 ga watan Yuni na 1993.

    Bikin ya zo ne bayan rikicin da iyalan sarautar na Jordan suka yi ta fama da rikicin cikin gida, wanda ya hada da sa-in-sa a fili tsakanin sarkin da kaninsa da suke uba daya, Yarima Hamza.

  8. Matsalar rashin aikin yi ga matasa ta damu hukumomin China

    Lardin yankin Henan na China ya kaddamar da wani gangami na kwana dari domin samar da ayyukan yi ga matasan yankin sakamakon karuwar rashin ayyukan yi da kasar ke fuskanta.

    Alkaluma a watan Afirilu sun nuna cewa mutum daya cikin biyar na matasa yan shekara goma sha shida zuwa ashirin da hudu na fama da rashin aikin yi, wanda shi ne mafi muni a cikin shekarun nan a kasar ta Sin.

    Jami'ai a Lardin Henan za su gana da daliban da suke dab da kammala jami'a domin taimaka masu wajen samun aiki a kamfanonin gwamnati.

    Ana sa ran matasa da suka kammala jami'a kusan miliyan goma sha biyu ne za su nemi aiki a China a wannan shekarar.

  9. Abin da ya kamata ku sani game da tasirin cire tallafin mai

  10. Wasu maniyyatan jihar Jigawa sun tsallake rijiya da baya, bayan sa'a biyar a sama

    Wani jirgin kamfanin Max Air dauke da maniyyata da ya tashi daga filin jirgin sama na birnin Dutsen jihar Jigawa a jiya Laraba ya yi saukar gaggawa a filin jirgi na Mallam Aminu Kano da ke birnin Kano bayan tafiyar wajen sa'a biyar a sama.

    Wani daga cikin maniyyatan da ke cikin jirgin da aka samu matsalar ya sheda wa BBC cewa suna cikin tafiya ne a cikin jirgin da ya dauko su tun da farko sai suka shiga irin gargadar nan ta sama, daga nan sai aka sanar da su cewa za su koma saboda wata mata domin a sauya musu wani jirgin.

    Ya ce: ''Bayan mun koma mun sauka a Kano sai aka ce mana nan da awa daya za a kawo wani jirgin. To cikin ikon Allah kafin awa dayan ma sai ga aka kira mu muka je muka shiga wanda aka kawo,''

    ''To kuma muna cikin tafiya mun yi wajen awa biyar da tashi sai aka yi wata sanarwa cewa za mu sake komawa Kano, wasu ma ba su ji sanarwar ba sosai saboda an ce tafiyar wajen awa shida ce kuma mun yi wajen awa biyar, wasu na cewa Jeddah aka ce,'' in ji shi.

    Maniyyacin ya kara da cewa, '' To muna haka kawai da jirgin ya fara yin kasa-kasa sai muka ga ai nan Kano ne muka dawo.''

    Mutumin ya ce daga baya suke jin cewa wai jirgin na biyu ya komo ne saboda wata matsala ta diflomasiyya, ko da yake ya ce ba wata sanarwa ba ce ta musamman illa dai wasu daga cikin ma'aikatan kamfanin jirgin saman ne da ke tare da su a jirgin suke gaya musu.

    Bayanai na nuna cewa a yanzu maniyyatan na dab da sake tashi a wani jirgin daban shi ma na kamfanin na Max Air.

    Babu dai wani bayani ko sanarwa ta musamman da hukumomi suka fitar kan wannan al'amari da ya shafi wannan rukuni na maniyyatan na jihar Jigawa wadanda su ne na farko daga jihar da za su ta shi a bana.

  11. Dole ne jami'an tsaron Najeriya su ninka ƙoƙarin da suke yi - Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce ya zama wajibi ga jami'an tsaron ƙasar su ƙara himma matuƙar ana son a ciyar da ƙsar gaba.

    Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin ganawarsa ta farko da shugabannin hukumomi da rundunonin tsaro na ƙasar a fadarsa da ke Abuja.

    A lokacin ganawa da manema labaru, jim kaɗan bayan kammala tattaunawar, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Babagana Monguno ya ce shugaban ya shaida musu cewa ba zai lamunci yanayin da ƙasar za ta rinƙa samun koma-baya ba.

    Inda ya ce bai kamata Najeriya ta rinƙa baya-baya ba a lokacin da sauran ƙasashe ke ci gaba.

    Ya kuma ce dole ne a samun haɗin kai tsakanin dukkanin ɓangarorin tsaro domin ganin an kawar da duk wata matsalar tsaron da ke addabar ƙasar.

    A lokacin da ya sha rantsuwa a ranar Litinin, shugaba Tinubu ya sha alwashin magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

  12. Harin roka ya kashe mutum 18 a wata kasuwa da ke Sudan

    An kashe farar hula goma sha takwas tare da raunata sama da mutum ɗari ɗaya a faɗan da ake yi tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun RSF, a wata kasuwa da ke babban birnin ƙasar Khartoum, kamar yadda mazauna yankin da kuma likitoci suka bayyana.

    Wannan ita ce asara mafi muni da aka yi a wannan rikici da ya ɓarke tun a watan Afirilu na wannan shekara ta 2023.

    Mazauna yankin da aka tabka wannan asara waɗanda suke taimaka wa jama'a da abinci da kuma magana sun bayyana ce lamarin ya yi muni matuƙa, inda suke roƙo ga likitoci da kuma neman taimakon jini.

    Lauyoyi masu kare ƴancin ɗan'Adam sun ce an yi amfani da makaman roka da na atilare a faɗan na kasuwar Mayo da ke yankin kudanci na babban birnin, a jiya Laraba.

    Da wannan rashi yanzu yawan farar hula da suka hallaka a sanadin yaƙin na sama da mako bakwai ya kai aƙalla 883 kamar yadda alƙaluman gwamnati suka nuna, ko da yake ana ganin sun fi haka a zahiri.

    Kusan mutane miliyan ɗaya da rabi rikicin ya raba da muhallinsu, inda wasu suka fice daga ƙasar.

  13. Tinubu na ganawa da shugabannin rundunonin tsaron Najeriya a karon farko

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawarsa ta farko da manyan hafsoshin soji na ƙasar a fadar gwamnati da ke Abuja.

    Dama dai a al'ada, shugabannin ƙasa kan yi irin wannan ganawa a kowane mako da manyan hafsoshin.

    Waɗanda suka halarci taron sun haɗa babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Farouk Yahaya, da babban hafsan sojojin ruwa na Najeriya, Vice Admiral Awwal Gambo, da babban hafsan sojojin sama, Air Marshan Isiaka Amao da Sufeta-janar na ƴan sandan Najeriya Usman Alƙali.

    Sai kuma shugaban Rundunar Tsaro ta farin kaya, Yusuf Bichi, da kuma shugaban Jami'an tsaron sirri na Najeriya, Ahmed Rufai Abubakar.

    A lokacin jawabinsa na kama mulki, shugaba Tinubu ya sha alwashin bai wa harkar tsaro muhimmanci a gwamnatinsa.

    Najeriya dai na fama da matsaloli na tsaro a kusan dukkanin yankunanta, waɗanda suka haɗa da na ƴan bindiga a arewa-maso-yamma da gyauron ƴan ƙungiyar Boko Haram a arewa-maso-gabas da kuma ƴan aware a kudu-maso-gabas.

  14. Yadda ƴan bindiga ke ƙona ƙauyuka ƙurmus a Darfur

  15. An yanke wa jagoran ƴan hamayya na Senegal ɗaurin shekara biyu

    Kotu ta yanke wa jagoran ƴan hamayya na Senegal, Ousmane Sonko, hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari a kan laifin bata tarbiyyar matasa.

    Sai dai kuma kotun ta wanke, Sonkon wanda bai halarci shari'ar ba, a kan zargin fyaɗe da barazanar kisan kai.

    To amma kuma duk da haka hukuncin ɗaurin na nufin ba zai iya tsayawa takarar shugabancin ƙasar ta Yammacin Afirka ba a zaɓen da za a yi a watan Fabarairu na shekara mai zuwa, 2024

    Ana ɗaukar Sonko a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ƴan hamayyar Shugaba Macky Sall.

    Shugaban wani shagon gyaran gashi inda aka yi zargin Sakon ya ci mutuncin wata mai tausa, ta lalata, wanda aka tuhume su tare shi ma an yi masa ɗaurin shekara biyu bisa laifin karfafa baɗala.

    An shiga wani yanayi a ƙasar na zaman ɗar-ɗar a cikin kwanakin nan a kan zargin cewa ƙila Shugaba Macky Sall ya nemi ta-zarce a wa'adi na uku.

    Ƴan sanda sun killace hanyar shiga gidan Ousmane Sonkon, inda suka yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa magoya bayansa da suke sukar shari'ar da cewa kutungwilar siyasa ce kawai.

    Zargin da gwamnatin Senegal ta musanta.

    A yau Alhamis ƙasar ta ɓullo da wata tattaunawa ta ƙasa da nufin shawo kan dambarwar siyasar da ake fama da ita, inda Shugaba Sall da wasu ƴan hamayya za su lalubo hanyar magance rikicin.

    Sai dai jam'iyyar Ousmane Sonko ta ki karɓar goron gayyatar.

  16. Majalisar Amurka ta amince da ƙara yawan bashin da ƙasar ke ciyowa

  17. Gwanin sojan Australia ya yi rashin nasara a kotu

    Wani jami'in soja da ya taɓa samun lambar yabo a Australia ya yi rashin nasara a ƙarar da ya shigar kan wasu kamfanonin jarida uku yana neman diyyar miliyoyin dala kan zargin ɓata masa suna,

    Soja ya ɗauki wannan mataki na shari'a ne bayan jaridun sun zarge shi da aikata laifukan yaƙi a Aghanistan.

    Mai shari'a Anthony Besanko, ya yanke hukunci cewa duk zarge-zargen da aka gabatar kan Ben Roberts-Smith akwai ƙamshin gaskiya a cikinsu.

    Wakilin BBC ya ce Ben Roberts-Smith ya musanta dukkanin zarge-zarge kan aikata kisa ba bisa ƙa'ida ba sama da shekara 10 da ta gabata.

    Haka kuma sojan ya musanta zarge-zargen cin zarafi da muzgunawa.

    Lauyansa ya ce maƙiya da ke kishi da nasararsa ne suka kitsa wannan labari ganin cewa ya samu lambar yabo mafi girma a aikin soja a Australia.

    Shari'ar da aka shafe shekara guda ana yi dauke da bayanai da karɓar bahasi daga tsofaffi da sababbin dakaru na musamman - ta ɗauki hankalin kafofin yaɗa labarai a duniya.

    Australia has had forces in Afghanistan since 2002

  18. Hare-haren Rasha sun hallaka yara da jikkata wasu - Sojojin Ukraine

    Jami'an gwamnatin Ukraine sun ce an kashe mutum uku a hare-haren cikin dare da Rasha ta kai babban birnin ƙasar Kyiv.

    Rundunar sojin ƙasar ta wallafa a shafinta na intanet da sauran shafukan sada zumunta da muhawara cewa biyu daga cikin mutum uku da aka kashe yara ne ƙanana.

    A hare-haren na Rashar wadda ta yi wa maƙwabciyar tata mamaye sun kuma jikkata mutum huɗu.

    An kai harin ne kan wata unguwa da ke gabashin tsakiyar babban birnin.

    A wannan makon Rasha ta zafafa kai hare-hare da jirage marassa matuƙa da makami mai linzami a birnin na Kyiv.

  19. BBC ta gano cewa shafukan sada zumunta na goge shaidun laifin yaƙi

    Wani bincike da BBC ta yi ya gano misalai da bayanai kan yadda kamfanonin shafukan sada zumunta da muhawara ke goge shaidun da ke tabbatar da aikata laifukan yaƙi daga shafukansu.

    Binciken ya ce ana goge hotuna da bidiyo masu muhimmanci da za su iya taimakawa wajen shigar da ƙara ko gurfanarwa a gaban kotu a nan gaba.

    Wani jami'i, cikin masu sa ido a kamfanin Meta, wanda ya mallaki Facebook da Instagram, Alan Rusbridger, ya ce sun ɗau matakan takatsan-tsan da irin waɗannan bayanai.

    Jakadiyar Amurka, Beth Van Schaak ta ce yadda bayanai ke ɓata gaskiya abin damuwa ne.

    Kamfanin Meta ya ce yana nazartar hanyoyin taimaka wa ƙasashen duniya domin tabbatar da adalci bisa nauyin da ya rataya a wuyansu na kare bayanan sirri da kuma dokokin shari'a.

  20. Babban Bankin Najeriya ya musanta karya darajar Naira

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya musanta wani rahoto da ke cewa ya karya darajar kuɗin ƙasar zuwa naira 630 a kan dala ɗaya.

    Wata sanarwa da muƙaddashin darektan sadarwa na bankin, Isa AbdulMumin, ya fitar ya ce ko a jiya Laraba ma an sayar da kuɗin ne a kan naira 465 kan kowace dala saɓanin abin da wancan rahoton ya ce naira 630.he report

    Sanarwar ta ce rahoton da wata jarida ta yi wanda ta ce ta samu bayaninsa ne ita kadai yana cike ne da karerayi da kuma jahilcin rashin sanin yadda kasuwar hadadar kudaden waje ta Najeriya take.

    Darektan ya jaddada matsayar bankin a kan lamarin inda ya ce ko a safiyar yau an sayar da naira 465 a kan dala ɗaya.

    Saboda haka bankin ya shawarci jama'a da su yi watsi da rahoton wannan jarida da cewa ta yi ne da nufin haddasa firgici a kasuwar musayar kuɗaden.